Da Dumi Dumi

Abokin gwamnan Bauchi ya kamu da Coronavirus

Mutumin ya kamu ne sakamakon mu'amalar da ya yi da Gwamna Bala Muhammad

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa wani abokin Gwamnan Bala Muhammed mai shekara 62 ya kamu da cutar Coronavirus.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Aliyu Muhammed Maigoro ne ya bayyana haka yana  cewa mutum na biyu da aka tabbatar yana dauke da cutar a jihar “Abokin wanda ya kamu da cutar na farko ne, amma an  kawo yanzu”.

Kwamishinan ya tabbatar da hakan ne yayin wani taron manema labarai da a Ma’aikatar Lafiya ta jihar.

Ya ce daga cikin mutum 48 din da suka kai jininsu Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) daga jihar an tabbatar mutum biyu ne ke dauke da cutar.

Dokta Maigoro ya kuma ce, yanzu haka za su dauki samfurin jinin dukkanin mutanen da mutum biyun suka yi mu’amala da su domin su ma a gwada su a gani ko suna dauke da cutar.

ADVERTISEMENT

Ranar Talata 24 ga watan Maris ne dai aka tabbatar da cewa Gwamna Bala Muhammed yana dauke da cutar ta Coronavirus wadda ake kyautata zaton ya kamu da ita bayan ya yi mu’amala da dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Gwamnan ya yi mu’amala da mutane da dama, ciki har da manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya na jihar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya