Abin da ya sa na koma Legas da harkokina – Adam A Zango

Shahararren dan wasan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya bayyana kudirinsa na komawa Legas da harkokinsa kacokan. Aminiya ta zanta da shi inda ya bayyana dalilinsa da irin harkokin da zai mayar da hankali,  ya kuma yi waiwaye a kan kalubalen da ya fuskanta a masana’artar fim ta Kannyhood:

 

Me ya sa za ka koma Legas da harkokin ka?

Alal hakika duk abin da zan yi a Arewa na kai kololuwa, ta fuskar sana’ata da kuma magoya bayana, don haka na duba na gani maimakon in ci gaba da tsayawa waje guda ya kamata in yunkura in tafi inda zan kara samun ci gaba. Kamar dalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare idan yana so ya ci gaba da karatu sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami’a, wannan shi ne manufata. Kuma alhamdulilahi da taimakon wadansu daga cikin masoyana da magoya bayana a Legas da na Arewa sun ba ni shawarwari da dama kuma na dauka ina fata Allah Ya shige mana gaba Ya yi mana muwafaka.

 

Wani bangare za ka fi maida hankali a harkokin da za ka yi a Legas?

Dawowata Legas abin da zan fi bai wa karfi shi ne waka. Saboda babu Hausawa ’yan fim a Legas, idan na ce fim zan yi sai dai in koma Arewa in yi ko in gayyato abokan aikina daga Arewa su zo Legas mu yi. Amma ka ga ita waka aba ce da zan yi kayana ni kadai sai dai jefi-jefi in na bukaci wani aikin zan iya zuwa Arewa in dawo. Don haka yanzu hankalina zai fi karkata ne ga waka.

 

Ka yi maganar sai dai ka je Arewa jefi-jefi ka dawo Legas wannan na nufin za ka dawo ne kacokan har da iyalinka?

Tabbas abin da nake shiri ke nan in Allah Ya yarda, na fara harkokina komai ya kankama ina shirin cikin wata shida zuwa shekara daya zan dawo da iyalina gaba daya  nan Legas har da mahaifiyata cikin yardar Allah. Legas gari ne na samun rufin asiri, idan mutum yana so ya ga ya samu rufin asiri mai nauyi, to Legas zai nufa domin a yanzu a Arewacin Najeriya mun samu matsaloli na wargajewar harkokinmu, da lalacewarsu da kuma matsala da muka samu da gwamnati wacce ta yi alkawarin za ta tallafa mana ta gina mana harkokinmu, muka bada gudumwarmu iya yinmu amma har yanzu gwamnati ba ta waiwayemu ba. Babu wani yunkuri da suka yi, don haka dole ta sa duk wanda yake neman ci gaba dole ya yunkura ya fito daga Arewa a wannan harka tamu, kuma ina fata abin da zan samu zai nunnukan abin da nake samu a baya tun shigata harkar. Yanzu in ka gan ni a Arewa sai dai in na je aiki na musamman ko biki ko makamancin haka. Don haka ina yi wa al’ummar Legas da daukacin mutanen Kudancin Najeriya albishir, yadda suka san ni da jajircewa wajen bai wa jama’a nishadi, to ga nesa ta zo kusa, na zo kusa da su. Za su rika ganina a wasanni da bukukuwa, dama a Kudu babu manyan jarumai ’yan wasan Hausa. To yanzu na zo zan cike wannan gurbi zan kuma jajirce domin farin cikin al’ummar wannan yanki da na kasa baki daya da duk masoyana a ko’ina suke a duniyar.

 

Ko kana da shirin yin aiki tare da shahararrun mawakan Legas?

Eh, insha Allahu, a yanzu haka da ka gan ni a nan abin da ya kawo ni ke nan, ina kokarin ganawa da kulla alaka da akalla manyan mawaka biyar a nan Legas, insha Allahu a badi (2020) zan yi wakoki na bidiyo da na murya da Dabido da Borna Boi da Lighter da Tekno da Olamide da kuma Phyno duk a badi in Allah Ya yarda, kuma yadda wadansu ke tunani cewa in mutum ya zo Legas zai lalace abin ba haka ba ne, zan ci gaba da kare mutumcina da addinina da kuma al’adata, zan guji duk abin da bai dace ba, zan kiyaye duk abin da zai taba mutuncina da addinina. Kuma burina shi ne daga martabar harshen Hausa don haka ne na zo in bukasa shi a nan Legas in kuma dabbaka al’adar Bahaushe.

 

Me ya sa ka fita daga Masana’artar Fim ta Kannywood?

Dalilin da ya sa na fita, babu abin da ya rage a wannan masana’anta sai zalunci da sharri da cin mutunci a kaina. Ban ce a kan kowa ba, me ya sa za ka zauna a wajen mutanen da suke cin mutumcinka, suke yi maka kazafi, suke yi maka sharri, suke neman lallai sai sun binne ka da ranka? Wannan shi ne dalilin da ya sa na yanke hukuncin barin Masana’artar Kannywood, wannan yana cikin abin da ya ba ni kwarin gwiwar da na tattara na bar Arewa na dawo Legas.