✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa kakar tumatir ba ta wuce ba har yanzu a Katsina – Manoma

Manoma tumatir a Jihar Katsina sun danganta yadda har yanzu suke ci gaba da dibar tumatir kan yadda manoma suke noman tumatir din da yawa…

Manoma tumatir a Jihar Katsina sun danganta yadda har yanzu suke ci gaba da dibar tumatir kan yadda manoma suke noman tumatir din da yawa a fadin jihar a wannan kakar.

Rahotanni sun nuna cewa, a bara manoma sun samo sababbin dabaru da suka tallafa musu wajen inganta dashen tumatir da yawa ta yadda za a yi maganin karancinsa a kasuwa da kuma yaki da kwarin da suke addabarsa. Don haka a bana baya ga samun nasara kan gwajin sababbin dabaru sun kuma taimaka wajen tsawaita kakar tumatir din,  kamar dai yadda manomansa suka yi bayani.

Saminu Bala, wani manomin rani wanda yake a garin Tafoki, ya ce wadannan dabaru sun yi musu aiki tun a bara wajen rage karancin tumatir a kasuwanni da kuma kawar da barazanar kwari.

“Ganin yadda dabarun suka yi mana aiki a bara, manoma da dama sun rungumi sababbin dabarun a bana,  wanda hakan ya sanya aka samu kakar tumatir mai tsayi a bana.”

“Ka san akasari karancin tumatir yana farawa ne a tsakiyar watan Maris, sannan yana tsananta a cikin watan Afrilu, inda za ka ga an fara amfani da busasshe tunda yake babu danye,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Wadannan sababbin dabaru sun taimaka wa manoma da dama. Yanzu muna sayar da karamin kwando kan Naira 350 tun a gona, shi kuma babban kwando ana sayar da shi Naira dubu 1 zuwa 1,200. Amma a wasu lokutan mukan sayar kasa da wannan farashi saboda yadda ya yi yawa.”

Wani manomin a Karamar Hukumar Bakori, mai suna Sani Sulaiman, cewa ya yi shirin nan na Babban Bankin Najeriya (CBN), na tallafin bashin noma ya taimaka wa manoma wajen samun sayen injinan ban-ruwa da kuma sayen sauran abubuwan da suke bukata. Wanda hakan ya bunkasa harkar noman rani a yankin.

Ya ce, “Ban da noman rani da manoma suke yi a kusa da madatsun ruwa, manoma da dama yanzu suna zuwa bakin gulabe don yin noman tumatir da sauran kayan gwari. Wannan shi ne dalilin da ya sanya kayan suka samu da yawa sannan suka yi araha a bana.

Sani ya ci gaba da cewa, a halin yanzu manoma na amfani da wani maganin kwari mai suna ‘Tai han’ wajen yakar tsutsa da sauran kwari.

“Ba kamar a baya ba, inda tsutsar tumatir da sauran kwari ke addabar manoma, a bana mun gano hanyar yaki da wadannan kwarin ta hanyar maganin nan na ‘Tai han’ wanda yake da karfin gaske wajen maganin tsutsa,” inji shi.