✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa bakwai da ba ku sani ba game da ayyukan NCDC

Tun bayan barkewar annobar coronavirus, ’yan Najeriya da dama sun yi korafi a kan yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC take gudanar…

Tun bayan barkewar annobar coronavirus, ’yan Najeriya da dama sun yi korafi a kan yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC take gudanar da aikinta.

Shin takamaimai wanne alhaki ne ya rataya a wuyan hukumar a yakin da ake yi da yaduwar annobar?

Ga abubuwa bakwai da ya kamata ku sani game da rawar da NCDC ke takawa a yakin.

1. NCDC ba ta ginawa ko tafiyar da dakunan gwaje-gwaje.

In ban da babban dakin gwaji na Babban Birnin Tarayya Abuja, sauran dakunan gwajin ko dai mallakin jihohi ne ko kuma na hadin gwiwa ne tsakaninsu da gwamnatin tarayya ko kuma na masu zaman kansu.

2. Aikin NCDC shi ne tantancewa da kuma bayar da duk wani taimako da wadannan dakunan gwaje-gwajen ke bukata don gudanar da ayyukansu.

Amma asalin gwajin ba NCDC ce take da alhakin gudanarwa ba.

3. Ba NCDC ce ke da alhakin tattarawa tare da jigilar mutanen da aka yi wa gwajin kuma aka tabbatar suna da cutar zuwa cibiyoyin killace su ba.

4. Bugu da kari hukumar ba ta ginawa ko gudanar da cibiyyoyin killace mutane ko wurin shan maganin su.

Alhakin dukkan wadannan ya rataya ne a kan gwamnatocin jihohi.

5. Ba NCDC ba ce ke da alhakin sanarwa da mutane sakamakon gwajinsu.

Galibi idan sakamakon gwajin ya fito daga dakunan gwaje-gwajen, NCDC ta kan mika shi ne ga cibiyoyin bincike mallakin jihohi; ko dai ma’aikatar lafiya ta wannan jihar ko kuma wadannan cibiyoyin binciken ne ke da alhakin sanar da mutane sakamakonsu.

6. Babban aikin NCDC shi ne tattara alkaluman sakamakon gwaje-gwaje daga dakunan gwajin sannan ta tattara su a matakin jiha-jiha, ta kuma tattara na dukkan jihohin kafin daga bisani ta sanar da jimillar na duk kasa a hukumance.

7. Idan NCDC ba ta samu damar karbar sakamakon alkaluma daga wata jihar ba kafin lokacin da take tattarawa tare da sanar da su da yamma, ta kan kyale wannan jihar sai zuwa kashegari sai ta hada gaba daya ta sanar.