✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abin da ya sa na yanke mazakutata’’

Mutanen da ke makwabtaka da barikin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a Sabon gari ta Jihar Taraba za su dade suna ta’ajibin abin da ya…

Orsian Yusuf a kan gadon asibitiMutanen da ke makwabtaka da barikin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a Sabon gari ta Jihar Taraba za su dade suna ta’ajibin abin da ya faru a ranar alhamis 7 ga watan Nuwambar nan, inda wani magidanci ya yanke mazakutarsa saboda matarsa ta juya masa baya.

Shi dai wannnan mutum mai suna Orsian Yusuf, dan shekara 39, ya ce ya yanke shawarar yanke mazakutar tasa ne saboda ya samu saukin mawuyacin halin da ya fada saboda kaurace masa da matarsa ta yi.
Makwabta dai sun bayyana cewa, Yusuf, wanda dan asalin karamar Hukumar Karim Lamido ne da yake sana’ar lankwasa rodi, ya fara nuna wadansu halaye da ba a sansa da su ba ne kwanaki kadan kafin ya aikata wannan aika-aikar.
Kafin ya aikata wannan danyen aikin, Yusuf sai da ya kulle kansa na tsawon kwanaki uku yana ta wadansu surutai na surkulle.
Da makwabta suka fahimci tambelen da Yusuf yake yi, sai suka yanke shawarar kiran limamin cocinsu domin ya yi masa addu’a, domin suna tunanin aljannu ne suka taba shi.
Lokacin da limamin cocin ya isa wurin sai makwabtan da suka taru a wurin suka balle kofar da karfin tsiya, inda suka tarar da Yusuf kwance male-male a cikin jini. Nan da nan aka garzaya da shi asibitin gwamnatin tarayya da ke Jalingo domin a duba shi.
An ce Yusuf ya yi amfani da wata tsohuwar reza ce ya yanke mazakutar tasa, wanda hakan ya nuna cewa lallai ya ji jiki a yayin gudanar da wannan aika-aikar.
A yayin da yake kwance a gadon asibiti, Yusuf ya ce ya aikata wannan danyen aikin ne saboda bata masa rai da matarsa ta yi, shi ya sanya ya yanke mazakutar tasa domin ya huta da harka da kowace mace. Ya bayyana matar tasa da cewa, hatsabibiya ce kuma fitinanniya da za ta iya kashe mutum.
Yusuf ya ce tun da matarsa ta barshi shekaru hudu da suka gabata ya kasa kusantar kowace mace. Kuma ya sha bayyana halin damuwar da ya fada da kuma rashin samun barci cikin dare saboda rashin ganin matarsa da kuma diyarsa na tsawon lokaci.
Sai dai kuma wakilinmu ya gano cewa Yusuf dai ba shi da mata kamar yadda ya nuna, ‘ Wannan mutumin bai yi aure ba, wadansu daga cikin ‘yan uwansa da suka zo nan muka tambaye su labarin matarsa sun ce bai yi aure ba, inji wata majiya a asibitin.’’
Makwabtansa ma sun tabbatar da cewa Yusuf bai taba yin aure ba, inda suke ganin ya aikata wannan danyen aikin ne saboda tabuwar hankali da ya samu. A yayin da wadansu kuma suke ganin aljannu ne suka shafe shi har ya kai ga aikata hakan, wadansu kuma suka ce kwaya ce yake sha.
Amma likitan da yake kula da shi Dakta Nyadze Dabine ya ce, ko dai Yusuf yana fama da tabuwar hankali ne ko kuma kwaya ce ta yi masa karo ya yi wannan mugun aikin.
Likitan ya ce, Yusuf ya yanke mazakutar tasa ne gaba daya ta yadda jini ba ya bi ta wajen, domin haka ya riga ya yi asarar azzakarin nasa gaba daya.
Dakta Dibine ya bayyana cewa, mutumin zai rayu kuma ya ci gaba da harkokinsa amma ba zai iya saduwa da mace ba, duk da cewa zai rika jin sha’awar saduwa da mace.
A cewarsa, sha’awar saduwa yana tasowa ne daga kwakwalwa, domin haka mutumin zai cigaba da sha’awar saduwa da mace a tsawon rayuwarsa.
kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Yusuf a lokacin da yake kwance a gadon asibiti ya ci tura, saboda jami’an asibitin sun ce ba zai yi magana da manema labarai ba sai an sallame shi daga asibitin.
Wani jami’in asibitin ya bayyana wa wakilinmu cewa, akwai alamun Yusuf yana fama da tabuwar hankali shi ya sanya yake magana irin na shirme. Domin mafi yawan maganganun da yake yi soki-burutsu ne kawai da bai kamata a kama ba.
Wakilinmu ya gano cewa majinyacin yana samun sauki a asibitin gwamnatin tarayya da ke Jalingo.