✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 4 da za a fi tuna Abba Kyari da su

A shekaru kusan shida da ya yi a matsayin Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari ya yi tasiri matuka a kan yadda…

A shekaru kusan shida da ya yi a matsayin Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari ya yi tasiri matuka a kan yadda al’amura ke gudana.

Shi ya sa ma ake ganin cewa mutuwarsa ta haifar da wani wawakeken gibi a harkar mulki a Najeriya a yau.

Ga hudu daga cikin abubuwan da ba za a manta ba game da Malam Abba Kyari:

  • A cikin mutanen da ke rike da manyan mukamai a Gwamnatin Buhari, babu wanda ya kai shi kusanci da shugaban kasar. A farkon fara zango na biyu na mulkinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya fada wa ministocinsa cewa duk wanda yake son ganinsa ya biyo ta hannun Malam Abba Kyari.
  • Ba kasafai akan ji muryarsa a bainar jama’a ba. An yi zarge-zarge, an yi suka a kan shi, amma marigayin bai ce uffan ba.
  • Kwana kadan kafin ba da sanarwar gwaji ya nuna cewa ya kamu da coronavirus, an kwarmata wata takarda da aka ce Malam Abba Kyari ya rubuta yana jan kunnen ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa, wadanda aka ce sun dawo daga waje kuma sun ki su ba da kansu a yi musu gwajin.
  • Shi ne mai rike da mukamin gwamnati na can koli (na kusa da shugaban kasa) na farko da ya rasu sakamakon kamuwa da COVID-19. Zuwa yanzu ba a samu wani mai rike da mukami na can sama ba da ya rasu sakamakon kamuwa da coronavirus.

Da daren Juma’a ne dai Malam Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya bayan ya yi makwanni yana jinya.

An yi amanna ya kamu da coronavirus ne, cutar da ta yi sanadin mutuwarsa, yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jamus a watan jiya.