Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Abin da ya sa muka saki Dasuki da Sowore – Gwamnati

Abin da ya sa muka saki Dasuki da Sowore – Gwamnati

  • Ba na kulle da kowa kan tsare ni -Dasuki

 

Ministan Shari’a, Alhaji Abubakar Malami ya ce jin kai da biyayya ga umarnin kotu ne dalilan da suka sa gwamnati ta saki tsohon Mai Bada Shawara ta Fuskar Tsaro Kanar Sambo Dasuki da mamallakin jaridar Sahara Reporters, Omowole Sowore.

A ranar Litinin ce gwamnati ta saki Sambo Dasuki bayan shafe sama da shekara hudu a tsare bisa zargin cin hanci da rashawa da karkatar da kudin sayen makamai domin yaki da Boko Haram.

A tattaunawarsa da BBC Abubakar Malami ya ce gwamnatin ce ta ga dacewar yin biyayya ga umarnin kotunan kasar da suka bayar da belin Sambo da Sowore, duk da cewa tana da damar ci gaba da tsare su, saboda  ta kalubalanci matakin kotunan.

“Ba ka da wani dalili da za ka ambata a matsayin hujja bayan dalili na sha’awa da da’a da abin da ya danganci doka da umarni na kotu,” inji Malami.

Ya kara da cewa an sako su ne “A bisa dalilai na jinkai, duk da yake Gwamnatin Tarayya tana da hakki na ta ci gaba da rike su a lokacin da take kalubalantar sakinsu, har a kai matuka a Kotun Koli.”

Wadansu ’yan Najeriya suna da ra’ayin cewa an saki Sambo Dasuki da Sowore ne saboda matsin lambar Amurka, musamman ganin cewa Sowore yana da shaidar zama dan Amurka.

Sai dai Abubakar Malami ya musanta haka, inda ya ce babu wani matsin lamba da suka fuskanta daga kowace kasa kafin sakin mutanen.

“Karya ce tsagwaronta cewa Ofishin Antoni Janar ko Gwamnatin Najeriya ta samu wata takarda daga wadansu ’yan majalisa ko wadansu sanatocin Amurka,” inji shi.

Ya kara da cewa “Har maganar nan da ake babu wata takarda a hukumance da muka karba daga bangaren Amurka ita kanta, dangane da abin da ya danganci wannan batu.”

Tun a ranar 1 ga Disamban 2015 aka kama Sambo Dasuki bisa zargin amfani da kudin sayen makamai wajen yakin neman zabe.

Kotuna da dama sun bayar da belinsa, amma gwamnati ba ta yi aiki da hukuncin kotunan ba sai yanzu.

Gwamnatin Tarayya ta ce a yanzu za a ci gaba da shari’ar Dasuki da Sowore kan tuhume-tuhumen da ake yi musu.

A wani bangaren kuma, sako Dasuki da Sowere ya sa mutane suna tambayar yaushe za a sako Shugaban Kungiyar Shi’a ta IMN Sheikh Ibrahim Zakzaky

Game da wannan, Ministan Shari’a ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumi na yin katsalanda a wata shari’a da take hannun gwamnatin jiha.

A wata zantawarsa da Muryar Amurka jim kadan bayan sako shi, Kanar Sambo Dasuki ya  ce kaddara ce daga Allah kama shi da aka yi, sannan ya ce a shirye yake ya kare kansa a kotu.

“Na daina zuwa kotu ne saboda an ki amincewa da umarnin kotu a sake ni bayan ta bayar da belina. Amma a shirye nake in je in kare kaina.”

Game da rade-radin da ake cewa Shugaba Buhari yana yi masa ramuwar gayya ce, Dasuki cewa, “Abin da na sani kawai shi ne wannan kaddara ce daga Allah. Ba ni da wani abu tsakanina da kowa. Na fi karfin haka.”

Ya kara da cewa, “Jahilci ne ka sa mutum ya yi tunanin cewa wani ne ya jefa shi cikin wani hali. Komai daga Allah ne. An tsare ni na shekara 4, kuma yanzu na fito, sannan Allah kadai Ya san gobe. Kawai dai ya kamata a rika yin adalci da gaskiya a komai.”

Sai ya gode wa mutane da suka rika yi masa addu’o’i, “Mun ga sakamakon addu’o’insu,” inji shi.

Da aka tambaye shi ko yana fama da wani ciwo, sai ya ce, “Ina cikin koshin lafiya.”