Sakamakon irin nau’o’in man shafawa na zamani da mata da dama ba su san da me ake hada su ba, su dai daga ganin ya yi kyau sai a ce zai yi wa fata kyau. Yawan shafa irin wadannan man na haifar da kuraje da ba su saurin barin fuska. Koda kuwa sun bar fuska sai a ga tabo na nan ba ya bata. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwan kwalliya shida wadanda ko a gida za a iya hada su domin samun fata mai laushi kuma marar kuraje.
•Man zaitun; yana dauke da sinadarin rage maiko a fuska. Don haka yana da kyau idan za a sake yin kwalliya a samu auduga a tsoma a man zaitun a rika goge fuska da ita kafin a sake maka wata kwalliyar. Yin haka na hana fesowar kuraje a fuska.
•Kwakwa; sai a ga mace fara kyakyawa kamar a wanke hannu kafin a taba amma daga an taba hannunta sai a ji shi kamar tana faskare ko surfe tsabagen tauri. Idan ana da irin wannan matsalar, sai a samu kwakwa a kankare bayanta a markada da ruwa kadan a tace sannan a sanya a firiji. Idan ta yi sanyi sosai sai a rika shafawa a tafin hannu yana sanya fatar hannu laushi.
•Zuma da sukari; idan mutum na fama da fata mai yawan saba musamman ma fatar fuska, sai a hada zuma da sukari a wuri guda sai ya shafa a fuska na tsawon minti talatin kafin a murza a fuska. Yin hakan na cire fatar da ta mace a fuska domin bai wa sabuwar fata waje. Idan an gama sai a wanke da ruwan dumi.
•Madara/kindirmo; tana sanya fatar fuska laushi da sulbi. A samu madarar kindirmo sannan a shafa a fuska na tsawon minti talatin a kullum kafin a kwanta barci . yin hakan na kashe kowace irin kwayar cutar da take fesowa a fuska ko kuma a fata.
•Kwai; a samu ruwan kwai a cire gwaiduwar a rika bugawa har sai ya yi kumfa. A shafa a gashin kai na tsawon awa daya ko rabin awa sannan a wanke da man wanke gashi. Yin hakan na cire dattin da ke cikin gashi da kuma hana gashi karyewa.
•Fiya; shi ma yana gyara gashi sosai. A kwaba shi ya yi laushi sannan a shafa a fatar kai domin hana fitowar amosanin ka. A bari a fatar kai na tsawon minti talatin kafin a wanke da ruwan dumi.