✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka karrama shugaban Kamfanin SLP – Ibrahim Small

Kungiyar Daliban Kimiyyar Harshe na kasa (NALLS) reshen Jami’ar Bayero da ke Kano ta karrama shugaban kamfanin fassara na SLP da ke Kano, Kwamrade Bello…

Kungiyar Daliban Kimiyyar Harshe na kasa (NALLS) reshen Jami’ar Bayero da ke Kano ta karrama shugaban kamfanin fassara na SLP da ke Kano, Kwamrade Bello Sagir a matsayin gwarzo a harkar fassara na bana.

Da yake bayyana dalilinsu na karrama Kwamrade Bello Sagir, shugaban kungiyar na Jami’ar Bayero, Ibrahim Aminu Isah (Small) ya bayyana cewa, “Dalilin karrama Kwamrade Bello Sagir a matsayin ‘Gwarzo Mai Sana’ar Harshe Na 2018’ shi ne yadda ya jajirce wajen ganin ya samar da abin yi ga masu karatu a wannan bangare. Shi kadai ne wanda muka sani ya assasa sana’ar da ta shafi harshe bayan kammala Digirin Farko a jami’a bangaren Kimiyyar Harshe. Kuma hakan ya haskaka mana yadda za mu dogara da kanmu bayan mun kammala digirinmu a kimiyyar harshen. Domin wannan ne da wasu abubuwa, muka ga lallai ya cancanci a karrama shi,” inji Ibrahim.

Da yake bayanin godiya, Kwamrade Bello cewa ya yi, “Ina matukar farin ciki da godiya ga kungiyar NALLS reshen Jami’ar Bayero inda na yi karatu. Allah Ya sakawa duk shugabanninta da alheri, musamman Musa Jibril (Ekuity), Mace mai kamar maza, Zakiyya Aliyyu Mj da kuma madugu wato Ibrahim Aminu Isah (Small). Allah Ya sa ku gama karatu lafiya, Ya kuma sanya albarka a ciki. Wannan lambar girmamawa da kuka bani ba karamin karfafa min gwiwa za ta yi ba a kan wannan sabuwar sana’a da na kirkira a Jihar Kano ta sana’ar harshe.

A baya daliban da suka yi karatu na harshe kamar Hausa, da Turanci, da Larabci ko Faransanci ko kuma na kimiyyar harshe irin wanda na yi, sukan dauka cewa in dai ba su rike alli ba, ba za su samu hanyar samun taro da sisi ba, amma ni kuma da taimakon takwarorina sai muka ce wannan batu ba haka yake ba!

Tunda muna da wadatattun malaman makaranta, to bari mu mu yi amfani da iliminmu da kuma baiwarmu mu tsunduma a cikin sana’ar harshe koda kuwa dubban daruruwan nairori da na saka a sana’ar za ta dulmiya ta zama asara.

“Daga karshe ina taya murna ga duk wanda ya yi ko kuma yake yin karatu mai alaka da harshe sannan ya sani cewa Allah Ya ba shi babbar sana’a domin samun rufin asiri da watakila ma samun arziki musamman a wannan karni na 21. Idan kana so ka zama mai kudi ta hanyar yin amfani da biro, to ka yi karantu da gaske na harshe kowane iri ne ko kuma ka karanta Kimiyyar Harshe, ka kuma fara sana’ar tu’ammali da harshe,” inji Kwamrade Bello.