✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da suka wajaba kan kowa don shawo kan matsalolin kasa

Huduba ta Daya Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai mulki, Mai tsarki. Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai tilastawa, Mai nuna…

Huduba ta Daya

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai mulki, Mai tsarki. Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai tilastawa, Mai nuna isa.Tsarki ya tabbatar wa Allah daga barin abin da mushrikai suke tarayya da shi. Ya Allah! Ka tsira da amince ga shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW), bawanKa, AnnabinKa, kuma ManzonKa. Annabin da bai koyi karatu da rubutu daga wani mutum ba; kuma (Ka yi tsira) ga jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, ya ku ’yan uwa na imani! Lallai abin ba a boye yake ba ga dukkan mai hankali daga cikinmu, cewa kasarmu da wasu kasashen da ke Kudu da Saharar Afirka da wasu kasashen duniya suna fuskantar nau’o’in bala’o’i da masifun da suke barazana ga zama lafiya da kwanciyar hankalin al’ummomi da na’yan kasashen ba ki daya. Ya Allah! Muna neman tsarinKa, game da wadannan matsaloli, kuma muna rokonKa, Ka yaye mana su, lallai Kai Mai jin addu’a ne! “Shin wa yake karba wa mai bukata idan ya kira Shi, kuma Ya sanya ku mamayan kasa? Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah? Kadan kwarai kuke yin tunani (An-Namlu: 62).

Daga cikin wadannan masifu, ya ku ’yan uwa! Akwai fada da addinin Allah ta hanyoyi daban-daban da zubar da jinane (ba tare da hakkin shari’a ba) da cin zarafin bayin Allah, musamman keta mutunci matan mutane da ’ya’yansu mata da ta’addanci ga dukiyoyin mutane da garkuwa da mutane yara da manya (domin neman kudin fansa ko kuma sace su da canja musu addini da kabila ala tilas) da shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran abubuwa masu sa maye da kazamar sata ta hanyoyi daban-daban a gidaje da masallatai da kuma ta Intanet (cyber crime) da wanin wadannan! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

Ya ku bayin Allah! Hakika daga cikin abubuwan da suka haifar da wadannan miyagun laifuffuka a fahimtarmu, akwai:

Jahiltar addinin Allah da wahami, wato rashin fahimtar addinin daidai da

sakaci game da tarbiyyar yara – tarbiyya ta Musulunci ingantacciya da mutuwar zuciya – mai haifar da talaucin karfi da yaji. Da zaluncin masu rike da madafun iko – musamman a shekarun da aka fito (lokacin da gwamnatoci ke “kashe- mu-raba” da kudin hukuma) da rashin fitar da Zakka ko rashin fitar da ita kamar yadda Allah Ya ce. Da rashin kyautata wa mabukata daga gefen mawadata da mummunan sakamakon fitintinu (yake-yaken) da suka auku a wasu kasashen Afirka (wadanda suka haifar da yaduwar makamai da rashin doka da oda).

Sauran su ne ci gaban mai ginar rijiyar da kafofin sadarwa na zamani (social media) suka haifar ga tarbiyya da nutsewa a cikin ayyukan sabo da zunubi da kawar da kai daga shari’ar Allah, alhali kuwa Allah (TWT) Ya ce: “Kuma wanda ya bijire daga ambatoNa (Alkur’ani) to, lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata a gare shi, kuma za Mu tayar da shi a Ranar Kiyama yana makaho” (Daha: 124).

Ya Allah! Lallai mun zalunci kawunanmu, zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubbai sai Kai; to, Ka gafarta mana; hakika, babu mai gafarar zunubbai face Kai! Ya Allah! Ka musanya mana mummuna da abu mai kyau, domin rahamarKa, ya Mafi jinkan masu jinkai! Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Mai girma.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Daga cikin hanyoyin magance wadancan matsaloli da taimakon Allah akwai, kamar yadda Sheikh Abdullahi dan Fodiyo (Allah Ya yi masa rahama) ya ce a cikin littafinsa “Tahzibul Insan Min Khisalis-Shaidan,” cewa: “Ka sani cewa rashe-rashen lafiya (na zukata) ba a magance su sai da kishiyoyinsu: Don haka, jahilci da ilimi ake magance shi. Rowa kuwa da kyauta ake magance ta – wato mutum ya kallafa wa kansa fitar da dukiyarsa yana bayarwa har (ya saba da haka) kyautar ta zama tana da sauki gare shi. Girman kai kuwa ana magance shi ne da tawali’u; wato mutum ya doge a kan ayyukan mutane masu tawali’u har (ya saba har) wannan hali ya saukaka gare shi. Kwadayi kuwa ana maganinsa ne ta hanyar tilasta wa kai kamewa daga abin da ake sha’awar (ko kwadayin), tilastawar gaske, kamar yadda ake hakurin dacin magani (a sha haka nan) domin mutum ya samu lafiya. To, duk sauran (miyagun) halaye haka ake magance su.”

A kan haka, mu kuma muke cewa, dacewa ga Allah take, ba shakka warware wadannan matsaloli na hannuwanmu tare da taimakon Allah. Don haka, mu yi kokarin magance kowace matsala da kishiyarta. Kada mu manta cewa lallai Shi Allah ba Ya canja yanayin mutane sai idan sun dauki matakin canjawa da kawunansu; kuma Allah ba Ya saba alkawari. Kada mu taba zaton cewa wani (ko wane ne) zai iya kubutar da mu daga wadannan matsaloli in ba Allah ba! (Domin Ya ce:) “Kuma idan Allah Ya shafe ka da wata cuta, to, babu mai yaye ta face Shi, kuma idan Yana nufinka da wani alheri, to, babu mai mayar da falalarSa” (Yunus: 107). Don haka, ya ’yan uwa! Mu tuba zuwa ga Allah, tuba ta gaskiya. Mu gyara abin da ke tsakaninmu da Shi da kuma abin da ke tsakaninmu da bayinSa. Ina nufin, mu kallafa wa kawunanmu ayyukan biyayya ga Allah da kuma nisantar sabonSa, kamar yadda Malam Abdullahin Gwandu ya ambata.

Sa’annan, kada mu manta cewa tarbiyyar ’ya’yanmu a kan ingantaccen tsari na Musulunci wajibi ne a kanmu. Kada wahalar tarbiyya a wannan zamani na na’urar kwamfuta ta sanyaya mana gwiwa! Iyaka dai mu yi iyakar kokarinmu – saura mu bar wa Allah; tunda duk wanda ya dogara ga Allah, to Ya isar masa! Don haka, mu nisanci sakaci a cikin lamuranmu. Kuma mu nisanci ragwanci da kasawa da zama ci-ma-kwance.

Kai jama’a, mu yi farin ciki, kuma mu gode wa Allah game da nau’o’in albarkatun da Ya zuba mana a wannan kasar Najeriya! Mu ribanya kokarinmu na neman arzikinSa ta hanya kyakkyawa (ta halal). Kuma mu rika taimaka wa raunana daga cikinmu (ko wanda ya zuba iya kokarinsa amma ya kasa). Mu kasance masu kokarin wanzar da zaman lafiya da kokarin kawo ci gaba ga kasarmu kamar yadda mutanen wadansu kasashe suke yi ga kasashensu.

Su kuma mawadata, wajibi ne su rika fitar da Zakkar dukiyoyinsu kamar yadda Allah Ya shar’anta. Kuma su rika kyautata wa bayin Allah kamar yadda Allah Ya kyautata musu. Su yi kokarin kakkafa masana’antu kanana da manya – ta yadda ayyukan yi za su samu sosai (a kashe zaman banza). Ba shakka, “Duk wanda ya rufa wa Musulmi asiri, to Allah zai rufa masa asiri a duniya da Lahira, kuma Allah na cikin taimakon bawa matukar bawa na cikin taimakon dan uwansa” (Daga Hadisin da Muslim ya ruwaito). Don haka, mu hada kai da shugabanninmu domin gyaran al’amura. Allah Madaukaki Ya ce. “Kuma ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa (tsoron Allah). Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zalunci…” (Ma’ida: 2).

Haka kuma, wajibi ne mu fahimci cewa sha’anin tsaro ba na shugabanni ne ba kawai; a’a, na kowa-da-kowa ne. Don haka, wajibin kowanenmu ne ya sauke nasa nauyin domin samar da tsaro ga kasa! A nan muke yabawa da jinjinawa ga Rundunar ’Yan sanda ta Kasa (NPF) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Kasa (DSS), a kan kokarin da suke yi wajen ceto yaran da aka sace daga wasu garuruwa zuwa wasu! Allah Ya saka musu da alheri.

Su kuma shugabanni, wajibi ne su ji tsoron Allah. Su tsaya da ayyukansu yadda ya cancanta. Su nisanci barna da bin son rai. Su yi kokarin yin hukunci da abin da Allah Ya ce gwargwadon ikonsu.

Malamai kuma, yana a kansu su himmatu da aikinsu mai falala, wanda suka gada daga Annabawa – wato tarbiyyar mutaneda shiryar da su da zama kyawawan ababen koyi gare su da yada ilimi da kira zuwa ga hanyar Allah domin tsantsar neman yardarSa.

A karshe dai ga baki daya, lallai mu ci gaba da addu’a (su Kunuti a cikin Sallah da sauransu) domin kyautatuwar al’amura. Kuma mu bi hanyoyin da ake karbar addu’o’i (kamar yadda malamai suka yi bayanai a littaffansu), domin addu’o’inmu su karbu. Dama Allah Ya ce: “Ku kira Ni, In karba muku.” (Ghafir: 60). Ya Allah, Ka karbi addu’o’inmu.

Ya Allah! Ka taimake mu ga ambatonKa da gode maKa da kyautata ibadarKa. Ya Allah! Muna rokonKa rangwame da lafiya a duniya da Lahira. Ya Allah! Ka saukar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasarmu da dukkan kasashen Musulmi. Ya Allah! Ka ba mu abu mai kyau a duniya, Ka ba mu abu mai kyau a Lahira, kuma Ka kiyashe mu daga azabar Wuta. Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga shugabanmu, Annabi Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE), ya gabatar da wannan huduba ce a ranar Juma’a 25 ga Rabi’ul Auwal, 1441 Bayan Hijira, daidai da 23 ga Nuwamba, 2019, kuma za a iya samunsa ta tarho mai lamba: +2348036049452