✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da suka biyo bayan nadin sabbin masarautu a Kano

A makon jiya ne Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kirkirar sabbin masarautu guda hudu masu daraja ta daya. Sarakunan da aka nada su ne;…

A makon jiya ne Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kirkirar sabbin masarautu guda hudu masu daraja ta daya.
Sarakunan da aka nada su ne; Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Bichi, da kuma Dokta Ibrahim Abubakar, Sarkin Karaye, da Tafida Abubakar Ila a matsayin Sarkin Rano, sai kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya.
Kirkirar wadannan sabbin masarautu ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin mutane musamman al’umar Jihar Kano, inda har wasu suka fito suka yi zanga-zangar nuna rashin jin dadi, yayin da wasu kuma suke murna.

Wani masanin tarihi mai suna Dokta Tijjani Naniya ya bayyana cewa a matsayin masarautar Kano wadda take da kusan shekara 2000, kirkirar sabbin masarautu a Kano zai rusa tarihi da darajar da aka san masarautar Kano da ita.
Shekaranjiya Laraba wata kotu mai zama a Ungogo ta soke nadin na sabbin sarakuna guda hudu.
Da yake hukunci, Mai Shara’a Nasiru Saminu ya bukaci duk wadanda abin ya shafa da su dakata a matsayin da suke kafin 10 ga watan Mayu har zuwa lokacin da za a saurari shari’ar.

 

Babu wata baraka tsakanina da Sarkin Sanusi – Sarkin Bichi

Da yake jawabi bayan ya karbi sandan sarauta, sabon Sarkin Bichi Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce yana da kyakkyawar alaka da Sarki Sanusi II,

“A rayuwata, ba ni da wani buri na ganin an rarraba masarautar Kano, domin mun san tana kawo hadin kai na al’umma baki daya,” kamar yadda sarkin ya shaida wa BBC.

Sarkin na Bichi ya ce duk da ba shi da burin raba masarautar, amma wasu dalilai da gwamnati ta hanga har kuma aka kawo wannan sauyi, “to babu wani abu da al’umma za su yi, sai dai su karbi wannan yanayi da Allah Ya kawo.”

Kafin nadinsa a matsayin sabon sarki, Aminu Ado Bayero ne Wamban Kano ne a masarautar Sarki Sanusi na II.

A karshe Sarki Aminu ya kara da cewa, “Allah ne Ya kawo wannan lamari, kuma a yi addu’ar Allah Ya sa haka ne ya fi alheri”.

Ya ce babu wani dalili da zai sa a samu baraka tsakaninsa da Sarkin Kano, don kuwa sun ba shi duk irin gudunmawar da ta kamata, lokacin da Allah Ya ba shi sarauta bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Ado Bayero.

 

Ba mu karya wata dokar kotu ba – Gwamnatin Kano

Kwamishinan Shari’ah na Jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtari ya bayyana cewa ba su karya wata doka ba wajen nada sabbin sarakan domin har zuwa daren ranar Juma’a da suka yi bikin nadin, bai karbi wani umarni daga kotu ba.

Babbar Kotun Jihar Kano ce ta ba da umarnin cewa gwamnati da Majalisar Dokokin Jihar su dakatar da duk wani mataki na kirkirar sabbin masarautu a jihar ta Kano har sai ta saurari karar da wasu ’yan majalisa suka shigar gabanta suna kalubalantar matakin yin dokar.

“Ban san da kara ba, kawai dai yadda kuka ji a gari, haka na ji a gari,” kamar yadda BBC ya ruwaito shi yana cewa, inda ya kara da cewa: “Ni ban ga oda ta kotu ba kowacce iri.”

’Yan majalisar bangaren Jam’iyyar PDP ne dai suka shigar da karar bisa jagorancin shugabansu Rabiu Sale Gwarzo kamar yadda BBC ya ruwaito.

 

Hakimin Bebeji ya yi Murabus

A wani al’amarin kuma, Hakimin Bebeji, Dan Galadiman Kano Haruna Sanusi ya yi murabus daga sarautarsa.

Dan Galadiman ya bayyana matsalar rashin lafiyarsa da kuma sauyin da aka samu na kacaccala tsarin masarautar Kano a matsayin dalilansa na Murabus.

Dan Galadiman ya sanar da murabus din ne a wata wasika da ya aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar Kano.

Ita dai Bebeji ta fada ne karkashin Masarautar Rano bayan rarraba masauratar Kano da aka yi a makon da ya gabata.

 

Mahaifin Kwankwaso ya yi mubaya’a ga Sarkin Karaye

Mahaifin Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne Hakimin Madobi, Musa Kwankwaso ya yi mubaya’a ga sabon Sarkin Karaye Mai Martaba Sarki Ibrahim Abubakar II.

Tuni hakimin ya jagoranci dagatai da sauran dattijan masarautarsa wajen zuwa Fadar Sarkin na Karaye domin gaisuwa da mubaya’a.

Al’umomin Wudil da Madobi sun nuna mubaya’arsu ga Sarkin Kano.

Su kuma wasu al’ummar kananan hukumomin Wudil da Madobi karkashin kungiyoyin Madobi Concerned Citizens Forum da Wudil Community sun bayyana mubaya’arsu ga Sarkn Kano Malam Muhammadu Sanusi II, inda suka bayyana cewa ba za su yi biyayya ga sabbin masarautun da suka fada ciki ba.

A sabon tsarin masarautun Karamar Hukumar Wudil ta fada karkashin Masarautar Gaya ce, yayin da Karamar Hukumar Madobi ta shiga cikin Masarautar Karaye.

A cikin takardar da Sakataren Kungiyar ta Madobi Malam Balarabe Adamu ya sanya wa hannu, kungiyar ta zargi Majalisar Jihar Kano bisa dokar da ta yi akan kirikrar sabbin masarautu hudun, “duk irin girman da dokar take da ita da kuma cece-kucen da dokar ta haifar amma ’yan Majalisar Dokokin Kano suka ci gaba tare da zartar da dokar cikin kwana biyu ba tare da bayar da damar jin ra’ayoyin al’umma ba.”

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kungiyar A’ummar Wudil Malam Yawale Idris ya bayyana cewa an kirkiri masarautun ne ba tare da yarda da amincewa ko tuntubar al’ummar yankin ba. “Ba a tuntube mu ba kafin yin wannan abu, domin sanya mu karkashin Masarautar Gaya ya saba wa tarihin tsarin sarautr Jihar Kano gaba daya. Kowa ya san mu Jobawa ne don haka ba za mu yi biyayya ga masarautar Gaya ba. Muna so Gwama Ganduje ya fahimci wannan.”

Dukkanin al’ummomin yankuna guda biyu sun nemi gwamnatin Jihar Kano da ta sake duba wannan al’amari tare da yin abin da ya dace a cikin lokaci.

 

Ana ci gaba da binciken Masarautar Kano

Tsohon Sakataren Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Isa Sanusi ya gurfana da a ofishin Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano don amsa wasu tambayoyi kan zargin facaka da kudaden masarautar.

Hukumar ta gayyaci shi ne tare da Dan Buran din Kano Munir Sunusi, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Sarkin, da akantan masarautar da kuma Falakin Kano Mujitaba Falaki.

An dai gayyaci wadannan mutane ne domin su yi bayanin kan zargin kashe kudaden masarautar ba bisa ka’ida ba.

A baya dai hukumar ta dakatar da wannan bincike, sai dai an sake waiwayensa a wannan karon.

Bayan fitowarsa daga wajen binciken tsohon sakataren Isa Sanusi ya shaida wa BBC cewa yana goyon bayan binciken da ake yi.

Malam Isa ya kuma nuna cewa duk da cewa su ‘yan gida ne ba za su ki bincike ba domin abu ne mai kyau saboda za a fitar da gaskiya a kuma tantace.

Masu nada sarkin Kano sun maka Gwamnatin Kano a kotu

Masu zaben sarkin Kano sun kai karar Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje kara kotu, inda suke nuna rashin amincewarsa da kirkirar sabbin masarautu.

Masu nada sarkin su hudu wato Madakin Kano, Yusuf Nabahani da Makaman Kano, Sarki Ibrahim da Sarkin Dawaki Maituta, Bello Abubakar da Sarkin Bai, Mukhtar Adnan sun zargi gwamnan da bata tarihin masarautar ta Kano baki daya, da kuma rikita matsayin da suke da shi a masarautar.

 

Babu ruwan Shugaba Buhari a cikin maganar sabbin masarautun Kano – BMO

Kungiyar Watsa Labaran Buhari wato Buhari Media Organisation (BMO) ta bukaci a cire sunan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a cikin maganar masarautun Kano.

Wannan bayanin ya fito a wata takarda da shugaban kungiyar, Mista Niyi Akinsiju da Sakatarensa Mista Cassidy Madueke suka sanya wa hannu, inda suka ce bai kamata wata jam’iyya ko mutane su rika sanya sunan Shugaba Buhari a cikin wannan maganar ba.

“Wannan maganar Jihar Kano ce wadda Gwamnatin Tarayya ko Shugaban Kasa bai ta cewa a ciki. Jam’iyyar PDP da wasu mutane suna ta kokarin sanya Shugaba Buhari a cikin maganar bisa rashin adalci. Amma ya kamata su san cewa Shugaba Buhari bai da ikon wuce makadi da rawa.”