✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na koma Ifeanyi Ubah – Abdullahi Abubakar

Matashin dan wasa kwallon kafar nan, Abdullahi Abubakar ya bayyana dalilinsa na amincewa da sanya hannu a kwantiragi da kungiyar Ifeanyi Ubah ta Jihar Anambra…

Matashin dan wasa kwallon kafar nan, Abdullahi Abubakar ya bayyana dalilinsa na amincewa da sanya hannu a kwantiragi da kungiyar Ifeanyi Ubah ta Jihar Anambra daga Lukman Academy ta Kaduna.

Abdullahi wanda aka fi sani da Essien ya bayyana cewa ya yi matukar farin cikin zuwa kulob din, kasancewar babbar kungiya ce a gasar Firimiya ta Najeriya wadda kusan kowane dan wasan Najeriya ke gogoriyon zuwa.

Dan wasan na tsakiya, wanda dan asalin Unguwar Hayin Banki ne a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da ke Jihar Kaduna ya bayyana wa wakilinmu cewa, “Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar zuwa wannan babbar kungiya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya. Wannan ba karamar nasara ba ce a gare ni. Yanzu abin da ke gabana shi ne in yi kokari wajen taimaka wa kungiyar domin ta samu ci gaba, sannan in ci gaba da kokari domin samun nasarori masu yawa a nan gaba.”

Game da yadda yake ji kan ya koma sabon waje sai ya ce, “Ai dan kwallo yana iya zuwa ko’ina domin buga kwallo. Babu gida ba dawa a harkar kwallon kafa. Ni dai burina kawai shi ne in fara da sa’a. Kuma cikin yardar Allah za mu samu nasara mai yawa.”

Abdullahi ya ce, “Burin kowane dan kwallo shi ne ya wakilci kasarsa, don haka ni ma ina da burin haka. Sai dai ba na son garaje, don haka ina so in bi abubuwa a hankali har lokacin ya zo. Abin da ke gabana yanzu shi ne in ci gaba da atisaye tare da kokarin gyara da daukar darasi a harkar domin fuskantar kalubalen da ke gaba. Zan so nan gaba in wakilci Najeriya, kuma da yardar Allah burina zai cika.”

A karshe ya bukaci ’yan uwa da masoyansa su ci gaba da taya shi da addu’a domin samun nasara.