Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

Ibrahim Sheme da littafinsa na Shata Ikon Allah

Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Shata

Aminiya ta gana da marubuci, mawallafi kuma kwararren dan jarida, Daraktan Watsa Labarai na Budaddiyar Jami’ar Najeriya (NOUN) da ke Abuja, Malam Ibrahim Sheme, wanda Shata ya ba amincewar ya rubuta tarihin rayuwarsa. Sheme ya bayyana wasu daga cikin muhimman al’amura da suka faru a shekara 20 bayan rasuwar Alhaji (Dokta) Mamman Shata Katsina: 

Malam Ibrahim, ko za ka bayyana yanayin da Shata ya rasu?

Karfe 1200 dare ya gota da kusan rabin awa a wani daki da ke cikin Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano, inda Shata ke kwance; minti kadan kafin lokacin, ’yarsa Jamila da ke jinyarsa tana zaune a kan kujera a gefen gadon, gyangyadi na dibarta. Ganin haka, sai ma’aikacin jinya da ke kula da shi, mai suna Malam Umar Ali Dodo, ya ce mata ‘idan barci kike ji, ga daki can ki je ki kwanta zuwa wani lokaci.’ Ta mike za ta fita daga dakin ke nan, sai ta ga ya kama mahaifinta, ya juya shi a hankali. Tana fita, a daidai karfe 12:30 na wannan dare, sai Allah Ya yi wa mahaifin nata cikawa. Allahu Akbar! Rana ta fadi a rayuwar mawakin da babu kamarsa a kasar Hausa.

Shata yana da shekara nawa a duniya ya rasu?

Alhaji (Dokta) Mamman Shata Katsina ya rasu yana da kimanin shekara 76 a duniya. A ranar da ya rasu aka yi masa jana’iza a Daura, inda ’yarsa Jamila ta kai shi domin a yi masa sutura kuma ta yi haka ne ba domin ya yi wasiyyar a rufe shi a can ba maimakon Funtuwa ko Musawa, sai don ganin cewa can ne garin babban masoyinsa, ubangidansa, wato Sarkin Daura a lokacin, Alhaji Muhammadu Bashar. Ranar Juma’a ce, 18 ga Yuni, 1999, wadda a Talatar da ta gabata ta yi daidai da shekara 20 da rasuwarsa.

Me za ka ce game da yanayin wakar Shata?

Ba zan cika ku da tarihin Shata ba, domin kusan kowa ya san wannan. Illa iyaka in ce a rayuwarsa, Shata ya yi wa kusan kowane abu da aka sani a kasar Hausa waka ko ya ambace shi a waka, mai rai da mara rai, har ma da abin da ya shafi addini kamar Allah da ManzonSa da shaihunnai. Waka a wajen Shata ba ta da gefe, don haka ba za mu iyakance ta ba.

Saboda gudunmawar da ya bayar ga ci gaban kasa ne aka karrama shi a lokuta daban-daban. Misali, tun lokacin da yake raye Kungiyar Mawaka ta Najeriya (PMAN) ta taba ba shi lambar girma; haka ita ma Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Kaduna a da, da kuma Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, wadda ta ba shi kyautar Digirin Dokta a 1988. Amma fa babbar karramawa babu kamar irin soyayyar da masu saurare ke masa har zuwa yau din nan. Da wuya ka samu mawakin Hausa wanda mutane suka ci gaba da sonsa shekaru masu dimbin yawa bayan mutuwarsa kamar Shata.

Wani abin sha’awa kuma shi ne yadda aka samu dimbin sababbin masoya wakokinsa, matasa, duk da yake mun shigo zamanin da ake gurbata al’adunmu na gargajiya da wasu bakin al’adu daga kasashe masu nisa da bakin al’ummomi da ke kusa. Wannan shaida ce da ke nuna cewa lallai mutanen yau da na gobe za su ci gaba da son Shata ko da kuwa ba su taba rayuwa a lokacin da shi ya rayu ba.

A matsayinka na marubucin littafin tarihin Shata, ko za ka bayyana wasu abubuwa da suka biyo bayan rasuwarsa shekara 20 baya?

Na farkonsu shi ne rabon gado kamar yadda shari’a ta tanada. An yi hakan ne jim kadan bayan rasuwar Shata. Sarkin Daura na lokacin, marigayi Alhaji Muhammadu Bashar, shi ne ya kafa kwamitin da ya yi bincike, ya tara bayanai kan abin da Shata ya bari kuma ya raba gadon ga magada.

To amma kamar yadda na bayyana a littafina, Shata bai bar wasu milyoyin Naira ba kamar yadda wadansu ke zato. Dalili shi ne, shi mutum ne wanda bai tara dukiya don ta taru ba, shi duk abin da ya samu rabarwa ya rika yi ga mabukata. Duk wanda ya zo neman agaji a wajensa, zai dauka ya ba shi. Hasali ma dai, ba kowa ba ne ya san cewa Shata ya biya wa dimbin jama’a kujerar Makka, kuma ya saya wa wadansu ragon suna, ya yi wa wadansu aure, ya biya wa wadansu kudin haya ko kudin magani, da sauransu. Sannan ya kula da iyalinsa sosai. Don haka, ba abin mamaki ba ne lokacin da ya rasu aka ga asusunsa babu nauyi duk da yake ya samu dimbin kyaututtuka na kudi da na dukiya kuma ya yi kasuwanci da noma da siyasa.

Ko yaya batun littafinsa da kai da wadansu kuka rubuta?

An kaddamar da littafin da shi ya ba da amincewar a rubuta kan tarihin rayuwarsa a cikin watan Yuli, 2006 a Kaduna. Mun so mu kammala littafin tun yana da rai, amma hakan ba ta samu ba. Duk da makarar da muka yi, ya kasance littafi na farko da ya taskace tarihinsa da zurfi kuma zai kasance babban kundin dubawa a wannan fanni. A karshen bara, mun sake fito da sabon bugu na littafin wanda tsarinsa da abin da ya kunsa suka fi na farkon inganci.

 Marigayi Mamman Shata da yaransa a bakin sana’arsa
Marigayi Mamman Shata da yaransa a bakin sana’arsa

A watan Yuni, 2013, ni da wadansu masoyan Shata da wadansu daga cikin ’ya’yansa muka hadu a Gidan Arewa da ke Kaduna, muka kafa Kungiyar Tunawa da Mamman Shata. A jawabin da na gabatar a taron, wanda ya zo daidai da shekara 14 da rasuwar Shata, na nuna bukatar da ke akwai ta kafa “Cibiyar Mamman Shata” ko “Cibiyar Kade-Kade Da Wake-Wake ta Mamman Shata” wadda aikinta ya hada da tattaro duk wani abin tarihi na makadan Hausa, irin su duk wata waka da aka yi da harshen Hausa da aka dauka domin a taskace su don kada tarihi ya shafe su. Na nuna cewar wakokin Hausa na da – irin na su Shata, Narambada, Caji, Doka, Uwaliya, Barmani, Uji, Danmaraya, Surajo Mai Asharalle, Danbade da sauransu – da kuma na zamani – irin na su Sani Danja, Aminu Ala, Yakubu Muhammad, Fati Nijar, Fantimoti, Zango, Sharifai da sauransu – suna cikin hadarin bacewa wata rana. Ban ce duk ba, amma ya kamata a adana da yawansu saboda ’yan baya su same su. Kada mu zauna mu zura ido har al’amuran rayuwa da ke rincabewa su batar da su.

Yaya yanayin wakokin Shata a cikin wadannan shekara 20 da rasuwarsa?

Bayan rasuwar Shata kuma an samar da wakokinsa a matsayin sautin kiran wayar hannu, wato “ring tones.” Kamfanin MTN ne ke tallata wakokin, wadanda jama’a kan biya ’yan kudi domin a ji su idan an kira su a waya. Ana ba iyalin Shata dan hasafi daga cikin kudin, kodayake ba kowa ba ne ya san yarjejeniyar da aka yi da kamfanin. Abu mai muhimmanci dai, a ganina shi ne, ana jin wakokin Shata a bisa wannan tsarin fiye da na kowane mawakin gargajiya.

Bayan haka, an kara karrama Shata bayan rasuwarsa. Gwamnatin Tarayya ce ta fara yin hakan a ranar 28 ga Fabrairu, 2014 lokacin da ta ba shi kyautar karramawa a matsayin daya daga cikin “manyan masu basira, marubuta da ’yan jarida da duniya ta san da su.” A bikin, wanda aka kira “Centenary Awards,” wanda aka gudanar a cikin Fadar Shugaban Kasa a Abuja, Shugaba Goodluck Jonathan da hannunsa ya mika kyautar ga iyalin Shata. Ban da Shata, sharararren mawakin nan Fela Anikulapo Kuti kadai ne mawakin da shi ma aka karrama shi a bikin.

Bayan wannan ko akwai wata kyautar da ya samu bayan rasuwarsa?

Wata kyautar da aka ba shi bayan ya rasu ita ce wadda Gidan Rediyon Jihar Kaduna ya ba shi. A lokacin, gidan rediyon ya yi bikin murnar dawo da matsakaicin zangonsa ne. Gwamna Mukhtar Ramalan Yero da hannunsa ya mika kyautar ga iyalin Shata. An ba da irin wannan karramawar ga Danmaraya Jos, wanda ya halarci bikin. Hasali ma dai, ba a dade da wannan taron ba Danmaraya ya rasu sakamakon rashin lafiya.

Bayan rasuwar Shata, an samu karin masu amfani da Intanet a Najeriya, musamman matasa. Hakan ya haifar da karuwar sababbin masoyan Shata ta hanyar zaurukan tattaunawa a Facebook da kuma WhatsApp. Ta hanyar Soshiyal Midiya, akan samu wakokin Shata na ji da na gani a YouTube da sauran wurare. Dadin abin shi ne, ba wakoki na ji kadai ba, har ma na kallo akan yada su a wadannan kafafe. Sannan karin dadin shi ne za ka iya tura waka ta tafi nisan duniya, ta iske milyoyin mutane kuma duk a kyauta. Ni ne mutum na biyu da ya bude zauren Shata a Facebook, mai suna ‘Dandalin Mamman Shata’, wanda a bara na sauya masa suna zuwa ‘Shata Ikon Allah!’ don ya yi daidai da sunan littafinmu.

Ko akwai wanda ya gaje shi cikin ’ya’yansa?

A zamaninsa, Shata ya hana duk wani da nasa ya gaje shi a wajen waka. Ya fi son su yi makaranta. Dalili shi ne ya lura da dimbin alfanun karatun zamani ga mutum da kuma al’umma baki baya, musamman idan ya tuno da yadda wadansu suka rika yi masa kallon raini saboda wai shi “maroki” ne. Lokacin da babban dansa Lawal (Magaji) ya fara waka, uban bai so ba. To, bayan rasuwar Shata, dansa Sanusi ya shiga harkar waka a cikin 2014 a matsayin ‘Halifan Shata.’ Yanzu  haka Sanusi yana bakin kokarinsa a fagen waka.

Haka kuma mutuwa ta ratsa gidan Shata har sau uku bayan rasuwarsa. Na farko shi ne dansa Nura, wanda ya rasu a watan Maris, 2016 yana da shekara 41. Na biyu, mutuwa ta dauki uwargidan Shata, wato Hajiya Furera, bayan wata daya. Shekarunta 58. Na uku danta, Mamuda, ya rasu watanni 14 cur da rasuwarta a shekarar 2017.

Daga karshe, me za ka karkare da shi?

Zan kammala da cewa dukkan abubuwan nan da suka faru bayan rasuwar Shata, manyan darussa ne ga kowa. Shata dai ya ba da muhimmiyar gudunmawa ga al’umma kuma an gode. Har yanzu ban ji wanda ya ce Shata ba mutumin kirki ba ne. Kuma farin jininsa bai ragu ba. Kowa na so ya ji muryarsa ko ya gan shi a bidiyo. Hasali ma dai, a bara barar nan, an ji Shehu Dahiru Usman Bauchi na bayyana shi a matsayin “dan Aljanna.”