Da Dumi Dumi

Abin da zai magance matsalolin Najeriya – Sheikh Muhammad Sulaiman

Sheikh Muhammad Sulaiman, Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna
Sheikh Muhammad Sulaiman, Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna

Sheikh Muhammad Sulaiman Abu Salaiman, shi ne Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna. A tattaunawa da  wakilinmu kan matsalolin da ake fuskanta a kasar nan, ya ce hanyoyin magance matsalolin kasar nan, su ne komawa ga Allah da kaurace wa aikata ba daidai ba da sauransu:

Aminiya: Wadanne hanyoyi ne kake ganin za a bi a magance matsalolin kasar nan, na kashe-kashe da garkuwa da mutane?

Sheikh Sulaiman: Allah Madaukakin Sarki Ya riga Ya gaya mana yadda za mu warware kowace matsala, idan ta taso. Kuma malamai suna iyakar kokarinsu wajen gaya wa mutane yadda za su yi ayyukan alheri. Domin dole ne a gaya wa mutane yadda za su yi ayyukan alheri, kuma a gaya musu ayyukan sharri da ya kamata su guje musu.

Babu shakka aikin malamai shi ne su fada wa mutane wadannan abubuwa, kuma aikin hukuma ce ta hana abin da ya kamata ta hana, kuma aikinta ne ta sa mutane,  su yi abin da ya kamata su yi.

Ya kamata malamai su nuna wa al’umma cewa a koma ga Allah, a roke Shi gafara. Domin duk wata azaba da masifa da ake yi, idan ana rokon gafarar Allah Ubangiji, ba zai yi wa mutane azaba ba.

ADVERTISEMENT

Domin  Allah Yana  yin bushara cewa Allah ba zai yi musu azaba ba, matukar suna rokon gafarar Allah. Don haka wadannan masifu da suke bullowa ta ko’ina a Najeriya, irin su talauci da kashe-kashe da garkuwa da mutane da cin amana, duk hanyoyin magance su shi ne komawa ga Allah. Idan al’ummar Najeriya  suka yarda sun yi laifi, suka koma ga Allah ba zai yi musu azaba ba.

Abu na gaba shi ne mu nemi ilimin sanin Lahira. Idan mutum ya yi ilimin sanin hakikanin Lahira, ya san cewa Allah Madaukakin Sarki ba Ya barin ko-ta-kwana, ya san cewa duk abin da ya yi Allah zai saka masa da wannan abin, ba zai aikata mummunan aiki ba.

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa wanda ya aikata mummunan abu, za a yi masa sakayya da mummuna. Kuma idan mutum ya samu ilimin cewa a Ranar Lahira, Allah zai fito masa da duk abin da ya yi a rayuwarsa, dole ne zai ji tsoron Allah. Duk abin da mutum ya yi a rayuwarsa, yana nan rubuce a wajen Allah Madaukakin Sarki.

Don haka idan mutum ya yi ilimin addini ya san cewa akwai wannan abin yana nan yana jiransa, maganar ya yi barna ba ta taso ba.

Misali idan da yaranmu masu shirya fina-finan Hausa za su koma ga shirya fina-finai kan abubuwan da suka shafi rikon amana da gaskiya da tausayawa, da sun rika samun lada a wajen Ubangiji.

Amma idan suka je suna shirya fina-finan yadda ake yin kwartanci da yadda ake yin sata da yadda ake yin fyade, babu maganar samun lada a wajen Ubangiji.

Idan muka koma ga Allah ko gwamnati ta kafa doka, babu ruwanta da sai ta sanya ’yan sanda su tilasta mutane, saboda suna tsoron Allah. Domin idan mutum yana tsoron Allah, komai aka sanya shi zai yi. Amma idan mutum ba ya tsoron Allah, komai ka sanya shi ba zai yi ba. Don haka wannan ita ce mafita, ga matsalolin da suke damun kasar nan.

Aminiya: Wato a ganinka kauce wa koyarwar addini  ya kawo matsalolin da muke fuskanta a kasar nan?

Sheikh Sulaiman: Wannan haka yake domin Allah Yana cewa ba Ya canja abin da ke ga mutane, har sai su mutanen sun canja abin da ke tare da su.

Da a Najeriya muna cikin ni’ima, arziki ya zo mana ta ko’ina, lokacin ba mu san fadan kabilanci ba, ba mu san tare hanya a yi fashi ba, ba mu san satar mutane ba, ba mu san fadan addini ba. Dukkan wadannan abubuwa da suke faruwa yanzu saboda mun bar Allah ne. Domin ni’imar da Allah Ya ba mu mun watsar da ita, saboda haka Allah Yake dandana mana azaba. Ko za mu yarda mu koma kan hanya.

A yau idan muka dawo muka koma ga Allah zai cire mana dukkan matsalolin da muke ciki a kasar nan. Abubuwan su zama tarihi a rika cewa da a Najeriya ana kashe mutane da satar mutane.

Kamar ni din nan ina dan shekara 6 aka dauke ni aka kai tashar jirgin kasa ta Jos aka hada ni da wata Ibo ta dauke ni, ta sanya ni a cinya ta kai ni Fatakwal, ta sani a mota ta kai ni har gidan da ake so a kai ni. Saboda lokacin ana zaune lafiya. Don haka idan Najeriya ta dawo aiki nagari za a warware matsalolin da suke damunmu.

Aminiya: Wace gudunmawa kake ganin malaman addini za su iya bayarwa, wajen warware matsalolin da suke damun kasar nan?

Sheikh Sulaiman: Kamar yadda na fada tun farko, babbar gudunmawar da malamai za su bayar wajen warware matsalolin kasar nan, ita ce su koma ga karantar da mutane kyawawan ayyuka. Domin idan dukkan malamai za su koma ga karantar da mutane kyawawan ayyuka, za a warware matsalolin da suke damunmu. Idan shugabanni da talakawa suna tsoron Allah, idan aka kafa doka ba za a karya ba.

Aminiya: To, wane kira  kake da shi ga gwamnati da al’umma baki daya?

Sheikh Sulaiman: Sau da dama ana cewa gwamnatin Najeriya, gwamnati ce da babu ruwanta da addini. Amma gaskiya abin ba haka ba ne, domin  babu wani shugaba da za a rantsar  a Najeriya, ba tare da ya rantse da littafin addinin da yake bi ba. Idan Musulmi ne sai an rataya masa Alkur’ani, idan Kirista ne sai an ba shi littafin Baibul,  ashe ka ga Najeriya tana da addini ke nan.

Saboda haka ya kamata kowace gwamnati a Najeriya ta rungumi masu addini hannu bibbiyu, domin su ne za su kawo gyara kan abubuwan da suka lalace a Najeriya. Kuma gwamnati ta kafa Ma’aikatar Harkokin Addini, ta tsara yadda shugabannin addini za su gudanar da ayyukansu.

Gwamnati a dukkan matakai su rungumi addini domin su samu saukin gudanar da abubuwansu. Wannan  ne zai kawo mana zaman lafiya, da kwanciyar hankali  a Najeriya.

Kuma ina kira ga al’umma kamar yadda na yi tunda farko cewa su nemi ilimi, domin ilimi ne zai warware komai. Su kuma ’yan siyasa masu rike da mukamai su tuna lokaci yana kurewa, idan an zabi dan siyasa a karo na farko, aka sake zabensa a karo na biyu, lokacin zai kare. Don haka kowane dan siyasa ya yi kokari, ya yi abubuwan da ya yi alkawari, domin duk alkawarin da mutum ya yi, Allah zai tambaye shi a ranar tashin Alkiyama.

Share