✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan Lura yayin shiga Kasuwar Hannun Jari (2)

A makon da ya gabata na fara gabatar da al’amuran da dan kasuwa zai yi la’akari da su yayin da ya yi niyyar zuba jari…

A makon da ya gabata na fara gabatar da al’amuran da dan kasuwa zai yi la’akari da su yayin da ya yi niyyar zuba jari a Kasuwar Hannun Jari, domin samun ingantacciyar riba da kuma gudun asarar da ka iya tasowa daga wannan yunkurin nasa. Abin lura na farko da na yi bayani a kai a makon na jiya, shi ne hawa da saukar farashin hannun jari. Na yi wa mai karatu bayanin yadda dan kasuwa zai rika amfani da bayanai a kan farashin hannayen jari da aka yi hada-hadarsu a kasuwar hannun jari a kowace rana, da ake wallafawa a kafofin watsa labarai. Na kuma ce dan kasuwa zai iya samun wadannan bayanai har ma da shawarwari game da hannayen jarin, ko wadanda suke shirin saye daga wakilinsa na kasuwar hannun jari. Yin haka zai kare dan kasuwa daga fadawa cikin asara.  
    Abin lura na gaba kuma ga dan kasuwa shi ne hadarin da ke tare da rikon Hannun Jari. Wannan ba wani bakon abu ba ne  a wannan fili na kasuwanci ba. Na yi bayanai da misalai a lokacin da nake kwadaita wa dan kasuwa game da yadda dan kasuwa zai amfana daga zama daya daga cikin masu kamfanin da yake rike da hannun jarinsa. To, kowane al’amari na alheri kan kasance da wani bangarensa marasa dadi; misali, kwadayin mallakar kamfani da samun ribarsa na iya sa dan kasuwa mallakar hannun jarin kamfani ko na kamfanonin da ka iya sa dan mallakar hannun jarin kamfani ko kamfanonin da ka iya karyewar jarin dan kasuwa ya salwanta.   
Na yi bayanai a kasidun baya, musamman ma a kasidar baya, yadda dan kasuwa zai guje wa wannan hadar ta neman shawarwarin kwararru. A nan na yi nuni  ga dan kasuwa ga matsalar dan kasuwa na barin hannun jarin kamfani ya karye a hannunsa. Na kuma yi nuni a kan irin hannayen jarin da ya kamata ya saya a kowane lokaci, da wadanda ya kamata ya sayar a lokuta daban-daban. A kan wannan al’amari ne na kawo misali a kan karayar hannayen jari da ta faru kimanin shekara biyar baya, wato tun shekarar 2008, ya zuwa bara. Musamman ma dai abin da ya faru da hannayen jarin bankunan kasar nan.     
   Karayar hannayen jarin bankuna da na kamfanoni a wannan lokaci ya karya jarukan ‘yan kasuwa da yawa. A misalan da na bayar a makalun baya da suka hada da na makon jiya, na yi nuni da faduwar farashin hannayen jarikan irin wadannan kamfanoni da bankuna da suka karye fiye da kashi 50 cikin 100 na farashin da aka rika sayar da su a watan da ya gabaci wannan lokacin.
A wannan faduwa da kasuwa ta yi, farashin jarikan wadansu kanfanonin ma ya fadi, yin faduwar da ta kai hukumar Kasuwar Hannayen Jari ta share su daga rijistarta, saboda darajarsu a kasuwa ba ta wuce ta takardar da aka buga su a kai ba. Sannan kuma haka farashin wadansu bankuna ya karairaye, har ma Babban Bankin Kasa (CBN) ya sayar da su ga Kamfanin Hada-hadar Kadarorin Najeriya (AMCON). Wannan ya sa duk masu hannun jarin irin wadannan bankuna suka rasa jarinsu da suka zuba a ciki.  
Mafita daga matsalolin sayen hannun jari ga dan kasuwa ita ce neman shawara daga kwararru kafin ya shiga kasuwar hada-hadar hannun jari. Irin wadannan kwararru kuma na nan a cikin kowane birni na kasar nan. Idan kuma aka duba kasidun baya da na yi a wannan shafin kan batun saye da rikon hannayen jari, za a ga iri-iren shawarwarin da na bayar, kama daga irin hannayen jarin da ya kamata a saya, da lokacin da yakamata a saye su, da kuma wadanne kudade yakamata a saye su, kuma wace irin bukata ake so a cimma da sayensu. Su ma kansu irin  kwararrun da ya kamata a tuntuba na yi batunsu a kasidun baya.
     Zan karkare wannan mukala ta abin lura yayin shiga kasuwar hannayen jari idan Allah Ya kai mu makon gobe.