Da Dumi Dumi

‘Abin da ya sa muka damu da mutuwar mata yayin haihuwa’

Gidauniyar Sultan da ke yaki da matsalar mutuwar mata yayin haihuwa da sauran matsalolin iyali a jihohin Arewa, ta bukaci karin azama wajen fadakar da iyali kan muhimmancin yin awo ga mata masu juna biyu da kuma tabbatar da cewa suna zuwa asibiti a lokacin da alamun nakuda suka bayyana.

Gidauniyar wadda aka kafa a shekarar 2014 ta kunshi sarakunan gargajiya da shugabannin addini a matsayin mambobin kwamitin amintattatu na kungiyar a karkashin shugabancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

Ko’odinetan Gidauniyar kuma Sarkin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera wanda ya jagoranci sarakuna 19 suka wakilci masarautun jihohin Arewa a yayin wani taro a Abuja a ranar Talatar makon jiya, ya ce gidauniyar ta damu matuka da alkaluman da ake fitarwa daga kafofin watsa labarai kan mace-macen mata wajen haihuwa a yankin da ke cewa a kullum ana rasa kamar mata 200. Ya ce gidauniyar na kokarin tattara bayanai a kan ikirarin ta hanyan amfani da shugabannin unguwanni a duk lokacin da aka samu rahotun mutuwar uwa ko kuma jariri da bai kai wata biyar ba.

Ya ce aikace-aikacen gidauniyar wanda ya hada da rangadi da shirya kwasa-kwasai ga masu fadakarwa da ke da ofisoshin rassa a yankin, ya samu tallafin Naira milaiyan 30 daga Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya, (UNFPA). Sarakunan sun kuma tattauna kan yadda za su fadada ayyukan gidauniyar a badi.

Taron ya tattauna kan yawaitar matsalar fyade ga yara mata kananan da ake danganta shi da tsubbace-tsubbuce ko sanadiyar tu’ammali da kwaya, inda suka bukaci karin fadakarwa musamman ta bangaren malaman addini. Sauran batutuwan da aka tattauna a kai sun hada da tabbatar da cewa ana gwajin jini a tsakanin masu niyyar yin aure, tare da nuna muhimmancin ba da tazarar haihuwa don samun cikakkiyar lafiya ga uwa da danta gabanin a yaye shi.

ADVERTISEMENT

Babbar wakiliyar Hukumar UNFP a Najeriya Hajiya Rabi’atu Sageer tana cikin wadanda suka gabatar da jawabi a yayin taron.

Share