✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa dalibai ke gasar shiga kwaleji don karanta fannin noma – Dokta Namakka

Aminiya: Yaushe aka kafa wannan kwaleji kuma mene ne manufofin kafa ta? Dokta Namakka: Wannan kwaleji, marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello ne ya kafa…

Aminiya: Yaushe aka kafa wannan kwaleji kuma mene ne manufofin kafa ta?

Dokta Namakka: Wannan kwaleji, marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello ne ya kafa ta a 1961. Kuma kwalejin ita ce asalin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Domin ita ce Sardauna ya fara kafa ginshikinta a matsayin kwalejin aikin gona, daga baya ta rikide ta koma Jami’ar Ahmadu Bello. Kuma wannan kwaleji ire-irensu uku ne marigayi Sardauna ya kafa, a karkashin Jami’ar Ahmadu Bello a wancan lokaci. Baya ga wannan ta Samaru, akwai Kwalejin Koyar da Aikin gona da Kiwon Dabbobi da ke Mando, Kaduna da kuma Kwalejin Koyar da Aikin Gona da ke Kabba a Jihar Kogi.

Manufar kafa wannan kwaleji, shi ne don horar da malaman gona wato daliban da kwalejin za ta yaye, su zama zakakuran malaman gona da za su fantsama cikin dazuka da kauyuka don su koya wa manomanmu dabarun noma na zamani. Wannan shi ne ainihin dalilin kafa wannan kwaleji. Domin lokacin da Sardauna da sauran masana suka kafa  kwalejin sun fahimci cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar nan, don haka suka kafa kwalejin da sauran kwalejojin don a rika horar da malaman gona da za su rika shiga lungu-lungu da kauyukan kasar nan, don horar da manoma a kan dabarun noma  na zamani, ta yadda za a bunkasa harkokin noma a kasar nan.

Kuma wannan kwaleji ta koyar da aikin gona da ke Samaru, Zariya, zallar abin da take koyarwa shi ne aikin gona. Kuma aikin gonar nan ya karkasu kashi-kashi. Misali akwai koyar da dabarun noma dangin hatsi kamar dawa da gero da masara da sauransu. Kuma akwai sashen koyar da dabarun noman itatuwa kamar su lemo da yazawa (kashu) da gwaiba da sauransu. Sannan akwai fannin kiwon dabbobi kamar su shanu da kaji da sauran tsuntsaye da su zomo da kifi. Kuma akwai sashen koyar da yadda za a magance cututtukan kwarin amfanin gona. Akwai sashen koyar da girke-girke. Wadannan su ne abin da wannan kwaleji ke horar da dalibai a kai a matakin karama da babbar Diploma.

Aminiya: Wace  gudunmawa kake ganin wannan kwaleji ke bayarwa wajen bunkasa noma a kasar nan?

Dokta Namakka:  Gudunmawar da wannan kwaleji ke bayarwa wajen bunkasa harkokin noma suna da yawa. Misali kamar yadda na fada wannan kwaleji tana horar da malaman gona da suke fitowa suke horar da manoma dabarun noma na zamani. Kuma akwai kamfanoni masu zaman kansu da suke daukar jami’an da muke horarwa a wannan kwaleji don yi musu aiki. Misali kamar kamfanonin irin shuka da kamfanonin magungunan  kwari da feshi. Bayan haka wadanda muke horarwa suna samun kansu a makarantu inda suke aikin koyarwa kan aikin noma. Wadannan suna daga cikin irin gudunmawar da muke bayarwa wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan.

Aminiya: A baya dalibai da dama ba sa son karanta fannin aikin gona, ganin yadda ake ta kokarin komawa harkokin noma a kasar nan, yaya abin yake a yanzu?

Dokta Namakka: Wato a da wannan al’amari na yadda dalibai ba sa son karanta fannin gona ya zama kamar ruwan dare game duniya. Domin a da idan aka yi maganar aikin noma wato aka ce dalibi ya je ya koyi aikin noma, gani yake yi kamar wata tsohuwar sana’a ce ko yagaggiyar riga da zai dauka ya yafa wa kansa. Kuma duk inda ya wuce yana ganin abin kunya ne a ce ga shi ya zo yana karanta fannin aikin gona a jami’a. Wato suna ganin noma kamar wata kasasshiyar sana’a ce da sai dai mutanen kauye ne kadai za su iya yi. Wannan ne ya sa a da kwalejojin koyar da aikin gona ba sa samun dalibai da yawa saboda kallon  da daliban suke yi wa wannan fanni na aikin gona.

Amma yanzu ganin hankali ya koma kan aikin gona kuma an gano wannan fanni yana bayar da guraben ayyukan yi ga jama’a, yanzu matasa sun gane suna ta shigowa wadannan kwalejoji na koyar da aikin gona. A bana sai da muka rage daliban da muka dauka saboda yawansu.

Kuma wani abin shawa’a shi ne yadda muka dada yin gyare-gyare a manhajar da muke koyarwa a wannan makaranta. Yanzu mun juya manhajarmu mun zamanantar da ita ta yadda dalibi idan ya yi karatu, idan ya fito ba sai ya dogara da aikin gwamnati ko aikin kamfani ba. dalibi zai iya kama sana’ar da zai iya rike kansa da sauran al’ummar da yake tare da su. Wadannan abubuwa sun taimaka wajen jawo mana dalibai a wannan makaranta. Yanzu za ka ga maza da mata suna zuwa wannan makaranta don karanta fannin aikin gona. Abin mamaki a da kafin ka ga mace tana karanta fannin aikin gona da wuya, amma yanzu idan ka ga yadda dalibai maza da mata ke gasar shigowa wannan kwaleji don karanta fannin aikin gona abin zai ba ka mamaki.

Aminiya: A matsayinka na masani kan aikin gona, yaya ka ga yadda al’ummar Najeriya suka rungumi aikin gona musamman a wannan lokaci da wannan gwamnati ta ce a koma  gona?

Dokta Namakka: A gaskiya yanzu an samu ci gaba kan aikin noma a Najeriya. Domin idan ka kalli harkokin noma yanzu a kasar nan ka kuma waiga baya ka kalli harkokin noma a Najeriya, babu shakka za ka ga cewa yanzu an samu ci gaba. Musamman wannan gwamnati da ta fito ta ce a ba da fifiko ga aikin noma.

Magana ta gaskiya hatta wanda ba ya noma a da, yanzu ya rungumi noman. Misali idan ka dubi noman nan za ka ga shi kadai ne yake jawo duk wani mutum da yake wata sana’a. Misali ka dubi likitoci da sojoji da ’yan sanda da injiniyoyi da malaman jami’a duk sun shigo aikin noma. Duk wanda ka san yana yin wata sana’a ko yana aiki a gwamnati ko wani kamfani mai zaman kansa ko wata ma’aikata, bana ya shigo aikin noma. Ka ga an ci gaba a aikin noma a Najeriya. Kwanakin baya na tafi Jihar Kuros Riba na yi ta tambaya kan malaman gona amma ko malamin gona guda daya ban gani ba.  

Don haka gwamnati ta shigo a dawo da malaman gona a inganta su yadda za su rika shiga lungu da sako suna horar da manoma dabarun noma na zamani. Aminiya: Wane kira ke gare ka ga gwamnati kan tallafa wa kwalejojin koyar da aikin gona?

Dokta Namakka: Maganar gaskiya tallafa wa kwalejojin koyar da aikin gona yana da matukar muhimmanci. Don haka muna kira ga gwamnati ta shigo ta tallafa wa wadannan kwalejoji ta hanyar ba su goyon baya tare da tanadar musu da abubuwan da suke bukata. Kamar ajujuwa da dakunan bincike da na’urorin bincike na zamani da motocin noma da sauransu. Sannan gwamnati ta taimaka musu da wadatattun kudaden gudanar da harkokin yau da kullum.

Yanzu misali idan ka duba za ka ga akwai wasu na’urori da tun zamanin Turawa ake aiki da su, a wadannan kwalejoji. Yanzu kuma zamani ya canja kullum ana samun ci gaba. Don haka muna son gwamnati ta shigo ta taimaka wa wadannan kwalejoji, su samu kayayyakin aiki na zamani da kudade don su mike kafafunsu wajen yin gogayya da sauran kwalejojin horar da aikin gona na kasashen duniya.

Misali a watan Nuwamban bara na je Habana babban birnin  kasar Kyuba taro kan aikin gona. Wani abin ban sha’awa wannan taro da muka je a wata kwalejin aikin gona ne aka gudanar da shi. Idan ka ga yadda suke koyar da yadda ake hada maniyyin shanu mace da namiji don a samu shanun da suke bayar da madara mai yawa abin zai ba ka mamaki. Ya kamata mu ma a rika tallafa mana don mu rika gudanar da irin wadannan abubuwa.