Aminiya

Abin da ya sa na bar Kyaftin a Wikki na koma Kano Pillars – Abdullahi Musa

Abdullahi Musa

Abdullahi Musa sannannen dan wasan kwallon kafa ne da yake jan zarensa a yanzu a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars. A hirarsa da Aminiya ya bayyana takaicinsa kan cire Pillars da aka yi daga gasar Zakaru ta Afirka da kuma burinsa a nan gaba:

 

ADVERTISEMENT

Wane ne Abdullahi Musa?

Sunana Abdullahi Musa, an haife ni a Tudun-Maliki a birnin Kano. Kuma na fara buga kwallon kafa tun ina yaro. Sannan na fara buga wa kungiyoyi na unguwa daga biSani nA fara buga wa kungiyoyin rukunin ’yan dagaji na jiha. Na yi kungiyoyi da dama amma kungiyata ta farko ita ce Kungiyar Pama. Sannan na zo na fara buga rukuni na uku ajin jiha da Kungiyar Ramsy ta Gidan Sarki inda muka samu nasarar hawa aji na biyu na jiha kafin in koma wata kungiyar kwallon kafa a Abuja inda a can ma na share shekara daya sannan likafa ta ci gaba na koma Kungiyar Wikki da ke Bauchi.

ADVERTISEMENT

Yaya kake ji kan yadda aka yi saurin fitar da Kungiyar Kano Pillars daga gasar Zakaru ta Afirka?

A gaskiya ban ji dadi ba sam, ganin yadda muka fara da zimma da fatar za mu taka rawa mai kyau don ganin mun cinye wannan gasa. To amma babu abin da za mu ce sai dai  haka Allah Ya kaddara. Don haka za mu ci gaba da mayar da hankali ga sauran wasanni.

Me ya sanya ka bar Kungiyar Wikki Tourist ka dawo Kano Pillars?

Gaskiya mutane na mamakin barin Wikki da na yi ganin cewa ni ne Kyaftin din kungiyar. Amma wannan ba wani abin mamaki ba ne, ganin ni a wurina yin haka samun ci gaba ne. Kuma ita kanta Pillars din ta share wajn shekara uku tana zawarcina amma Allah bai nufa na dawo ba sai a wannan lokaci.

Yanzu mene ne abin yi ga Kano Pillars ganin cewa an fitar da ita daga gasar Zakarun Afirka?

Ai mu yanzu tuni hankalinmu ya dawo wajen gasar Firimiya ta Najeriya. Mun fara atisaye don ganin mun ci wasanninmu na nan gaba.

Ko kana da burin buga wa Najeriya kwallo a nan gaba?

Sosai ma kuwa ina cike da fata da kuma yakinin zan buga wa Najeriya kwallo da yardar Allah. Kuma ina sa ran zan bada gagarumar gudunmawa in har aka ba ni wannan dama.

Da a ce ba Kano Pillar kake buga wa kwallon a yanzu ba, wace kungiya kake so a ce kana buga wa kwallo?

A gaskiya ina matukar son in buga kwallo a Kungiyar Filato United. Saboda da farko ina da yayana a can tare da su, sannan ina sh’awar buga musu kwallo ba tun yanzu ba.

Wane matsayi Kungiyar Kano Pillars take da shi a wurinka a matsayinka na dan Kano?

Pillars tana da matsayi na musamman a wurina, saboda bayan kasancewarta kungiyar wasa ta garina, kuma yanzu ita nake taka wa leda sannan in dai kai dan wasa ne mai taka leda a  Najeriya ya san cewa Pilllars ba kanwar lasa ba ce.

Yaya za ka kwatanta goyon baya da kular da kake samu a tsakani magoya bayan Kano  Pillars?

Suna matukar nuna mini soyayya tare da yi mini addu’a. Ba abin da zan ce musu sai dai Allah Ya bar zumunci.