Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Abin da ya sa Najeriya ke fuskantar barazanar tsaro – Gadzama

Mista Afakriya A. Gadzama, a yayin wani taro a kwanakin baya
Mista Afakriya A. Gadzama, a yayin wani taro a kwanakin baya

Mista Afakriya A. Gadzama shi ne tsohon Shugaban Hukumar Tsaro ta DSS a lokacin mulkin Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa wanda aka nada a shekarar 2007. Ya bayyana hanyoyin da za a magance matsalar tsaro a Najeriya.

Muna ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a kasar nan ko, wane ya fi zama mafi kalubale?

ADVERTISEMENT

Abin bakin ciki shi ne akwai matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta sosai a yanzu, wanda ya fi fice shi ne matsalar ’yan ta’adda da ke Arewa maso Gabas, sai garkuwa da mutane da kisan gilla, sai kuma fashin teku da ya yi fice a yankin Neja-Delta. Wadannan matsaloli ko shakka babu suna kara matsalar tsaro a kasar nan. Misali, yawan karuwar ta’addanci da karuwar miyagun makamai a hannun mutane.

Idan ba a mance ba, jami’an tsaro sun koka a kan yawaitar miyagun makamai a cikin kasar nan. Bugu da kari kuma ga kalaman batanci da ke fitowa daga bakunan ’yan siyasa wanda ke jefa dar-dar a zukatan jama’a. Wannan kawai zai nuna maka irin matsalolin tsaro da kasar nan ke fama da su. Akwai wasu abubuwa da ke samar da rashin tsaro wadanda dole sai an fahimce su idan har ana son magance matsalar. Kashi sittin na matsalolin tsoro a kasar nan suna faruwa ne saboda rashin cika alkawura ga jama’a da shugabanni ke yi. Rashin adalci da rashin tausayi na shugabanni ga talakawansu. Wannan ne ya samar da rashin tagomashi na gwamnati ga jama’a. Yanzu mun kai lokacin da mulki da shugabanci suka zama abin son zuciya. Babu wanda zai iya tabbatar maka da cewa akasarin wadanda aka zaba su wakilci jama’a na yin hakan kamar yadda ya dace ba tare da son zuciya ba.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, daya matsalar da ke kawo rashin tsaro ita ce rashin kishin kasa a zukatan shugabannin da aka zaba a dukan matakai. Wannan yana matukar shafar romon dimokuradiyya da ’yan kasa ke bukata daga wajen ’yan siyasa. Maganar gaskiya kuma, jami’an tsaro ba su da kwarewa da kayan aikin da za su taimaka musu wajen magance rashin tsaro a kasar nan. Sojoji da sauran jami’an tsaro ba su da isassun ma’aikata da za su iya dakile wannan matsala. Bana shakkar cewa sojoji da sauran jami’an tsaronmu za su iya magance matsalar ta’addanci da garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga idan har aka ba su kayan aiki kamar jirage masu sarrafa kansu da masu saukar ungulu domin leken asiri.

Ka bayyana cewa rashin shugabanci na kwarai musamman a Arewa na daya daga cikin dalilan da suka janyo rashin tsaro, ko za ka yi karin bayani?

Ai ba ka bukatar dogon tunani kafin ka fahimci cewa rashin shugabanci na kwarai ne ya fi shafar yankin Arewa. Kuma kada ka manta cewa yankin ne mafi talauci a kasar nan, musamman ta fannin rashin masana’antu da za su dauki mutane aiki. Bari in ba ka wani misali na farko shi ne, danne kananan hukumomi a kasar nan. Bayanai sun bayyana cewa yanzu gine-ginen kananan hukumomi suna ne kawai a yankin na Arewa. Domin ana karkatar da kudadensu, wanda hakan ke hana su yi wa jama’a ayyukan da suka dace. Rashin bai wa kananan hukumomi kudadensu da jihohi ke yi ya kara yawan talauci a yankin.

Kai akwai zargin da ake yi cewa hatta kudaden zaizayar kasa da ake raba wa jihohi ba a amfani da su yadda ya kamata. Babbar yaudarar ita ce batun kudade da ake bai wa ’yan majalisa domin aiwatar da ayyuka a mazabunsu. Yawancin kudaden babu wanda zai ce ga inda ake kai su. A yayin da wadansu ’yan majalisar daga wasu bangaren kasar nan ke aiwatar da ayyukan ci gaba a mazabunsu, a nan Arewa babu abin da ke gudana a wasu jihohi. A yanzu haka an samu gibi a tsakanin yankin Arewa da sauran yankunan kasar nan a fannin ilimi da kiwon lafiya da zuba jari. Hadarin da wannan ke da shi a fannin tsaro shi ne, idan nan da shekaru masu zuwa ba a magance matsalolin nan ba, yankin Arewa zai zama matattarar duk wani rashin tsaro ko rikici.

Baya ga haka kuma akwai bincike da aka aiwatar da ya nuna cewa matasan Arewa ne kan gaba wajen tukin Keke NAPEP da masu sayar da ruwa kuma su ke yin kananan ayyuka a yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Wannan ke muna maka lalacewar shugabanci a yankin.

Ta yaya wannan ya shafi rashin tsaro?

Me kake ganin ya hura wutar ta’addanci a yanken Arewa maso Gabas? Babu wani abu illa rashin kishin kasa na wasu daga cikin shugabanninmu da suka ki yin abin da ya dace, musamman domin inganta rayuwar talaka. Rashin adalci da kuma saka kabilanci da son rai sun taimaka matuka.Bari in fadi maka gaskiya yankin Arewa ba wai kawai wulakanci da son rai na shugabanni kawai suke fama da shi, wanda ya mayar da yankin wani wajen zubar da jini ba, a’a akwai gibi tsakanin Arewa da Kudu musamman ta fannin samar da aikin yi da samar da ababen jin dadin rayuwa, wanda ke damun jama’a har ta kai ga ana iya canja wa mutum tunani.

Mene ne ra’ayinka game da yaki da ta’addanci da ake yi a yankin Arewa maso Gabas?

Akwai wasu abubuwa da ba zan ce komai a kai ba a bayyane amma bari in sake fada maka, Shugaba Buhari ya yi kokari wajen samar da shugabanci domin dakile ayyukan ta’addanci a fagen fama. Jami’an tsaro ma sun cancanci yabo, musamman wajen kokarin karya lagon ’yan ta’adda. Sai dai kuma wannan ba zai hana a ce yaki da ta’addanci ya samu koma baya ba a ’yan watanni uku da suka wuce, domin ’yan ta’addan sun mamaye wasu garuruwa da inda soji suke a yankin. Dole soji su sake dabara domin dakile su. Kamar yadda na dade ina fadi ne cewa, abin da kawai zai kawo karshen ’yan ta’addan nan shi ne a samar wa jami’an tsaro makamai na zamani da jiragen sama da masu saukar ungulu da manyan bindigogi da karin ma’aikata. Wannan kuma dole a fahimci cewa ta’addanci wani abu ne da ya shafi tunanin mutum. Saboda haka dole ne a sanya ko samar da hanyoyin canja wa mutanen tunaninsu. Har ila yau wadanda kuma ke amfana da yakin da ake yi dole a bayyana su, domin a hukunta su. Bari in sanar da kai cewa shugabanni na sake duba lamarin da suka shafi yaki da ta’addanci a yankin domin samar da sababbin dabaru.

Ko kana da masaniyar akwai bayanan da ke nuna wadansu da ake zargin ’yan kungiyar IS ne sun shigo Najeriya?

Wannan wani abu ne da ke tabbatar da wani abu da ake ta fadi shekarun da suka wuce, musamman tun lokacin da aka samu labarin cewa ’yan kungiyar IS sun shigo kasashe irin su Mali da Burkina Faso da Nijar, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a yankin Sahel kamar Libya. Ka san daga nan abin da ya rage shi ne Najeriya. Kuma kada ka manta cewa IS din nan na aiki da wani bangare na Boko Haram. Duk wannan na daga alamun da suka sa ayyukan kungiyar ya kara kunno kai a ’yan watannin baya. Babban abin da ya kamata ya dame mu shi ne shirin kasar Amurka na janye sojojinta daga kasashen Syria da Mali. Sai dai idan an maye gurbinsu cikin gaggawa, in ba haka ba kuwa wannan zai kara yawan ayyukan ta’addanci a kasashen Afirka.

An dan samu damuwa kadan a Hukumar DSS a watannin baya, sakamakon samun sauyin shugabanci a hukumar, me za ka ce?

Abin da ya faru a Hukumar DSS a watannin baya ba sabon abu ba ne a hukumomin tsaro. Abin fadi kawai shi ne cewa hukumar ta samu shugaba jajirtacce a yanzu. Yana da masaniya a kan abubuwan da suke faruwa a hukumar a shekarun baya kuma kwararre ne. Baya ga haka kuma ya samu goyon bayan shugabannin hukumar da suka yi murabus da kuma wadanda ke cikin aikin a yanzu. Gaskiya ina ganin nada shi da Shugaba Buhari ya yi ya dace. Haka kuma shi kansa Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara a fannin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya dace da mukamin, domin tare za su yi aiki da Shugaban DSS. Wadannan mukamai na da matukar muhimmanci a fannin tsaron kasar nan.

Wace shawara za ka bayar kan batun harin ’yan bindiga a Zamfara da garkuwa da mutane a kasa?

Bari in soma da Jihar Zamfara, gaskiya abin bakin ciki ne matuka da aka bari lamarin ya yi kamari. Gwamnati da jami’an tsaro ya kamata a ce sun dauki darasi daga abubuwan da suke faruwa a sauran sassan kasar nan. Ya kamata a ce an kara yawan jami’an tsaro sannan a tabbatar da an samar da kayan yaki ko na fada isassu. Kuma batun Jihar Zamfara wani abu ne da ke da sarkakiya. Hare-haren na nuna rikon sakainar kashi da gwamnati ta yi wa batun ne tun farko da kuma lalacewar gwamnati da ’yan siyasa, wadanda ke fakewa da batun ayyukan ’yan ta’addan. Dole ne a dauki dukan matakan da suka dace wajen hana yaduwar ta’addanci zuwa jihohi makwabta. Dole kuma jami’an tsaron sirri su tabbatar da cewa wadansu mugayen kungiyoyi ba su fakewa da sunan ’yan ta’addan ba wajen haddasa kashe-kashe a kasar nan. Kuma akwai bukatar ’yan siyasar Zamfara su tashi tsaye wajen ba da tasu gudunmawa domin kawo karshen fitinu a jihar.

Sauran kashe-kashe da suke faruwa a Arewa ta Tsakiya akwai alamun an shigo da bakin aure cikin kasar nan. Dole sai an mayar da hankali a kan haka, in ba haka ba kasar nan ba za ta taba zama lafiya ba. Sannan akwai muhimmanci a samar da wani shiri da zai tabbatar da zaman lafiya a kasa. Kuma a maganace matsalar rashin ma’aikata a jami’an tsaro. Abin da ya sa batun rashin tsaro ya- ki-ci-ya-ki-cinyewa shi ne rashin isassun jami’an tsaro a sassan kasar nan.  Game da batun sace-sacen mutane dole ne a yaba wa sashen yaki da garkuwa da mutane na  ’yan sanda tare da jami’an DSS a bisa kokarin da suka yi. Ina ganin kokarinsu zai karu ne idan aka kara samar musu da kayan aiki na zamani. Wannan matsala ta garkuwa da mutane zan dora ta ne a kan rashin samar da shugabanci nagari da rashin isassun jami’an tsaro da za su yi aiki tukuru.

Ka nuna damuwar cewa akwai alamun da ke nuna wadansu na neman kirkiro rikici a Arewa me ya sa ka ce haka?

Su wane ne kuma me ya sa ake samar da rikice-rikicen addini da kabilanci a wasu jihohin kasar nan? Su waye ke makarkashiyar yin amfani da addini da kabilanci domin kawo rikici a Arewa? Daga karshe me ya sa ba mu da hadin kai a siyasance a Arewa kamar yadda ake samu a sauran sassan kasar nan? Yaudarar kai ne idan ka dauka kawai abu ne da ke faruwa ba tare da dalili ba. Ba ka bukatar wani malamin tsibbu ya fada maka dalilan da suka sa Arewa ke rasa martabarta a kasar nan. Zancen kawai shi ne akwai wadansu daga waje da ke amfani da rashin hadin kan Arewa domin sake raba yankin.

Yawan rikice-rikicen addini da danne hakkin wadansu a yankin da rashin girmama shugabannin yankin na daga cikin abin da ’yan waje ke amfani da shi wajen raba kawunan al’ummar yankin bayan sun samu hadin kan wadansu ’yan Arewa marasa kishin yankin. Wanda hakan ya saba da tunani da koyarwar shugabanninmu na farko masu kishin Arewa.

Mene ne tunaninka a kan zabe mai zuwa?

Ba na jin tsoron komai game da zabe mai zuwa domin an samu canji a wasu bangarori. Shugaba Buhari ya riga ya ba da tabbacin gudanar da zabe mai inganci. Abin da kawai ya rage shi ne masu ruwa-da-tsaki su ba da goyon baya. Hukumar zabe da jami’an tsaro dole su maido da martabarsu da ta nemi lalacewa kafin zaben shekarar 2015. Jihohi da ya kamata a mayar da hankali a kai a lokacin zabe da bayan zabe su ne Akwa Ibom da Kaduna da Benuwai da Borno da Bayelsa da Kano da Ribas da Bauchi. Sauran su ne Adamawa da Ogun da Kwara da Nasarawa. Dole mu tuna wa junanmu cewa zaben nan mai zuwa ba karamin zabe ba ne. Zabe ne tsakanin fadawa cikin duhu ko kuma zaben buri da ci gaba.