✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan Lura yayin shiga Kasuwar Hannun Jari (3)

Wannan shi ne mako na uku da nake ba dan kasuwa shawara a kan abubuwan da yakamata ya lura da su kafin ya fara saka…

Wannan shi ne mako na uku da nake ba dan kasuwa shawara a kan abubuwan da yakamata ya lura da su kafin ya fara saka jarinsa a kasuwar hannun jari, kuma a wannan makon zan kammala wannan makalar. A makon shekaranjiya da na fara gabatar da wannan makala, na fadakar da dan kasuwa a kan hawa da saukar farashin hannayen jari, inda na yi masa nuni game da yadda zai fuskanci wannan lamarin a kasuwar domin samun ingantacciyar riba ya kuma kauce wa asarar da ka iya tasowa daga wannan al’amarin.
    A makon jiya kuma a makalar na yi bayanin irin hadarin da ke tattare da rikon hannayen jari. A nan na yi bayanai a kan yadda kwadayin neman ingantacciyar riba ya sa wadansu dubban ‘yan kasuwa suka yi asarar biloyoyin Naira a wadansu bankuna da kamfanonin da suka rushe kimanin shekara uku zuwa hudu da suka gabata. Wadannan ‘yan kasuwa suna rike da hannayen jarin bankunan da kamfanonin ne ba tare da la’akari da abubuwan da ka je su zo ba a kasuwar da kuma yanayin al’amuran tattalin arzikin kasar ba a wancan lokacin. Na kuma yi bayanin yadda dan kasuwa zai kauce wa irin wannan asara yayin da ya hango yuwuwar faruwar irin wadannan al’amuran.
    A wannan makon kuma zan ba dan kasuwa shawara a kan irin wakilin da zai tafiyar da harkarsa a kasuwar hannun jari, domin rashin samun wakilin kwarai na iya haifar da asara, ko kuma raunanniyar riba. Idan dan kasuwa bai manta ba, na taba bayanin yadda dan kasuwa zai shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari, yayin da na yi makala a kan kasuwar a wannan filin kimanin shekaru uku da suka gabata. Na yi bayanin matsayin wakilin saye ko sayar da hannayen jari da ake kira Stock broker da Turanci. To kamar yadda na yi bayani a wancan lokacin, ita kasuwar hannun jari ba kamar sauran kasuwanninmu da ke birane da kauyuka ba ce inda za mu shiga kai tsaye mu saya ko mu sayar da kayayyakin masarufi ko na ababen hawa ko tufafi ko sauran ababen amfanin yau da kullum.
    Ita kasuwar hannun jari kasuwa ce ta kwararru, wacce ake tafiyar da ita a bisa wakilci, inda dillalai (Stock brokers) ke wakiltar mai saye da mai sayarwa. Misali, idan dan kasuwa na bukatar sayen hannun jarin wani kamfani sai ya je wajen irin wadannan dillai ya shaida musu, su kuma su ba shi fom ya cike ya biya su kudi jimlar yawan hannayen jarin da yake son saye. Saboda haka shi zai wakilci dan kasuwa a wannan kasuwa domin sayo masa hannun jarin wannan kamfanin. Haka kuma idan dan kasuwa na rike da hannayen jarin wani ko wadansu kamfanoni da yake bukatar sayarwa, to su dai irin wadannan dillalai zai samu su sayar masa a kasuwar ta hannayen jari. Hakazalika kuma ko da musanya zai yi daga hannayen jarikan wadansu kamfanonin ya zuwa na wadansu, dole dai wajen wadannan dillalai zai zo su wakilce shi wajen yin hakan. Sannan kuma saboda yau da kullum mai hulda da hannun jari na kasancewa da dillali daya a matsayin wakilinsa a kasuwar, shi zai saya ya sayar masa da hannun jari, ya kuma ba shi shawara a matsayin kwararre a bisa hulda irin haka.
Saboda yarda da dan kasuwa ya yi da wakilinsa, ya kan ajiye kudi a wurin wakilinsa, inda zai ba shi umarnin ya sai masa irin hannun jarin da yake so idan ya samu, ko kuma wanda wakilin nasa ya ga yakamata a saya a wannan lokaci ba tare da ya tuntube shi ba. dan kasuwa kuma na iya bar wa wakilinsa takardun shaidar mallakar hannayen jarinsa a kan duk sa’ilin da ya ga bukatar a sayar ta taso to ya iya sayarwa, ko a musanya, ko kuma a ajiye kudin a asusunsa har sai an samu hannayen jarikan da ya kamata a saya a wannan lokaci.
To, ba a faye samun matsala tsakanin masu hada-hadar hannayen jari da wakilansu ba, amma a kan samu daidaikun matsaloli daga bangaren wakilan, musamman ma da kasuwar ta shiga wani hali a ‘yan shekarun nan. A kan samu yanayin da wakili ya sayar da hannayen jarin dan kasuwa ba tare da ya sanar da shi ba, ko kuma mai hannayen jarin bai umarce shi da ya yi hakan ba. Ko kuma a yi kasayar-kudinne- babu, inda za a umarci wakili ya sayar da hannayen jari ya kuma kasance a karshe bai ba mai kayan kudinsa ba. A kan kuma samu wakili na juya kudi ko hannayen jarin mai su ba tare da ya bayar da umarnin yin hakan ba, kuma ba ya amfana daga ribar da aka samu daga yin hakan. Wannan ya sa dole dan kasuwa ya yi bincike a kan wakilin da ya kamata ya yi hulda da shi kafin ma ya shiga hada-hadar hannayen jari.