✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa majalisarmu ta sha bamban da wadanda suka shude – Sanata Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana abin da ya sa sanatoci suke aiki da juna duk da bambancin jam’iyya da ra’ayin siyasarsu. Sanata…

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana abin da ya sa sanatoci suke aiki da juna duk da bambancin jam’iyya da ra’ayin siyasarsu. Sanata Ahmed Lawan ya bayyana haka ne a wajen liyafar da Jami’ar Maiduguri ta shirya a karshen mako. Sanata Lawan yana daya daga cikin fitattun wadanda suka yi karatu a jami’ar.

Ya ce majalisar da yake jagoranta a yau tana da bambanci da sauran majalisun da aka taba yi a kasar nan, domin kuwa ba a la’akari da sabanin siyasa a wajen aiki. “Mun zabi mu hada kai mu yi aiki tare, domin wannan shi ne kishin kasa. Babu bambancin jam’iyyar siyasa. Za ka iya zama dan Jam’iyyar APC a majalisa, ko dan PDP ko kowace jam’iyya. Burinmu yi wa al’ummar kasar nan da suka kai mu wannan wuri aiki.

Muna gode wa jam’iyyunmu, kuma mun yarda da akidu da muradun jam’iyyun, amma mun hadu kan cewa za mu dunkule mu yi wa kasa aiki,” inji shi.