✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa nake samun nasarori a kwallon kafa – Yusuf Chaki

Yusuf Yahaya Alasan da aka fi sani da Chaki shi ne Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Gombe United, a hirarsa da Aminiya ya bayyana…

Yusuf Yahaya Alasan da aka fi sani da Chaki shi ne Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Gombe United, a hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara wasan kwallon kafa da nasarorin da ya samu da kuma shawararsa ga matasa masu sha’awar harkar kwallon kafa:

 

Mene ne matsayinka a Kungiyar Gombe United

Bayan kasancewata dan wasan kungiyar har wa yau ni ne Kyaftin din Kungiya Kwallon Kafa ta Gombe United.

Yaushe ka fara buga kwallon kafa?

Na fara buga kwallo ne tun ina karami a makarantar firamare, inda idan an fito tara mukan yi wasa da abokaina ko mu buga tsakanin aji da aji. Tun a lokacin wasu ajujuwan sukan yi hayata in buga musu. Daga nan sai na fara yi a filin wasa na unguwarmu, amma a boye saboda mahaifana suna yi mini fada don ba sa son suna ganina ina buga kwallo, ga shi kuma ba na son in yi abin da zai bata musu rai. A haka na ci gaba da bugawa a kananan kungiyoyi  har ta kai ga na buga gasar makarantun sakandare ta jiha.

Na fara da buga wa Kungiyar Flash ta  Gombe sannan na koma Tudun Wada United daga bisani na dawo  Kungiyar Liberpool wacce a yanzu ake kira Gombe Warriors. Ba zan manta ba duk da yake ina samun nasarori a cikin wasan, mahaifana ba sa  son ina yin kwallo kamar yadda na fada da farko. Haka kuma an taba kai ni makarantar addini a Maiduguri amma saboda yadda hankalina ya koma kan kwallo sai na kasa zama na dawo gida na ci gaba da buga ta.

A haka wata rana na je wajen wasan na ji ciwo aka dauko ni aka maido ni gida inda mahaifiyata ta yi ta yi mini fada tana cewa dama irin abin da take guje mini ke nan. Amma bayan na buga gasar cin Kofin Gwamna ne kuma na yi kokari sosai duk da cewa ni ne mafi kankanta a cikin ’yan wasan a wancan lokaci, sai iyayena suka lura cewa na riga na yi nisa a  wasan kwallo, don haka sai suka daina yi mini fada, maimakon haka sai suka fara yi mini addu’ar samun nasara. Addu’ar tasu ce ta yi mini tasiri sosai zuwa yanzu.

Da farko an gayyace ni in buga wa makarantar sakandare ta Pilot ta Gombe wani wasa a Abuja a wata gasa ta kasa. Bayan mun samu nasara a Abuja sai muka wuce don buga wasan karshe a Filin Wasa na Kasa da ke Surulere a Legas a wancan lokaci. Daga nan kuma sai muka wuce kasar Ingila inda muka buga wata gasa ta Festibal na ’yan kasa da shekara 16 wanda daga karshe muka samu nasarar zama zakaru. Bayan mun dawo ina nan ina wasa a kungiyar kwallo ta Liberpool ta Gombe sai wani bawan Allah ya ga yadda nake taka leda sai ya kira ni zuwa garinsa. Bayan na je sai ya tambaye ni shin idan ya dauke ni ya kai ni wani gari ba Gombe ba ko zan iya zama in buga kwallo a can?

Take na ba shi amsar cewa ko yanzu ma a shirye nake. Na ba shi wannan amsa ce saboda ganin cewa mahaifana da suke yi mini fada a da, yanzu suna taya ni da addu’a ta Allah Ya kara mini daukaka a cikin harkar kwallo. Don haka daga karshe dai ya kai ni kungiyar kwallon kafa ta NPA, suka gwada ni kuma suka dauke ni bayan sun ga na cancancanta. To daga baya kuma sai na dawo nan kungiyar kwallon kafa ta Gombe United wacce ga shi har yanzu na kai ga matakin rike Kyaftin dinta.

Wadanne nasarori ka samu a harkar kwallon kafa?

To, alhamdulillahi, da farko dai ka ga na samu rufin asiri a cikin wannan sana’a ta buga kwallon kafa. A cikinta nake yin komai da ka sani hadi da taimakon ’yan uwa da abokan arziki. Sannan tunda na fara kwallo a firamare nasara nake samu, na rike mukamin shugaban wasa na makaranta a lokacin ina sakandare, na ci kofin gasar makarantun sakandare sau biyu baya ga wasu kofunan da na yi ta ci tare da wasu kananan kungiyoyi. Sannan na yi Kyaftin din Liberpool ta Gombe da na makarantata ga shi kuma yanzu ni nake rike da wannan kambi a Gombe United.

Haka na buga kasar Confederation ta Afirka da kuma gasar Kalubale ta Afirka duk a Gombe United. Kuma na buga wasannin da dama a kungiyar ’yan kasa da shekara 17 ta kasa a matakin neman hayewa zuwa gasar Kofin Duniya na U17 din duk da yake ba a je da ni gasar ta duniya ba.

Mene ne burinka a yanzu?

Burina a halin yanzu shi ne in ga Gombe United ta zo ta farko a gasar Firimiya ta Najeriya. Wannan shi ne babban burina.

Kwanakin baya an ga ’yan wasan kungiyar  Gombe sun kama wuri sun zauna a Kano ko me kuke yi a can?

Mun je Kano ne don killace kanmu, kasan dan wasa sai ana yi ana kula da shi tare da killace shi. Kuma mun yi haka ne don yin atisaye da wasannin sada zumunta a wani mataki na gwaji da sabon mai horar da ’yan wasan wannan kungiya ya dauka don ya tantance ’yan wasan da za su yi masa amfani da su a gasar Firmiya da za a fara. Wannan a takaice shi ne dalilin zamanmu Kano kuma ina ga mu a wajenmu wannan ba wani abu ne sabo ba.

Wadanne kalubale kake ganin ’yan wasa daga Arewa suke fuskanta?

A gaskiya muna da kalubale da dama, musamman wajen samun wadanda za su dauki nauyin matasan ’yan wasa zuwa wasu kungiyoyi na kasashen waje.  ’Yan wasa daga Kudu sun yi mana fintinkau ne saboda suna da masu agaza musu wajen daukar nauyinsu. Shi ya sa ma za ka ga ko a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa babu ’yan wasa daga Arewa da yawa kamar yadda babu su da yawa a kasashen Turai. Wannan matsala ce da ta kamata a yi kokarin kawar da ita.

Wane kira kake da shi ga gwamnatin Jihar Gombe da magoya bayan Kungiyar Gombe United?

Da farko ina yi musu godiya bisa goyon baya da soyayya da suke nuna mana. Sannan ina rokonsu  su ci gaba da ba mu goyon baya dari-bisa-dari. Gwamnatin Jihar Gombe kuma ina yi mata godiya ga irin daukar nauyin wannan kungiya da suke yi. Ina fata za su ci gaba da ba mu wannan tallafi da suke yi domin fatarmu ita ce mu ci gasar Firimiya ta kasa a bana in Allah Ya yarda.

Wace shawara gare ka ga matasa masu sha’awar wasan kwallon kafa?

Shawarata gare su ita ce su dage su mayar da hankalinsu a kan wannan sana’a. Sannan su nemi iyayensu su taya su da addu’a domin kuwa  kamar yadda na fada a baya na ga tasirin addu’ar iyaye a rayuwata musamman a cikin wannan sana’a ta kwalon kafa.