✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da fata ke bukata

Sakamakon irin nau’o’in man shafawa na zamani da mata da dama ba su san da me ake hada su ba, su dai daga ganin ya…

Sakamakon irin nau’o’in man shafawa na zamani da mata da dama ba su san da me ake hada su ba, su dai daga ganin ya yi kyau sai a ce zai yi wa fata kyau. Yawan shafa irin wadannan man na haifar da kuraje da ba su saurin barin fuska. Koda kuwa sun bar fuska sai a ga tabo na nan ba ya bata. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwan kwalliya shida wadanda ko a gida za a iya hada su domin samun fata mai laushi kuma marar kuraje.

•Man zaitun; yana dauke da sinadarin rage maiko a fuska. Don haka yana da kyau idan za a sake yin kwalliya a samu auduga a tsoma a man zaitun a rika goge fuska da ita kafin a sake maka wata kwalliyar. Yin haka na hana fesowar kuraje a fuska.

•Kwakwa; sai a ga mace fara kyakyawa kamar a wanke hannu kafin a taba amma daga an taba hannunta sai a ji shi kamar tana faskare ko surfe tsabagen tauri. Idan ana da irin wannan matsalar, sai a samu kwakwa a kankare bayanta  a markada da ruwa kadan a tace sannan a sanya a firiji. Idan ta yi sanyi sosai sai a rika shafawa a tafin hannu yana sanya fatar hannu laushi.

•Zuma da sukari; idan mutum na fama da fata mai yawan saba musamman ma fatar fuska, sai a hada zuma da sukari a wuri guda sai ya shafa a fuska na tsawon minti talatin kafin a murza a fuska. Yin hakan na cire fatar da ta mace a fuska domin bai wa sabuwar fata waje. Idan an gama sai a wanke da ruwan dumi.

•Madara/kindirmo; tana sanya fatar fuska laushi da sulbi. A samu madarar kindirmo sannan a shafa a fuska na tsawon minti talatin a kullum kafin a kwanta barci . yin hakan na kashe kowace irin kwayar cutar da take fesowa a fuska ko kuma a fata.

•Kwai; a samu ruwan kwai a cire gwaiduwar a rika bugawa har sai ya yi kumfa. A shafa a gashin kai na tsawon awa daya ko rabin awa sannan a wanke da man wanke gashi. Yin hakan na cire dattin da ke cikin gashi da kuma hana gashi karyewa.

•Fiya; shi ma yana gyara gashi sosai. A kwaba shi ya yi laushi sannan a shafa a fatar kai domin hana fitowar amosanin ka. A bari a fatar kai na tsawon minti talatin kafin a wanke da ruwan dumi.