✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da za mu sanya a gaba a Jihar Sakkwato –Shugaban IPAC

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Shugaban Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta Jihar Sakkwato Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo, ya bayyana jin dadinsa kan…

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Shugaban Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta Jihar Sakkwato Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo, ya bayyana jin dadinsa kan zabensa da aka yi a matsayin sabon shugaba gamayyar a jihar da abin da za su sanya gaba:

Aminiya: Bayan zabenka Shugaban Gamayyar Jam’iyyun Siyasa  (IPAC) a Jihar Sakkwato yaya za ka kwatanta ayyukan gamayyar?

Gamayar Jam’iyyun Siyasa da aka fi sani da IPAC reshen Jihar Sakkwato an samar da ita ce domin samun fahimtar juna a rika tafiya tare a duk abin da ya taso. Akwai ta a kasa baki daya da jihohi har zuwa mazabu. Wannan gamayya, mahada ce tsakanin ’ya’yan jam’iyun siyasa da hukumar zabe, kuma duk wani abu ya faru za mu hadu mu sasanta kanmu. Ba kungiya ce ta adawa ba, domin har jam’iyya mai mulki mamba ce, kowane shugaban jam’iyyar siyasa mamba ne a kungiyar, ba mu la’akari da wanda ya ci zabe ko ya fadi kowa na iya samun nasara domin tana zuwa ne daga Allah. Burinmu kawai a harkar shi ne samun fahimtar juna. Nasarar da na samu daga Allah ne da magoya bayana da muke tare da su da ’yan uwana shugabannin jam’iyyu a Jihar Sakkwato. Domin lokacin da na nuna sha’awar fitowa takarar neman in shugabance su  kowa ya ce ya janye min, haka aka zabe ni ba hamayya. Ina shirin kara karfafa dangatakarmu don ciyar da Jihar Sakkwato gaba.

Aminiya: Kafin zamanka Shugaban IPAC a Jihar Sakkwato, gamaryar ta dare gida biyu me za ka yi don dunkuke ta wuri daya?.

Abin da nake son ka sani da farko ba IPAC ce ta dare gida biyu ba, ita jagora ce kowace jam’iyya tana cin gashin kanta amma dai a kungiya muna nan tsintsiya madaurinki daya. Sai dai in wani abu ya taso bisa ga akasi za mu zauna mu fahimci juna, abin da ke kawo mana cikas bai fi son kai ba, wannan kuma an kawar da shi kuma a wannan jagoranci nawa daidai gwargwado zan kwatanta adalci.

Aminiya: Ana zargin mafi yawan shugabannin IPAC da zama ’yan amshin shatar gwamnati ko za a samu sauyi daga bangarenka?

To fahimtar mutane na da yawa, a gaskiya mu dai shugabanni mun san Allah zai tambaye mu. Don haka in mun ga an yi daidai za mu yaba, akasin haka ma za mu yi magana. A kullum shirye muke  in mun kuskure mu fadi domin ba za mu rungume hannu a cutar da jiha ba domin mu aka cutar. Duk inda muka ga haka za mu bada shawara domin a gyara. Duk da Gwamna mai ci yanzu koyaushe yakan ce in mun ga wani abu na kuskure mu fadakar da shi don a gyara. Misali kamar korar ma’aikata don bambancin siyasa ya ce shi bai gamsu da yin haka ba duk in da muka samu labari za mu sanar da shi, yana fadin shi shugaba ne na kowa, hakkin duk wani dan Jihar Sakkwato na kansa. IPAC ba ta yarda da duk wani abu da zai cutar da jiharmu da kasa ba, in mun gani za mu yi magana don a gyara.

Aminiya: Akwai matsaloli a Jihar Sakkwato da suka shafi harkar ilimi da kiwon lafiya da sauran bangarorin rayuwa ko kuna fadakar da gwamnati?

Gaskiya a kudirin da Mai girma Gwamna ya fito da shi mun ga alama akwai niyya ta alheri ga Jihar Sakkwato. Mun sa ido mu gani zuwa wani lokaci in an yi za mu yaba in ba a yi ba za mun tunatar da shi don mu Sakkwato muke da ra’ayi ba kowa ba.

Aminiya: A matsayinka na dan siyasa mai adawa kana ganin karin kudin wutar lantarki ya dace?

Karin kudin ya dace in zai yi tasiri kuma ya biya bukatun jama’a. Ko kyauta za a ba ka wutar lantarki in babu ba ta da amfani. Kamar yadda ake tsammani za a kara kudin wutar domin samar da kudin da za su isa wutar ta zo wurinmu ban ga laifi ba tunda wutar ta koma ta kasuwa a yanzu. Amma dai shugabanni su rika sanya talaka da kasa a gaban komai cikin mulkinsu. In wutar lantarki za ta wadatu a Najeriya ina goyon bayan karin kudin da gwamnati ta kudiri aiwatarwa.