✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Shata ya yi min wakoki – Sahabi Liman

“dan Liman yake jikan Liman,Na gode wa Sahabi Liman.kaura za ni da ’yan yarana,Domin in iske Sahabi Liman,Na gode wa Sahabi Liman.”Wannan na daya daga…

“dan Liman yake jikan Liman,
Na gode wa Sahabi Liman.
kaura za ni da ’yan yarana,
Domin in iske Sahabi Liman,
Na gode wa Sahabi Liman.”
Wannan na daya daga cikin wakokin da marigayi Dokta Mamman Shata Katsina ya yi wa Alhaji Sahabi Liman kaura. Duk da cewa marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina wani irin mawaki ne da kudi ko mukami ko sarauta ba su sa ya yi wa mutum waka, Alhaji Sahabi Liman na daya daga cikin mutanen da Mamman Shata ya yi musu wakoki ba ma waka ba. Wakilinmu ya tattauna da Sahabi dan Liman don jin yadda aka yi har Shata ya yi masa wakokin:

Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau

Aminiya: Mene ne takaitatcen tarihinka?
Sahabi Liman: To tarihina dai ba wani mai wahala ba ne, sunana Alhaji Sahabi Liman kauran Namoda, ni haifaffen garin kauran Namoda ne da ke nan Jihar Zamfara, kuma mu ne muka gaji sarautar limanci a garin kaura, domin kakanmu shi ne, ya taimaka wa Namoda suka yi jihadi da Shehu Usmanu dan Fodiyo,
kamar shekara dari da wasu abubuwa suka yi yake-yake na Musulunci.
Aminiya: Kana nufin daga nan ne wannan suna na liman ya samo asali ke nan har ya bi ka?
Sahabi Liman: kwarai kuwa nan ya samo asali, za ka ji ana ce mana gidan Liman a kauran Namoda
Aminiya: Ko za ka gaya mana dangantakarka da marigayi Alhaji Mamman Shata?
Sahabi Liman: To, Alhaji Mamman Shata dangantakata da shi ita ce tun muna yara yana zuwa kaura yana wasa da yaransa, akwai wani kanen tsohuwata ana ce masa Sahabi Jikan Kwaso, to shi ne har ya yi masa waka, a lokacin muna yara. Daga baya, bayan na zama magidanci ina Sahabi Liman ya taba zuwa wajena na yi masa alheri.
Aminiya: To yaya abin ya kai har ya yi maka waka?
Sahabi Liman: Na taba yin wani aure a Katsina, sunan amaryar ana ce mata Maryam, tare da Husaini danbaba Maroki yana Kwatarkwashi, shi mutumina ne, kuma mutumin Shata ne, shi ne ya je ya samu Shata ya gaya masa cewa Sahabi Liman ya yi aure  a Katsina, ya kamata mu je ka gaishe shi. Bayan an dauko amarya daga Katsina, wajen karfe biyar sai ga Shata ya zo kaura gidana, ya zo ya gaishe ni, ya ce ya ji labarin na yi aure. Na ce haka ne amaryar ma suna nan tafe, nan ne aka shirya biki Shata ya yi wasa. Daga nan akwai wani abokina Alhaji Iya-da-Rusa na nemi shawaransa na ce me ya kamata in bai wa Shata? Sai ya ce ya kamata a ba shi mota ce, nan kuwa na dauki kudi Naira dubu 55 cikin dare aka tafi wajen Adamu Dinawa a Gusau aka sawo masa mota mai suna Kwamfuta an samu mota kan Naira dubu 52 da 500, yanzu ana samunta wannan mota ana sayar da ita Naira miliyan hudu da wasu abubuwa. Aka dauke ta aka bai wa Shata, ya ajiye tsohuwar motarsa ya shiga wannan motar shi da yaransa ya koma Funtuwa.
Aminiya: Kana nufin Shata bai fara yi maka waka ba sai da ka ba shi wani abu?
Sahabi Liman: Lallai ya fara yi mani waka ne tun kafin in fara ba shi wani abu, sai dai kafin lokacin yakan zo wajena ya gaishe ni, in kuma yi masa alheri, sai lokacin wannan bikin ne Shata ya fara yi mani wakoki,
kuma na ci gaba da yi masa alheri, kuma wakarsa ta farko ita ce: Sahabi Mijin Mairo dan Liman.” Ita ce ya fara yi mani.
Aminiya: An ce Shata yakan zabi wani lokaci in ya yi sai ya ziyarce ka, yaya abin yake?
Sahabi Liman: Haka ne, domin bayan ya yi mini wannan waka sai ga aurena ya sake tashi a gidan Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da ’yarsa Mariya. Bayan ta kammala karatunta a Amurka sai na ganta na kuma roki marigayi Sarkin Kano aurenta, ya kuma ce to ya ba ni ita. To  a wannan bikin ne na je otel din Kabo, na kama duk dakunan da ke otel din saboda baki. To ashe Shata yana cikin otel din, to da Shata ya samu labari sai ya ce, to shi ne zai dauko amarya. Daga nan ya dauko amarya ya kawo ta kauran Namoda, masu wasa suka yi wasa, nan Shata ya yi wasa har safe, nan kuma ya sake yi mani wata waka da ake kiranta Na-Mariya Jikan Bayero. Wakar tana nan ina da ita, bayan wadannan kuma ya yi mani wata ta “Sahabi dan Limamin kaura” kai ga su nan da yawa, kuma na yi masa kyauta mai yawa.
Aminiya: Ko akwai abin da Shata yake yi wanda yake ba ka mamaki a haduwarku da shi?
Sahabi Liman: Abubuwan da Shata yake yi ai suna da yawa masu ban mamaki, amma akwai so. Idan yana sonka, to zai yi maka waka, don yana da ra’ayi na son mutum, kuma al’amarinsa ba su da iyaka, domin ka ga ni duk inda Shata yake idan azumi ya kai bakwai, sai ya zo Gusau ya kwana kamar karfe tara ya zo mu gaisa, tare da yaronsa Ariya mu yi hira ya koma gida. Shekara ta fi ashirin haka yake, domin saboda
yana amfani da cewa shi Bafullatani ne ni ma Bafullatani ne, to muna da dangantaka ta asali, kuma yana amfani da shi sosai. Kuma ni ma nakan je Funtuwa ina sayen hatsi mu zauna muna hira.
Aminiya: To yaya maganar cewa yana da aljanu shi ya sa yake haka?
Sahabi Liman: To ka san kowa da abin da ya yarda da shi, ni ban yarda da irin wadannan abubuwa ba, ko aljanu ko tsafi da sauransu. Amma na yarda akwai baiwa wadda Ubangiji Yakan sanya wa bawanSa da Yake so. Don haka Allah Yana sonsa kuma Ya sanya masa baiwa da basira, wannan kam al’amari ne na Allah kawai.
Aminiya: Ko ka samu wani kamar Shata cikin wadanda suka yi maka waka?
Sahabi Liman: To, lallai a yanzu kam babu, akwai masu yi mani waka suna da yawa amma babu kamar Shata a wurina.
Aminiya: Mene ne Shata ya taba yi maka wanda ba za ka taba mantawa ba?
Sahabi Liman: Ai na gaya maka, babu kamar yadda yake zuwa wurina idan azumi ya yi, duk shekara sai ya ziyarce ni, mu zauna mu yi wasa da dariya, mu ci mu sha, wannan ai abin farin cikina ne kuma ba zan manta da shi ba har abada. Ciki har da wasu marokinsa daya ana kiransa Ariya a Gusau da wani ana kiran sa da Baba Kwatarkwashi amma duk sun rasu.
Aminiya: Cikin wadanda Shata ya yi muku waka a nan Jihar Zamfara ku nawa kuka saura?
Sahabi Liman: To a sanina dai bayan ni, akwai Isan Mayana shi yana nan da ransa kuma Shata ya yi masa waka.
Aminiya: Wani hali ko dabi’a Shata ke da su, kuma idan mutane suka dauke su za su amfane su?
Sahabi Liman:  To, wannan hali bai wuce so da gaskiya ba, idan yana sonka ko kana da kudi ko babu zai yi maka waka. Kuma akwai rikon amana da gaskiya da sanin ya kamata a wurin Shata. Wadanda su ne suka yi karanci a tsakanin mutane a yanzu, ya kamata mutane su rike wannan. Daga karshe ina yi wa marigayi Dokta Mamman Shata addu’ar Allah Ya jikansa, Ya kuma gafarta masa, Ya saka masa da Aljannar Firdausi, amin.