Da Dumi Dumi

Abin da zan yi da kudin fanshon tsofaffin gwamnoni da aka soke – Matawalle

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle ya ce zai yi amfani da fanshon tsofaffin gwamnonin jihar da aka soke wajen raya karkara.

Wata sanarwa da Kakakin Gwamnatin Jihar ya fitar, ta ce, Gwamna Matawalle ya ji takaicin yadda tsohon Gwamnan Jihar yake neman a biya shi makudan kudi a daidai lokacin da sauran ’yan fansho a jihar ke cikin kangin wahala saboda rashin biyansu kudadensu, kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito.

Ya ce ’yan fansho na bin gwamnatin da ta shude bashin fansho da ya kai Naira biliyan 10.

A farkon makon nan ne wasika da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya rubuta yana neman Gwamnan Jihar Zamfara ya biya shi basussukan kudin fansho da yake binta inda ya ce ya kamata a rika biyansa Naira miliyan 10 duk wata kamar yadda doka ta tanada.

Bayan kwana biyu da bayyanar wasikar ce,  Majalisar Dokokin Jihar ta soke dokar da ta tanadi biyan tsofaffin gwamnonin da mataimakansu fansho har tsawon rayuwarsu.

ADVERTISEMENT

Alhaji Faruk Musa Dosara na Mazabar  Maradun 1 ne ya gabatar da kudirin soke dokar, inda ya bukaci  ’yan majalisa su soke dokar biyan tsofaffin gwamnonin da mataimakansu makudan kudi, inda a cewarsa ana biyansu sama da Naira miliyan 700 duk shekara. Ya ce kamata ya yi a mayar da hankali kan sauran ma’aikata da ba a biya su hakkokinsu ba na wasu shekaru da suka gabata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya