✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ake kushe fina-finan Hausa -kasimu Yero

Aminiya ta samu ganawa da shahararren  dan wasan kawikawayon nan  kasimu Yero wanda ya yi mata bayyani a kan yadda harkokin  wasan kwaikawaiyo suka gudana…

Alhaji Kasimu YeroAminiya ta samu ganawa da shahararren  dan wasan kawikawayon nan  kasimu Yero wanda ya yi mata bayyani a kan yadda harkokin  wasan kwaikawaiyo suka gudana a jiya da yau da kuma yadda za a inganta harkar. Ga yadda hirar ta kasance: 

Aminiya: Masu karatu za su so ka gabatar da kanka a takaice.
kasimu Yero: Sunana kasimu Yero, daya daga cikin masu wasannin kwaikwayo da kuma fina-finai a kasar Hausa.
Aminiya:Ka share kamar shekaru nawa kana wannan harka ta wasan kwaikwayo da fina-finai a kasar Hausa?
kasimu Yero:Mu dai mun san tun muna makarantar sakandare muka fara wannan harkar cikin wata kungiya irin tamu ta ‘Yan makaranta,ana kiranta ‘Drama Group’ko ‘Drama Club’ wato tun wurin 1962 ko kuma 1963 ke nan , har muka fita, a 1966 muka gama makarantar,duk da haka ba mu manta ba.Sai ya kasance ni ina gab da shiga Jami’a bayan na gama HSC,sai ya kasance ana wasa a Gidan Talabijin a Kaduna,lokacin ana kiranta Radio /Telebision Kaduna [R.T.K].Abokanmu da suke aiki a gidan suka ce akwai abokanmu da muka yi ta wasannin kwaikwayo yayin da muke sakandare, kuma yawanci suna da rai. Mun tabbata idan an kira su za su zo su bayar da tasu gudunmawar a wannan tashar. Lokacin sai Allah Ya jikan rai Khalifa,ya same ni har gida ya ce mini akwai wani wasan kwaikwayo da ake yi a Gidan Talabijin na Kaduna, da ma ka san tun a makaranta mu ke yi, shi ne na ce, ka zo ka taimaka, mu shiga, mu gani ko za mu bayar da tamu gudunmawar ta kara armashi. Na ce to. Ka ji yadda na shiga cikin harkar gadan-gadan a tsakanin 1970, ko 1971. Daga lokacin da muka ci gaba har yau,ba tsayawa, kuma wasa-wasa wannan aikin sai ya zame mana sana’a.
Aminiya: Ko kana iya tuna wasan da ya zama sanadiyyar shahararka a duniyar  Hausawa da kewaye?
kasimu Yero:Da muka fara, kowane dan wasa yana zuwa ne da nasa irin wasan da za a yi da ka, sai a yi shirin da ya kamata a yi. Da aka zo kaina sai na zo da rubutaccen wasa.Wanda ke shirya wasan, wato tsohon  Babban Darekta na NTA Mista Patrick, sai ya ce ai ko  na ga wani ya zo da rubuttaccen labari, kuma na ga kamar labarin zai yi kyau a yi shi.To tun daga lokacin na fara rubuta wasan kwaikwayo a Gidan Talabijin. A lokacin mun  fi karkata alkiblar wasannin wurin fadakarwa. Yau a ce mutane su lura da kaza ba shi da kyau. Duk lokacin da muka yi wasa muna fahimtar da jama’a wani abu muhimmi da zai amfane su. Sai wata rana aka ce mana wai an dinga wasan nan ke nan ba za a kawo na raha wanda zai rika ba jama’a dariya ba? Sai aka yi shawara aka ce ai akwai su da yawa. Shi ne muka fara wani wasa da ake kira ‘Karanbana’ .Da muka yi shekara hudu muna wasan Karanbana, sai aka ce ya kamata a tashi tsaye a shiga cikin littattafan da aka rubuta na Hausa a mayar da wani ya zama wasa.Sai na ce ai ko ni ke da littafin da za a mayar fim.Domin lalle a cikin littattafan da muka karanta na Hausa ba kamar ‘Magana Jari Ce’. Sai aka ce to ya ya za a yi?Sai na ce ni zan iya. Zan dauki labaran Magana Jari Ce in mayar da su wasannin Kwaikwayo. Aka ce to shi ke nan,cigaba.
A lokacin nan mai shirya wasan shi ne Allah Ya jikan rai Alhaji dalhatu Bawa, muka yi wajen  wasanni 25,sannan aka tsayar da wasan. Dalilin tsayar da shi shi ne, saboda an fara wani shiri na turanci a Jos mai suna ‘Cock Row At Dawn’ da ake watsawa duk kasa ta gani.Yawanci muna zuwa Jos akai-akai. Ka ji abin da ya tsayar da wasan Magana Jari Ce ke nan.
Muna nan wani lokaci,sai aka ce mana ana neman wani wasa daga Arewa, amma da Turanci za a yi shi ,don a ga mutanenmu da al’adunmu da suturunmu da sauran muhimman abubuwa. Sai na ce zan iya mayar da lttafin Magana Jari Ce daga Hausa zuwa wasannin turanci.Za Ka iya? Na ce kwarai da gaske. Aka ce to, ga shi nan an bar maka. Aka rubuta takarda aka aika Legas aka ce kasimu Yero ya ce zai iya yi.To Ku bar masa ya yi.
Da an so a shirya wasan Magana Jari Ce na turanci a Kano, muka tirje, daga bisani aka ba mu izinin yin komai a Kaduna, don a Kaduna muka yi na Hausa. Aiki ya kankama, aka sanya wa wasan suna ‘Wisdom Is An Asset,’ shi ma kamar na Hausa, na rubuta tsakanin wasanni 25 zuwa 28, yau da gobe shi ma aka dakatar da shi.
Tunda aka tsayar da wannan wasan shi ke nan. Da mu nan a kasar Hausa muna Magana Jari Ce, kasar Yarabawa suna da ‘billage Head Master,’ can kuma kasar Ibo suna da Ichekwu da su ‘New Maskurade’.Tsayar da wadannan wasannin da aka yi ta watsawa a babbar tashar talabijin ta kasa daga kowace shiyya ce ta haifar da wadannan fina-finan da ake yi a wannan zamanin da suke sayarwa .Ai da ba sayarwa ake yi ba.Yawancin shirye-shiryen kyauta ne, nunawa ake kowa ya gani, mutane su zauna su natsu su kalla su yi dariya,har wasan ya kare. Da aka tsayar da wasannin ne wadansu suka yi amfani da wannan damar su ke shirya wasanninsu a dauka da kamara a gyara a sayar wa jama’a. Ka ji abin da ya haifi fina-finan yanzu ke nan.
Aminiya:Wadanne sauye-sauye ne kake ganin an samu a wannan harka ta wasanni a tsawon lokacin da ka share wajen bayar da gudunmawa ga al’umma?
kasimu Yero:Wasannin da muke yi a da na gwamnati ne. Gwamnati ke sa mu yi, sannan ta watsa wa jama’a suna zaune a gidajensu. Ka ga haka ya sa an samu tsafta wurin hana furta kalaman da ba su kamata ba irin na batsa, da hotunan da ba su kamata ba, ko nuna bambancin addini, ko na kabila, ko wani abu mai kama da haka. Fina-finanmu na da ba ka da ikon ka kushe su ta kowace fuska. Ka ga yanzu kuwa,wanda zai yi, zai yi ne don kashin kansa, labarin nasa ne, ba abin da zai dame shi, abin da ya ga dama zai yi.Wasu nafina-finan da suka saba wa al’ada,wasu na shirya fina-finan da suka saba wa addini,da ke kawo rikita-rikitar da suka sa aka kafa Hukumomin Tace Fina-Finai na kasa da na Jihohi.Saboda tsaftace al’amarin da ake gani idan ba matakai aka dauka ba, suna iya haifar da rikice-rikice a wannan kasar.Ka ga a da ku iyaye ba ku shakkar kallon wasanni tare da ‘ya’yanku, don kuna da tabbacin cewar wasanni masu tsafta za a nuna don an saba nunawa.Ka ga na yanzu har tsiraici ake nunawa iyaye na kallo tare da ‘ya’yansu.
Sai  mu zo fannin ‘Yan wasa, a da kafin a same su sai an yi da gaske, yanzu kuwa muna da su da yawa .Idan kuma ka koma wajen kayan aiki, wato na’urorin da ake daukar wasannin, a da kam suna da girma, ga kuma nauyi, na yanzu kuwa ba su da girma bare nauyi. A da ana amfani ne da kasa-kasai,yanzu kuwa kananan faya-fayai ake amfani da su don jama’a su kalla, wato su CD da DbD.
Aminiya:Kana ganin Hukumomin tace Fina-finan nan na taka rawar da ta kamata
kasimu Yero:Da yawansu sun yi kokarin tabbatar da cewa abubuwa sun tafi daidai. Har yanzu dai ana nan ana gwagwagwa da su. Ka ga kamar Hukumar Tace Fina-Finai Ta kasa, ta tsaya tsayin daka,don kuwa tana sanya kafar wando daya da duk masu shirya fina-finan da ke nuna batsa, da dangoginsu. Don idan aka kama mutum da laifi, ana yi masa hukunci ne yadda ya kamata.Su kuma na Jihohi wadanda a yanzu ake kafawa, su suka fi karfi, don su ke da yawancin masu shirya fina-finai. An sha kirana in shugabanci  kwamitocin ladabtar da wadanda ake tuhuma da aikata ba daidai ba. Idan gwamnati tana son ta tabbatar cewa an tsayar da al’adu da harshe da addini yadda ya kamata don na baya su gani su runguma hannu bibiyu yadda ake yi a wadansu kasashen, lallai ne gwamnati ta rika bayar da wani kaso ga duk wanda zai shirya fim.  Idan aka ga gwamnati ta tallafa da wani kaso, lalle kam za ta iya magance wadannan barnar da ake yi.
Aminiya: A matsayinku na iyaye, wace rawa kuka taka wurin gyara wannan al’amarin?
kasimu Yero: Idan ka zo da fim da kake son ka shirya, idan muka lura da cewa akwai wadansu abubuwan da za ka nuna wadanda ba su kamata a ce an nuna su, ba za mu shiga ba. Ka ji gyaran matakin farko da muke yi ke nan .Idan shi wanda zai shirya fim din ya zo da kansa ya ce ga fim ina son ka duba mini kura-kuran da ke ciki a gyara, a nan ma muna amsa mu gyara kura-kuran da muka gani. Idan na duba, sai in kara na karawa, in kuma cire na cirewa, na biyu ke nan.Ya kamata a fadakar da wadanda za su shirya fina-finai da taurarinsu muhimman abubuwan da suka kamata su sanya a gaba, wadanda suka hada da al’adu da addini da harshe. Idan aka yi haka za a kauce wa sanya duk abubuwan da ba su dace ba a fina-finai.
Aminiya;Mene ne ra’ayinka game da wakokin da ake yi a fina-finan Hausa?
kasimu Yero:Bahaushe na cewa kare da kudinsa sai a rubuta masa Lahaula ya sha. Zancen nan guda daya ne. Duk wanda yake son ya shirya fim abinda ya ga dama zai sa, ko ya sa waka, ko ya sa rawa, ba ka isa ka hana shi ba. Kowa ya san a kasar Hausa ana kida da waka, a kasar Yarabawa ana yi, a kasar Ibo ma ana yi, amma cusa sabbin abubuwan da wadannan mutane ke cigaba da yi da sunan cewa haka al’adun kabila kaza take, ban ji dadi ba. A ce Saurayi da Budurwa sun fito cikin fulawa suna raye-raye da wake-wake kam, ko a ce maka mutum ya zo gidan wata yarinya yana nemanta da aure ya fara waka ta Katanga, ba su da tsari  ko kadan.
Aminiya: Mene ne fatanka ga wannan harka ta Fina-finai a kasar Hausa.
kasimu Yero: Fatana shi ne, masu shirya fina-finan nan su rika shirya su da kyakkyawan nufi. Ba wai ka zo ka yi abin da ranka ya ba ka ba, ko ya saba wa wani, ko ka sa habaici, ko zagi, ko bakar magana. Ba wadannan abubuwan suka kamata a yi ba. Kamata ya yi duk lokacin da aka saki fim, duk wanda ya kalla ya ji dadi,ya kuma gamsu.