Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
Abin da ya sa na koma Katsina United – Gambo Muhammad - Aminiya
Aminiya

Abin da ya sa na koma Katsina United – Gambo Muhammad

Tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Gambo Muhammad wanda kuma dan wasan gaba ne da ya yi suna, ya bayyana wa Aminiya dalilan da suka sanya ya canja sheka daga kungiyar zuwa kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a wata tattaunawa kamar haka:

 

Mun samu labarin ka koma Katsina United da wasa, duk  da ka share shekara 12 a Kano Pillars kuma kai ne Kyaftin dinta, mene ne dalili?

To ka san dan kwallo kamar ma’aikaci ne na wucin-gadi, yau yana nan gobe kuma za ka iya samunsa ya koma wani wuri. Don haka wannan yanayi ne ya sanya na koma Katsina United, amma ba ni da wata rashin jituwa da Kano Pillars kamar yadda wadansu suke zato.

Ko gaskiya ne cewa Kungiyar Katsina United ta ba ka wasu makuda kudi ne ya sanya ka koma can?

ADVERTISEMENT

A’a, a gaskiya ba haka ba ne. Tabbas sun ba ni kudi masu tsoka amma ba irin yadda mutane suke zuzutawa ba. Wannan dai wata shawara ce da na yanke ta kashin kaina.

Me ya jawo ka fara tunanin barin Pillars din ganin cewa kai ne Kyaftin?

To a gaskiya abu na farko da ya sanya na yi tunanin barin Pillars shi ne don in je wurin da za a ba ni cikakkiyar dama ta buga wasanni. Tunda har yanzu taurarona yana haskawa, shekaruna kuma kanana ne a cikin harkar kwallon kafa.

Shin kana nufin a Kano Pillars ba a ba ka damar da ta kamata?

Haka ne, domin za ka ga mafi yawan lokaci ana wasa ina zaune a kan benci, wani sa’in sai a rabin lokaci za a saka ni. Bayan kuma wadanda suke a cikin ba su fi ni kokari ba. Don haka na ga ya dace in koma inda za a rika ba ni dama ina bugawa koyaushe. Kuma Katsina United sun tabbatar mini za su ba ni wannan dama.

Wace irin tarba ka samu a Katsina?

A gaskiya babu abin da zance sai godiya, domin kuwa da na zo Katsina na ga yadda suka tarbe ni sai na ji kamar ina Kano ne. Domin sun fito sun yi mini gagarumar tarba.

Yaya ka ga irin ’yan wasan da sabuwar kungiyar taka take da su?

Tabbas na gamsu da irin ’yan wasan da Katsina United take da su. Domin na ga abokanina da na sani da dama wadanda kuma dukkansu kwararrun ’yan wasa ne. Haka na ga wadansu da kungiyar ta gayyato wadanda duk sanannun ’yan wasa ne.

Kana ganin za ku iya yin wani abin a zo a gani a wannan kakar wasa?

A gaskiya ina sa ran za mu ba marada kunya. Ina sa ran za mu iya cin gasa ta kasar nan da yardar Allah. Musamman idan muka samu goyon bayan da muke bukata.

Wane kira kake da shi ga magoya bayan Kungiyar Katsina United?

Ina kira gare su da su ci gaba da mara wa wannan kungiya baya. Sannan su guji aikata wani abu da zai jefa kungiyar cikin matsala. Domin mu a namu bangaren za  mu tsaya mu buga musu kwallo iya kokarinmu don ganin mu kai ta gaci.

To yaya maganar komawar Kungiyar Super Eagles?

To ka san an sha gayyatata ina buga wa Super Eagles kwallo, kuma burin kowane dan wasa shi ne ya ga yana buga wa kasarsa. Don haka ina nan zan ci gaba da kokari kuma ina sa ran za a sake kirana  don in buga mata. Kuma idan haka ta faru ina tabbatar maka cewa zan yi amfani da damar don ba marada kunya.

To daga Katsina United ina ka dosa, za ka je Turai ne ko kuwa?

To burin duk wani dan wasa da yake bugawa a gida ya je Turai ya buga. Ni ma ina da wannan burin, kuma ina addu’ar Allah Ya ba ni wannan damar domin ba mu da wani zabi face wanda Ya zaba mana. Duk da yake babu wani dan wasa da yake da burin ya fara wasansa ya gama ba tare da ya je ya buga a Turai ba, idan Allah Ya nufa a nan gida za mu yi kwallonmu mu gama wannan ma ba wani abu ba ne da zai zama na damuwa domin akwai ’yan wasa da dama da suka yi wasansu suka gama ba su je ko’ina ba. Abin dai da muke so shi ne mu samu albarka a cikin duk abin da muke yi. Don haka shi ya sa muke bai wa Allah zabi Ya shige mana gaba a duk wasu lamuranmu.