✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da suka faru a majalisa bayan dawowa daga hutu

A ranara Talatar da ta gabata ce Majalisar Dokoki ta Kasa ta dawo zama bayan dogon hutu da ta je a makon karshe na watan…

A ranara Talatar da ta gabata ce Majalisar Dokoki ta Kasa ta dawo zama bayan dogon hutu da ta je a makon karshe na watan Yuli. Tun a watan Satumba majalisar ta yi alkawarin komowa aiki amma ta dage zaman saboda zabubbukan fitar da gwani na jam’iyyun siyasa, kamar yadda ta bayyana.

An dai samu sauyin sheka a tsakanin ’yan majalisar cikinsu har da shugabanni, lamarin da ake ganin zai haifar da wani sabon yanayi a zauren majalisun biyu, inda ake ganin sauya shekar taa iya tasiri ga muhimman batutuwan da majalisar za ta duba don amincewa da su.

Kwana guda kafin komawa hutun wadansu sanatocin APC sun gudanar da taron gaggawa cikin dare game da makomar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Sanatocin sun gana ne a Abuja don tattaunawa kan yadda za su tsige Saraki, bayan sauya shekarsa daga APC zuwa PDP.  Wasu rahotanni sun ce sanatocin sun tafka zazzafar muhawara kan batun tsigewar, inda wadansu ke cewa, APC ba ta yi musu adalci kan wasu batutuwa ba.

Tun ficewar Saraki daga APC, Sanatocin APC suka lashi takobin tsige shi daga mukaminsa, inda suke cewa, dole ne jam’iyya mai mulki ta rike kujerar shugaban majalisa saboda rinjayenta a majalisar.

Kazalika an yi yada jita-jita game batun tsige Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da zarar an koma hutun, to amma sai dai mai tsawatarwa a majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya yi watsi da jita-jitar, inda ya ce ba gaskiya ba ce, ya ce Dogara na da ’yancin shiga duk jam’iyyar da hankalinsa ya fi kwanciya da ita, kamar kowane dan Najeriya kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

“Tabbas dukanmu ’ya’yan APC ba mu ji dadin ficewarsa ba da kuma rudanin da ke faruwa. Amma kuma tilas mu sani cewa Dogara bai fa aikata wani laifin da ya karya dokar kasa ba. Sannan don dan majalisa ko shugaban majalisa ya fice daga jam’iyya, to bai karya wani tsari ko dokar majalisa ko kundin tsarin mulkin Najeriya ba.

“Mu dai a matsayinmu na wadanda suka san yadda majalisa take, ba mu yin wani tunani na tsige shugaban majalisa, domin bai aikata laifin da za a tsige shi ba,” inji Doguwa.

Sai dai  hadiman ’yan majalisar sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadi kan kin biyansu hakkokinsu na alawus-alawus da ba a yi ba. Sun gudanar da zanga-zangar ce a ranar Talatar, bayan shafe makon 10 da aka yi ana hutu.

Sun rika rera wakoki yayin da suka samu wani gefe daya a cikin harabar ginin majalisar suka yi dandazo. Kowanensu yana dauke da allon da aka yi wa rubutu, wanda da Hausa ke cewa, “Mu fa hadimanku ne, ba bayin ku ba!”

Dalilin da ya sanya Majalisar Dattawa shiga taron daga su sai su kadai, wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya jagoranta da kansa.

Jagoran zanga-zangar, Nyakari-Abasi Etuk ya shaida wa manema labarai cewa tun da majalisa ta fara zamanta a shekarar 2015, har yau ba a taba biyansu kudin rangadi da sauran alawus-alawus ba.

“Tilas ta sa mu rika cin bashi a tsakanin junanmu, har ta kai wadansu na bin wadansu bashin Naira miliyan daya da wani abu. Kuma kudade ne da akan aike mu yin wani abu. Majalisar da ta gabata ta rika biyanmu dukan hakkokinmu. Wannan fa ban da ma maganar ba mu horo, wanda a cikin doka akwai yin haka. Domin kamata ya yi a rika ba mu horo kan makamar aiki sau hudu a shekara.

“Amma tunda muka fara a karkashin wannan gwamnati, ba a taba ba mu horon sanin makamar aiki ba. Wanda muka yi a baya Hukumar Kula da Harkokin Majalisar Tarayya ce ta dauki nauyin gudanar da shi, ba majalisar da kanta ba. Amma mu yanzu abin da muka fi damuwa da shi, a biya mu hakkokinmu kawai,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Wannan babbar matsala ce da ta shafe mu, muna shaida wa kowa cewa ga shi dai an dawo daga hutu yau, amma wadansu hadiman sun mutu, wadansu kuma ko kudin makarantar ’ya’yansu ya gagare su. Kowace shekara ana ba da kudin alawus na hadiman majalisa a cikin kasafin kudi, amma sama da shekara uku ba a ba mu ko sisi ba.”