Da Dumi Dumi

Abin da ya sa mu yaki da masu garkuwa da ’ya’yanmu – ’Yan sa-kai

Masu aikin tsaro na sa kai da aka fi sani da ’Yan sa-kai da ke kauyen Girnashe a karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato sun yi arangama da barayin da suka addabe su da satar shanu da sace mutane da kashe-kashe, abin da ya jawo hasarar rayuka da jikata mutane da dama a kauyen.

Mata da yara da wadansu magidanta sunkaurace daga kauyen gaba daya zuwa garin Isa hedikwatar karamar Hukumar Isa don samun mafaka.

Wakilin Aminiya ya ziyarci ’yan gudun hijirar in da ya zanta da su kan wannan kokari da mutanen kauyensu suka yi.

“Mun yanke shawarar yakar wadanda suka yi garkuwa da yaranmu mata 7 ne don ba mu iya biyan kudin da suka nema na fansar yaran da suka yi garkuwa da su. Sun bukaci Naira miliyan 15 ne, duk kauyenmu babu mai Naira miliyan daya. An gaya musu haka a lambar da suka bayar ta hannun wata yarinya daya da suka bari.

Bayan mun sanar da su suka ce ba za su saki yaran ba tunda mu maza ne mu zo mu karbi ’ya’yanmu, da muka ji haka sai muka gayyaci ’yan uwanmu ’yan sa-kai muka taru mun fi dubu a ranar Asabar da safe muka shiga dajin don kwato yaran,” inji wani da aka sakaya sunansa.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa: “Ba mu yi nisa ba muka hangi wadansu mutane a saman dutse suna busa usur kafin mu ankara sai ga barayin ta ko’ina suna fitowa a kan babura Boksa su uku-uku a kan kowane babur. Suka kama harbi ta ko’ina kamar zuma ta taso, bindigogin kwarai ne suke da su, kuma irin yadda harsasai suke ratsa mu ba ma iya lissafa su amma sun fi 100.”

Mutumin mai kimanin shekara 38 da ke da mace biyu da ’ya’ya 7 a kauyen ya ce an kashe musu mutanen a Girnashe sun kai mutum 10 amma bai san sauran na kauyuka ba, sai dai yana ganin suna da yawa, su kuma sun kashe barayin akalla 20, kafin su gudo don tsira da rayuwarsu.

“barayin sun mamaye mu ne da zuba wata hoda da ba mu san da ita ba, mai sanya tsananin jin kishin ruwa duk wanda ya shaka sai ya ji komai ba ya so sai ruwa in bai samu ba kawai nan take zai mutu, mu da muka ji harbin ya yi mana yawa sai muka dawo da gudu ana harbinmu rigar da nake sanye da ita ta yi rugu-rugu,” inji shi.

Ya ce abin da ya daga musu hankali da ban tsaro lokacin La’asar bayan gama artabun sun ga saukar jirgi a dajin ba mu san abin da ya zo aiwatarwa ba.

Malam Halilu Aliyu mai shekara 65 shi ne wakilin mai garin Girnashe, ya shaida wa Aminiya a madadin mai garin cewa garinsu babu jami’an tsaro ’yan sa-kai ne kawai suka sanar da su za su shiga dajin tunda ba su da matsara.

Don haka ya yi kira ga gwamnati ta shiga lamarin ta kawo musu jami’an tsaro a kauyen da makwabtansu.

Alhaji Umaru Sa’idu Isa, Shugaban kungiyar Ci-gaban Matasan Isa wanda shi ne ya jagoranci saukar da ’yan gudun hijirar da samar musu abinci da wurin kwana ya gaya wa wakilinmu yadda suka yi wannan aiki. “A ranar Asabar da wuce ne muka ga mutane da yawa mata da maza sun shigo garinmu daga Girnashe inda aka sace mata 7, da ganinsu sai na tare su inji abin da ya shigo da su, saboda ni ne Sakataren Kwamitin Zakka da Wakafi na Gundumar Isa. Mutanen sun gaya min sun gudo ne saboda garinsu babu lafiya daga nan na kira Sarkin Gobir na Isa suka yanke shawara da Sakataren karamar Hukuma aka kai mutanen makarantar firamaren Maitandu nan take aka ba su abinci kusan buhun shinkafa 12 daga karamar hukumar. Sai Alhaji Umaru Ajiya ya aiko musu da buhu 100, Ma’aikatar Lafiya ta ba su magani a haka ne muke kulawa da su a karkashin jagorancina,” inji Umaru Sa’idu.

Ya ce mutanen sun fi 900 sun zo ne daga kauyukan Girnashe da Gidan Abdulkarim da Maikwanti da wasu biyu, “A Sakkwato ba wani abu da ake yi mana a harkar tsaro, muna kira da jami’0an tsaro su hana ’yan bunburutu sayar da mai ga wanda zai tafi daji da shi kamar yadda aka yi a Zamfara, a kula domin fatattakarsu ce a can suka shigo nan, ’yan sa-kai suna taimaka wa harkar tsaro sosai ya kamata a karfafa su,” inji shi.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya