✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da zan yi bayan shekara 10 a Gwamna da 12 a Sanata – Bukar Abba

Sanata Bukar Abba Ibrahim wanda ake yi wa lakabi da Uban siyasar Yobe, shi ne Sanatan Yobe ta Gabas  a Majalisar Dattawa kuma yi yi…

Sanata Bukar Abba Ibrahim wanda ake yi wa lakabi da Uban siyasar Yobe, shi ne Sanatan Yobe ta Gabas  a Majalisar Dattawa kuma yi yi Gwamnan Jihar Yobe na shekara 10, sai Sanata na shekara 12. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa yanzu zai yi ritaya daga siyasa, da kuma tsare-tsaren rayuwarsa a gaba:

Aminiya: Ka yi Gwamnan Jihar Yobe na tsawon shekara 10, me kake tunanin ake bukata wajen zama Gwamna?

Sanata Bukar: Ba wai wata takamaiman takardu ne a ake lura da su wajen zama Gwamna ba. Abin lura kawai shi ne irin halin da mutanen jihar suke ciki da kuma yanayin siyasar domin dole a samu shugaba. Sannan duk wanda mutane suka zaba, dole ya zama Gwamna. Haka idan lokacin barinsa ya zo, sai shi ma ya tafi wani ya karba. Haka abin yake zagayawa.

Aminiya: Yaya kake ganin za a gyara siyasar kasar nan ta yadda ’yan siyasa za su daina daukar abin kamar yaki?

Sanata Bukar: Ana samun ci gaba a yadda ake tafiyar da al’amura a kullum. A lokacin da aka kirkiri Jihar Yobe, irin siyasar da muka yi ta bambanta da irin wadda ake yi yanzu, domin ’yan siyasar sun canja kuma tsarin ma ya canja kuma ana samun sauye-sauyi da ci gaba a wasu bangarori a harkar wasu kuma suna lalacewa.

Aminiya: Ana cewa wai Majalisar Dattawa zaure ne da tsofaffin gwamnoni suke zuwa domin su huta. Me za ka ce game da wannan batu?

Sanata Bukar: Ya danganci irin aikin mutum. Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai aikinsu shi ne su yi doka. Su ne suke yi wa gwamnati doka, su duba tare da gyara dokokin kasar. Ba zai yiwu a tafiyar da kasa ba tare da doka ba. Don haka ba na ganin Majalisar Dattawa a matsayin wajen hutu. Kullum aikin Majalisar Dattawa shi ne ta yi doka domin kasa ta gyaru kuma a samu gwamnati mai inganci.

Idan Sanata yana so ya huta kamar yadda nake so in huta yanzu, sai ya yi ritaya. Da kaina na hakura na bar wa Gwamna Geidam kujerar Sanatan Yobe ta Gabas lokacin da ya nuna yana sha’awa. Sau uku na yi Sanata, wato shekara 12 ke nan. Hakan ya sa na bar wa kanena domin ya ci gaba, da shi da sauran wadanda suka lashe zabe.

Aminiya: Ganin cewa ka yi Gwamna na shekara 10, Sanata na shekara 12, wanne daga cikinsu kake ganin ya fi wahala?

Sanata Bukar: Dukansu akwai wahala lokacin da nake rike da su. Na yi Gwamna na shekara 10, sannan na sauka lokacin da wa’adina ya kare. Sannan na tafi Sanata. Don haka babu bukatar kwatanta yanayin aikin biyu domin kowannensu aikinsa daban kuma tsarin gudanar da su daban. A dukansu na yi iya kokarina, kuma ina godiya ga Allah bisa yadda na gama lafiya kuma ina murnar nasarorin da na samu. Sai kuma wadansu su ci gaba daga inda na tsaya.

Aminiya: Lura da yadda ka dade a siyasa, sai mutum ya rika tunanin ko me za ka yi bayan ka bar ta?

Sanata Bukar: Da farko dai zan dan huta ne, sannan sai in ci gaba da ba ’yan siyasa shawara a kan abin da ya kamata a duk matakan gwamnati tun daga Shugaban Kasa zuwa Kansila. Sannan ina da gona da zan ci gaba da nomawa a Damaturu. Ina da kusan itatuwa miliyan daya na karo. Ina da shanu da raguna da sauransu, sannan zan rika noma hatsi. Don haka zan koma gona domin amfanin iyalina da ni kaina da jihar da ma kasa baki daya. Don haka akwai abubuwan da zan ci gaba da yi.

Aminiya: Wace shawara za ka ba sababbin ’yan siyasa?

Sanata Bukar: Lallai akwai shawarwari da yawa da ya kamata a ba su. Dole su sanya Najeriya a gaba da komai. Su sanya jiharsu da kuma matsayin da suke nema a zabe su. Idan kuma suka samu dama, sai su dage su yi iya kokarinsu tsakaninsu da Allah, sai su bar wa Allah sauran.

Aminiya: Yanke shawara barin siyasa ba karamin abu ba ne, amma yaya ka ji lokacin da yanke wannan shawara?

Sanata Bukar: Ba na tunanin yanke shawarar shiga ko barin siyasa na da wahala. Komai na rayuwa yana da farko kuma yana da karshe. Kawai dai ya danganci yanayin da mutum ya tsinci kansa ne. Ban taba tsammanin zan shiga siyasa ba. Na bar aikin gwamnati ne a matsayin babban mai tsara kasa da safiyo da nufin in bude kamfanina in ci gaba da aikin da na kware a kai. Kawai sai aka nemi in zo in bayar da tawa gudunmawar a siyasa. A lokacin muna Jihar Borno ne domin ba a kirkiri Jihar Yobe ba. Tun wancan lokacin nake siyasa. Don haka babu wani abu mai sauki a rayuwa, amma kuma babu yanke shawarar da za a ce wai ta yi girma ko wahala.

Aminiya: Wane abu ne a siyasa da za a iya cewa ya fi burge ka

Sanata Bukar: Babu kamar a ce ka dauki alkawarin yin wasu abubuwa, kuma Allah Ya taimake ka ka cika wadannan alkawura, sannan mutane su nuna murnarsu. Wannan shi ne abin da na fi jin dadi a siyasa. Kuma na samu irin wannan nasarorin a lokuta da dama.

Ban taba shiga wani takaici ko da na sani ba a rayuwata ta siyasa ba, amma na fuskanci kalubale da yawa. Amma kuma duk lokacin da na fusakanci kalubalen, nakan yi kokarina wajen magance su ne.