✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin misali daga rayuwar Sa’adu bin Abu Wakkas (4)

Sa’adu a zamanin Abubakar (RA): Bayan jarumta Sa’adu ya nakalci dabarun shugabanci, domin haka ne Halifa na farko Sayyidina Abubakar Siddik (RA) ya zabe shi…

Sa’adu a zamanin Abubakar (RA):

Bayan jarumta Sa’adu ya nakalci dabarun shugabanci, domin haka ne Halifa na farko Sayyidina Abubakar Siddik (RA) ya zabe shi ya kasance mai mulkin (Gwamnan) Hawazin. A wancan lokaci mutanen Hawazin ba su dade da shiga addinin Musulunci ba.

Kafin wannan lokaci, mutanen Hawazin sun taimaka wa mutane da’ifa wajen yakar Musulunci a yake-yaken Hunaini da da’ifa. Sayyidina Abubakar (RA) ya zabi Sa’adu ne ya jagoranci yakin Hawazin domin ganin cewa yaki ne mai barazana da wahala, yana bukatar jarumi kuma wanda ya nakalci  shugabancin jama’a. Kuma dukan wadannan halaye ne na Sa’adu (RA). Haka Sa’adu (RA) ya yi ta taimakon Sayyidina Abubakar (RA) a harkokin shugabanci da yaki har zuwa karshen rayuwar Halifa Abubakar Siddik (Allah Ya kara masa yarda).

Sa’adu a zamanin Umar (RA):

kokari da hazakar da Sa’adu (RA) ya nuna a zamanin halifancin Sayyidina Umar bin Khaddabi (RA) suna da yawa da kuma tarin muhimmanci. A farkon zamanin Halifancin Umar (RA), Musulmi sun fara karfi a Daular Rumawa, amma a wancan lokaci Daular Farisa tana dada zama barazana ga Musulmi. Don haka Musulmi suka ga cewa babu mafita illa su yi shiri domin yakar wannan daula da kawo karshen shisshigin da take yi ga Musulmi da Musulunci.

Umar bin Khaddabi (RA) ya so ya jagoranci wannan muhimmin yaki da kansa, amma aka hana shi. Ya aika zuwa dukan kasashen Musulmi yana neman gudunmawar mutane da kayan yaki. Nan da nan mayaka da kayan yakinsu suka taru a Madina. Da aka hana Sayyidina Umar (RA) fita domin jagorantar wannan yaki, sai aka yi tunanin wane ne fitaccen jarumi wanda zai iya (jagorantar) wannan aiki mai girma. Hikimar wannan tsari shi ne idan aka bar Umar (RA) a Madina zai ci gaba da samar da mayaka da kayan yaki yana turawa ga jagoran filin yaki. Idan ma an kashe jagoran ne a filin ga (Shugaba) Umar (RA) yana nan zai aiko da wanda zai maye gurbinsa.

Bayan Umar (RA) ya karbi wannan shawara sai ya fara tunanin wanda zai iya wannan aiki. Wata rana Umar (RA) yana karanta wasikar da Sa’adu bin Abu Wakkas (RA) ya aiko masa cikin sahabbansa game da mayaka da kayan yaki da ya aiko daga lardinsa na Hawazin, sai kawai sahabban da suke wurin suka bayyana amincewarsu da sunan Sa’ad a lokacin da aka ambace shi. Domin Umar (RA) yana cikin karanta wasika daga Sa’adu (RA) sai ya ji mutane suna cewa, ‘mun samu shugaba na wajen yaki.’ Sai Umar (RA) ya tambaye su wane ne wannan shugaban da na ji kuna cewa an samu shugaba? Sai suka ce ai Sa’adu bin Abu Wakkas muke nufi.

Daga nan Umar (RA) ya amince, wannan ita ce hanyar da aka zabi Sa’adu (RA) a matsayin wanda zai jagoranci yaki a kan shaidar da sahabbai suka bayar a kansa. Umar (RA) ya aika aka kirawo shi ya dawo Madina, kuma ya umarce shi da jagorancin rundunar Musulunci zuwa Iraki da Iran, daga nan Sa’adu (RA) ya shirya aka fita.

Umar (RA) ya ba shi shawarwari kafin ya fita kamar haka: “Ya kai Sa’adu! Kada ka nuna kai wani ne, saboda kana matsayin kawu ga Manzon Allah (SAW), domin Allah babu ruwansa da ’yan uwantakarka, kuma babu abin da zai taimaka wa mutum face kyawawan ayyukansa. Mutane daidai (bai-daya) suke a wurin Allah babu bambancin matsayi. Ayyukan bayi ne kawai suke bambanta su a gaban Allah. Domin haka ka rika rubutowa kana aiko mini halin da Musulmi ke ciki a filin yaki, haka ma halin da suke ciki da kuma matsayin abokan gaba.” 

Sannan ya umarce shi ya nada mataimaki daga cikin fitattun jaruman da suke tare da shi.

Sa’adu (RA) ya ci gaba da tuntubar Umar (RA) ta hanyar wasiku domin sanar da shi halin da Musulmi suke ciki a filin yaki. Shi kuma Umar (RA) yana shawara da sahabban da suke tare da shi a Madina domin ci gaban aikin da aka sa a gaba na neman nasarar wannan yaki da ake yi, ana aika wa Sa’adu da sauran mayaka a can filin yaki, saboda yaki dan dabara ne.

Wasikar Musannah zuwa ga Sa’adu:

Musannah bin Harisa (RA) shi ne yake jagorantar rundunar Musulmi kafin Sa’adu (RA), kuma mutum ne wanda ya yi fice a wannan fage. Lokacin da ya kwanta rashin lafiya, kuma ya yi tsammanin ciwon ajali ne sai ya rubuta wasika zuwa ga Sa’adu yana ba shi shawara kan yadda zai samu nasarar yaki.

Kuma ya shawarce shi cewa idan ya rasu, yana so Sa’adu (RA) ya auri matarsa Salmah, saboda tana da kwarewa wajen dabaru da hikimar samun nasara a filin yaki.

Bayan Al-Musannah ya rasu, Sa’adu (RA) ya yi amfani da shawarwarinsa, kuma ya sa dan uwansa a matsayin mataimakinsa.

Yakin kadisiyyah:

Wannan shi ne yaki na farko da Sa’adu (RA) ya jagoranta (lokacin da ya fuskanci Daular Farisa) kuma ya kasance mai tsananin gaske. Ya yi nade-nade masu dama domin ganin an cimma nasara. Ya nada Salmanul Farisi (RA) ya zama Kakakin Ayarin Musulmi, sai Zaidu bin Sabit (RA) ya zama marubucin (Sakataren) Rundunar Musulmi, sannan ya zabi wadansu sahabbai su kasance shugabanni a rundunonin yaki daban-daban.

Sa’adu (RA) yakan kebance lokaci domin zaburar da kwamandojinsa don samun gasa a tsakaninsu, saboda cin nasarar Musulmi. Kuma yakan karfafa su da cewa ana samun nasara ce idan aka ji tsoron Allah kuma aka yi hakuri. Kuma yakan ce Musulunci da Musulmi su ne gaskiya don haka nasara tana gare su daga Allah, har abada ba za a yi ranjaye a kansu ba. Kullum yakan ba da umarni a yawaita karatun Alkur’ani, wanda hakan ke sa ka su cikin nishadin ibada da karfafa musu gwiwa ga ci gaba da yaki da neman shahada. Ana cikin haka ne har Sa’adu (RA) ya aike da wani dan sako a kan ya kira Sarkin Farisa Rustum da jama’arsa cewa su shigo addinin Musulunci. Ya ce a bayyana wa Rustum cewa idan ya karbi Musulunci zai samu duk alfarmar da Musulmi ke da ita babu bambanci. Kuma wanda aka aike zuwa ga Sarki Rustum, shi ne Rabi’ah bin Amir (RA).

Da jagoran ’yan aiken da ’yan rakiyarsa suka isa sun jawo hankalin Sarki Rustum  da cewa Musulunci ya zo ne domin ceto mutane daga hallaka da azabar wuta zuwa ga shiriya da hasken hakika (imani). Kuma yana kira  ga barin bautar gumaka zuwa ga bautar Allah Shi kadai. Rabi’a ya kara da cewa “Sarki Rustum, wannan sako ne gare ka da mu baki daya. Idan ka amsa kira to za mu koma inda muka fito ba tare da mun taba kowa ba, kuma kasarka za ta ci gaba da zama a karkashinka. Kuma za mu ci gaba da taimaka maka wajen ba ka kariya daga wadansu da za su iya kawo maka hari daga wani wuri. Idan kuma ba za ka karbi wannan sako ba, to kana iya biyan jiziya don kariyar da Musulmi za su ba ka. Idan kuma duk wadannan ba su karbu a wurinka ba, to babu komai a tsakaninmu da kai sai yaki.” Sai Rustum ya tambaye su, to shin su me zai kasance moriyarsu idan har suka yi yaki? Rabi’a ya ce, “Idan muka yi shahada (aka kashe mu) akwai gidan Aljanna. Idan kuwa muka yi nasara, to akwai farin ciki da zai tabbata ga wanda ya rayu cikin nasara.”

Duk da wannan bayani Sarkin Rustum na Farisa ya yi watsi da sakon da aka aike masa, domin yana ganin girman rundunarsa da ke kunshe da kimanin mayaka dubu 100. Haka dai ’yan aike suka dawo ba a samu nasara a tattaunawarsu da Sarki Rustum na Farisa ba. 

Za a iya samun Ustaz Aliyu Gamawa ta tarho: 08023893141, 08035829071