Da Dumi Dumi

Abubuwan da ya kamata a yi lokacin azumi – Kamal S. Alkali

Kamal S Alqali

Darakta a masana’antar fina-finan Hausa, Kamal S. Alkali ya bayyana abubuwan da ya kamata mutane su rika yi lokacin azumi.

Jarumin ya yi bayanin ne cikin wani sako da ya aiko wa Aminiya a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce, “Sakona ga jama’ar Annabi (SAW) bisa ga la’akari da cewa kowa yana jan hankali ga addini domin shi ne kan gaba, to amma zan yi amfani da wannan damar in ja hankali a kan yadda ake mu’amala da yadda za a kula da kai lokacin azumi. Da yawa daga cikin likitoci da malaman addini sun yi jan hankali a kan kada mai azumi ya wuni a rana ko da neman kudi ko da ibada mutum yake yi.”

Daraktan ya shawarci masu azumi da kada mutum ya wuni a rana ko ya tsaya a kan abu daya da zai ginshe shi, “Idan aikin lada ne a rasa ladan saboda gajiya ko jin kamar takaici yake yi na kure, ya kamata masu azumi su rika dan samun barci daga karfe biyu zuwa hudu, ba sai lallai awa biyu ba, ko na minti 10 ne ka rintsa za ka ji jikinka ya dawo,” inji shi.

Ya ce, dangane da garuruwan da suke da zafi sosai ya kamata masu azumi su rika amfani da kayan itace idan an sha ruwa, su kasance cikin natsuwa sannan su guji duk wani abu da zai bata musu rai.

Ya ce, “A kauce wa shan ruwa mai sanyi sosai ko wani nau’in abin sha mai sanyi sosai. Ina nufin kada daga zarar an sha ruwa, mutum ya durfafi abu mai sanyi ya sha, to shi ma yana kawo illa, ka ga mutum magashiyan. An fi so mutum ya samu dabino ko wani abu mai dumi kamar kunu wanda zai jika koda ta samu ta yi aiki kai-tsaye  yadda ta wuni babu komai a cikinta wanda za ta tace.”

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya