Da Dumi Dumi

Abin da ya sa mutane suke hankoron fim din Game of Thrones

Mutane da dama na ta ce-ce ku-ce a shafukkan sada zumunta kan wani shahararren fim da ake yi  zango-zango da ake kira Game of Thrones.

An fara zangon farko na fim din ne a shekarar 2011, kuma bana ne za a kammala, kamar yadda masu shirya fim din suka bayyana.

A cewar mutane, duniya ta dade ba ta ga fim din da ya shahara kamarsa ba.

A jerin fina-finan da suka fi karbar lambobin yabo na Emmy’s, wannan fim ne ya zo na hudu kuma ya shiga kundin tarihi da nuna bajinta na Guiness sau shida.

Haka kuma fim din Game of Thrones ya habbaka yawon shakatawar Arewacin Ireland, kasancewar a kasar aka dauki fim din. Dubban masu kallon fim wanda yake zangonsa na karshe suna ci gaba da ziyartar inda aka dauki fim din a Arewacin Ireland.

ADVERTISEMENT

Yawancin mutanen da ke ziyartar wurin da aka yi fim din dai, sun fi sha’awar zuwa Westeros da Winterfell kasancewar nan ne manyan garuruwan da aka fi dauka a fim din.

A cikin makonni masu zuwa za a san makomar manyan ’yan fim din kamar su Jon Snow da Daenerys Targaryen da kuma Lanisters.

Ana kiyasta cewa Arewacin Ireland zai fuskanci habbakar tattalin arziki saboda yadda fim din ya shahara, kamar yadda John McGrillen wanda shi ne shugaba mai kula da yawon shakatawa a Arewacin Ireland ya shaida wa BBC.

Wannan fim na Game of Thrones da atakaice ake kira GOAT, Dabid Benioff da D.B Weiss ne suka kirkire shi daga kirkirarrun labarun littafan A Song of Ice and Fire na marubuci George R. R Martins.

An dauki fim din a kasashen Kanada da Kuroshiya (Croatia) da Malta da Moroko da Scotland da Spain da Amurka da kuma Arewacin Ireland inda aka fi daukar fim din.

Marubucin ya kware matuka wajen rubuta littafi da tsarin nishadin hululu, wanda a kan haka ne aka tsara fim din.

An dauki shirin ne a kirkirarrun nahiyoyi na Westeros da Essos, kuma an tsara shi a kan jigo uku. Na farko a kan wata kujerar mulki na karfe ne na masarautu  bakwai, inda masarautun suke ta fafatawa a kan mallakarsa. Na biyu ana fafatawa ce a kan tsohon Sarki, wanda aka tsige, kuma yake kokarin dawowa sarauta. Sai jigo na uku wanda yake nuni a kan fadawan masarautar wadanda suke kokari ba dare ba rana wajen kare martabar masarautar daga mahara da wasu halittun tsafi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya