Search
Subscribe
Abin da ya sa auren matan Hausawa ba ya dorewa – Hadiza Karry

Abin da ya sa auren matan Hausawa ba ya dorewa – Hadiza Karry

Hajiya Hadiza Karry dattijuwa ce da ta kai shekara 84, kuma a haife ta ne birnin Baitul Mukaddas da ke kasar Isra’ila. A can ta yi karatu har ta yi aure. Dattijuwar wadda a kasar Isira’ila aka haife ta amma ’yar asalin garin Hadeja ce a Jihar Jigawa, yanzu haka ita ce Shugabar bangaren Koyar da Sana’o’i ga Mata a Cibiyar Koya wa Matasa Sana’o’i ta Sani Abacha da ke Kano. Hajiya Karry ta ce ta iya sana’o’i sama da 30 da take koyar da su. Ita ce mace ta farko da ta fara sana’ar kayan makulashe na Ice cream a Kano shekara 30 da suka gabata. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana kyuya a matsayin babban abin da ke kawo wa matan Hausawa cikas a zamantakewar aurensu. Ga yadda tattaunawarmu ta kasance:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihin rayuwarki?
Hajiya Karry: An haife ni a garin Jerusalam (Baitul Mukaddis) da ke kasar Isra’ila. Na yi duk kartuna a can har na samu horo kan aikin soja na tsawon shekara daya, daga nan na yi aure. Asalin iyayena ’yan Najeriya ne sun je kasar Isra’ila ne don ziyartar Masallacin Baitul Mukaddis a kan hanyarsu ta dawowa daga aikin Hajji. Daga nan sai suka yi zamansu a can inda suka haife ni da ’yan uwana mu biyar wadanda a yanzu mu uku ne muka saura. Tun a lokacin Sardauna sai wasu Hausawa daga Najeriya da suka hada da Sarkin Kano Sanusi 1 da Alhaji Isah Kaita da Babangida Joseph suka kai ziyara Baitul Mukaddis sai muka hadu da su, inda na dauke su na kai su gidanmu wurin mahaifinmu. Da suka koma Najeriya sai suka aiko mana da fasfo a kan mu zo gida ziyara amma sai mahaifana suka ki zuwa. Ni kuma sai na nemi yardar mijina na taho Najeriya na sauka a Kaduna. Daga nan aka kawo ni Kano inda na sauka a wurin Sarki Ado Bayero (Allah Ya ji kansa) ya shirya min tafiya zuwa Hadeja inda har na gana da ’yan uwan mahaifana. Bayan na koma sai na sake dawowa tare da maigidana inda muka ci gaba da zama a Kano har na haifi ’ya’yana biyu duka maza. Ba mu dade da zuwa kasar nan ba maigidana ya rasu, tun kuma daga wancan lokaci ban sake wani auren ba. Na ci gaba da zama ina tarbiyyar ’ya’yana har suka yi karatu suka yi aure. A yanzu haka babban Husam, injiniya ne yana da ’ya’ya bakwai yayin da karamin Yusuf yake da ’ya’ya uku. Ina nan a Kano a 1965 sai Sarkin Kano ya sama min aikin koyarwa a Makarantar Firamare ’Yan mata ta kwana da ke Shekara. Daga nan kuma aka yi min canjin aiki zuwa Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Dala. Daga nan kuma na koyar a Makarantar Horar da Malamai ta Gezawa a lokacin tana Magwan, wato a 1970. A duk makarantun da na yi aiki ina koya wa dalibai fannin tattalin gida da sana’o’in hannu da sauransu. Kasancewar ina da horo a kan aikin soja lokacin da aka yi Yakin Basasa na so in bi sojojin wajen yakin, amma sai ba a ba ni damar hakan ba. Lokacin da na je na samu shugaban sojojin na wancan lokaci na manta sunansa. Sai ya ba ni bindiga ya umarce ni da in kwance ta sannan in hada. Daga nan ya mike ya ba ni hannu yana yi min jinjina. Sai dai daga baya ya gaya min cewa ba su sanya mata a harkar yaki, sai dai idan zan je wurin yakin a matsayin ma’aikaciyar jinya, amma kasancewar ba ni da horo a bangaren aikin jinya sai ban je ba. Ko a wancan lokaci ban zauna haka ba, ina aikina na koyarwa ina kuma dan taba harkar kasuwanci. Ina iya tunawa a wancan lokaci nakan je garin Garko in sayo shinkafar gida in zo in gyara ta in rereye ta sai in ware manyan daban da kananan. To sai na dauki manyan shinkafar in zuba a buhu in aike wa wasu Turawa da ke Legas inda suke amfani da ita. Haka kuma nakan aike musu da alkama ma da sun samu kayan sai su turo min kudina ta banki.
Aminiya: Kin taba halartar wata makaranta ko wani kwas a kan sana’o’in hannu ne?
Hajiya Karry: Ban taba zuwa wata makaranta ko samun wani horo a kan abin da ya shafi sana’o’in hannu ba. Ina ga abin ya samo asali ne daga irin makarantar da na yi a Jerusalam inda bayan karatu ana koya wa kowane dalibi sana’o’in hannu da zai dogara da kansa. Kasancewar na iya sana’o’in hannu da suka hada da dinki da saka da rini da shirin duwatsu da sauransu lokacin da na daina aikin gwamnati sai na kafa wata cibiya da nake koyar da matsa sana’o’in hannu inda aka yi ta a Gidan Magajin Gari da ke Yakasai. To daga baya kuma sai Cibiyar Sani Abacha ta dauke ni a matsayin Shugabar Sashin Koyar da Mata Sana’o’i wanda har zuwa yanzu ina yin aiki a wurin. A can garinmu dole ne mutum ya yi aiki a natse, domin idan ka bata wa mutum kayansa ya kai ka kotu sai ka biya shi kudin kayansa.
Aminiya: Ya kika yi fama da bambancin abinci da sutura a wancan lokaci?
Hajiya Karry: A hankali na koyi cin abincin kasar nan. Sai dai tun farkon zuwana ina son tuwo da miyar kuka. Haka kuma batun sutura nakan sa riga da wando da hula wacce ake kira hana sallah. Daga baya a hankali na fara amfani da dogayen riguna, amma fa har yanzu ba na iya daura zani.
Aminiya: Yaya za ki kwantanta zamantakerwar aure tsakanin mutanen Jerusalam da na matan Hausawa?
Hajiya Karry: Kai kai akwai bambanci sosai a tsakanin matan kasashen biyu. Kun ga mata a can ba su da wani lokaci na kansu da za su zauna zaman banza ko yawon shiga makwabta hira. A tarbiyyarmu ba za ka bata minti biyar a banza ba tare da wani aiki ba. Lokaci yana da muhimmanci. Abin da na lura da shi babbar matsalar matan Hausawa ita ce kyuya wace take jawo aurensu ba ya dorewa. A koyaushe sun fi so su kwanta  ba tare da aikin komai ba. Sai dai su dauki ’yan aiki a gidajensu. Sannan abin haushi kuma sun fi kowa son mallakar miji. Ta yaya za ki mallaki mijinki ta hanyar kyuya? Ba ki yi wa mijinki abinci mai kyau, ba kya kula da shi yadda ya kamata? Ya kamata mata su fahimci cewa dole sai mace ta tsaya tsayin daka a kan lamurran gidanta sannan za ta samu kan mijinta. Na farko dole sai mace ta dage da kula da cikin mijinta. Ki iya girki iri-iri amma ba kullum a rika girka wa mutum abinci iri guda ba, kullum a ce shinkafa da jar miya shi ne abinci saboda ta fi saukin girkawa. Ya kamata a rika cancanjawa, shi canjin girki fa ba wai kudi yake bukata da yawa ba, illa dabarun iya sarrafa kayayayakin abincin da muke da su kawai. Ni ban yarda da batun cewa maza suna hana matansu kudin cefane ba, matan ne suke janyo hakan. A duk lokacin da mijinki ya san zai bayar da kudinsa a yi masa abinci mai kyau, to babu abin da zai sa ya fita waje ya ci abinci da tsada. Haka kuma yanayin yadda matan Hausawa ke zama cikin kazanta babu kwalliya wannan ma ba zai sa miji ya kula da matarsa ba. Wata matar za ta zauna yini guda da daurin kirji haka mijin zai fita ya bar ta, har kuma zai dawo ya iske ta a wanann hali. Ya kamata mace ta fahimci cewa namji kamar yaro yake, yadda kika tarbiyyantra da shi haka zai tafi a kai. Haka kuma tamkar makaho yake, ke ce mai yi masa jagora. Don haka akwai babban aiki a gabanki a matsayinki na mace, dole ki jajirce wajen sauke nauyin da ke kanki. Ki fahimci me mijinki ya fi so ki rika yi masa. Ki kula da tsabtar kanki da kwalliya, idan ya fita ya dawo ya tarar da ke da wata sabuwar kwalliyar ba wacce ya gani da safe ba. Haka kuma dole idan mace tana son ta samu martaba a wurin mijinta dole ta tsaya ta nemi na kanta, ba wai ta sa ido komai sai maigida ya yi ba. Lalaci ba na mace ba ne.  A rayuwar mace gaba daya ba lalaci.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga gwamnati wajen ganin ta bunkasa sana’o’in hannu a tsakanin al’ummarta?
Hajiya Karry: Babban kirana ga gwamanti shi ne bayan ta dauki nauyin horar da matasa ko al’ummarta game da sana’o’in hannu, to ta shigo wajen tallafa musu da jari da kuma ba su kwarin gwiwa. Sannan ta sama musu kasuwa yadda za su rika sayar da kayan da suka sana’anta don su samu kudin shiga. Bababn abin da yake damun masu kananan sana’o’i a kasar nan shi ne rashin kasuwa. Za ki samu mutum ya iya sana’o’i da dama amma babu hanyar da zai shigar da kayan kasuwa. Akwai bukatar gwamnati ta yi duk abin da za ta yi wajen ganin ta bunkasa ire-iren kayayayakin da muke yi a gida ta hanyar yin amfani da su a harkokinta na yau da kullum. Sannan ta rufe duk wata hanya ta shigo da kayayyakin kasar waje cikin kasar nan wanda hakan zai sa al’umarmu su rungumi kayayyakinmu na gida.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin