✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da ya kamata a yi don rage kaushin fata

Akwai abubuwa da dama da suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya. Kaushin kafa yana yawan fito wa…

Akwai abubuwa da dama da suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya. Kaushin kafa yana yawan fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar; yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama da ake sayar das u domin magance matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli na fata sai ku karanta abubuwan da na lissafo muku.

  • A rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.
  • Lemun tsami da sukari suna taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.
  • Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga jiki.
  • A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya dan yi dumi sannan a shafer fatar jiki kaf da shi na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka a kwanta. A rika yin haka kullum.
  • Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci a kullum na taimaka wa fata sosai.
  • A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.
  • A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sai a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi.
  • A yi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a hada duka a jiki, amfani da abubuwa da yawa a fata yana haifar da kuraje a fata.
  • A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bar ta na tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum.