Da Dumi Dumi

Abubuwa uku da ke hallakar da matasa

Daga Sanusi Hashim
Daga Sanusi Hashim

Wassalatu Wassalamu Alan Nabiyyu (SAW)

1-Shaye-Shaye,

2-Kallace-Kallace,

3-Zaman kashe wando

A yau cikin ikon Allah darasin namu zai tabo wasu daga cikin manyan sabubba da ke da nasaba da fadawar da yawa daga cikin matasanmu wani mawuyacin hali.  Idan na ce matasa ina nufin mace da namiji.

ADVERTISEMENT

Illa ta farko kuma wadda ita ce jagorar duk wata illa ita ce;

1-Zaman kashe wando; kila ku yarda da ni idan na ce “rashin aikin yi na iya sanya matashi ko matashiya yin shaye-shaye, shaye-shayen kuma su ne tsanin da za ka taka ya kai ka ga duk wani mummunan aiki.”

Yau a kasarmu mafi yawan matasanmu ba sa yin aikin komai sai zaman kashe wando, inda ta kai wadansu daga cikin ’yan siyasarmu suke amfani da su don su zame musu ’yan bangar siyasa.

Ba lallai ba ne sai gwamnati ta samar wa daukacin al’ummarta aikin yi ba, amma a ce akalla mafi yawa suna da hanyar samun kudin shiga, kama daga Gwamnatin Tarayya zuwa ta jiha zuwa kananan hukumomi. Kamar yadda wasu matakan da na ambata a sama musamman gwamnatin jiha da su samu hanyoyi da za su bunkasa rayuwar matasa, ta hanyar koya musu sana’o’i da ba su jari, in sun kammala samun horo. Kamar yadda na sani wasu daga cikin jihohinmu suna yi.

Tabbas wasu gwamnatoci duk wata suna raba basussuka ga matasa, haka an samu wasu da suka bude wata masana’anta suna koyar da ’yan uwa matasa, sai dai inda gizo ke sakar, a gaskiyar magana da yawa daga cikin irin wadannan tsare-tsare ba sa zuwa ga wadanda suka cancanta, sai ka ga an sanya siyasa a ciki da sauransu.

A nan zan yi kira ga gwamnati ta dduki dukkan al’ummarta a matsayin uwa daya uba daya, domin in kana takamar ka gyara yaranka na wani kuma ko oho, to karshe in wadancan suka lalace sai su shafi naka yaran.

A takaice zan dakata a kan abin da ya shafi illar rashin aikin yi, kuma kamar yadda na yi kira ba sai gwamnati ba, masu kudinmu da ’yan kasuwarmu sai sun taimaka don bai yiwuwa a zura wa gwamnati ido duk da ita ce mai babban hakki.

Mu kwana nan

Sanusi Hashim Abban Sultana

Daga Jihar Katsina

08065507271