✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan Lura yayin shiga Kasuwar Hannun Jari

Na yi makonni biyu ina yin bayanin alfanun da ke tare da sayen hannayen jari ga dan kasuwa, a wannan makon kuma zan fadakar da…

Na yi makonni biyu ina yin bayanin alfanun da ke tare da sayen hannayen jari ga dan kasuwa, a wannan makon kuma zan fadakar da dan kasuwa da wadansu abubuwa guda hudu da ya kamata ya yi la’akari da su yayin da zai shiga wannan harka ta sayen hannayen jari. Lura da wadannan abubuwa ne zai tabbatar da nasara da kuma rashinta ga shigar dan kasuwa kasuwar hada-hadar hannayen jari.
    Hawa da Saukar Farashin Hannun Jari: Idan mai karatu bai manta ba na yi bayanai a madalar makon shekaranjiya, da kuma madalun da na yi a kan al’amurran da suka jibanci harkokin hannayen jari a shekarar da ta gabata, cewa wani abu guda daya tabbatacce game da kasuwar hannun jari shi ne faduwa da tashin farashin hannayen jari. Wannan ya sa a kowace ranar kasuwa ake wallafa farashin hannun jarin kowane kamfanin da aka yi hada-hadarsa a kasuwar. Kafofin yada labarai na yin bayanai a kan matsayin farashin kowane hannun jarin kamfani game da darajarsa a wannan rana a kasuwar, wato ko farashinsa ya tashi, ko ya fadi, ko kuma bai canja ba. Saboda haka a kodayaushe nake bai wa masu karatu shawarar tuntubar wakilansu na kasuwar hannayen jari domin shawarwari a kan hannayen jarin da suke rike da su, ko kuma wadanda suke sha’awar saye, ko kuma wadanda yakamata su saya.
    Kamar yadda na yi bayanai da misalai a lokacin da farashin hannayen jari suka fadi warwas a dasar nan, na fadakar da mai karatu hadarin da ke tattare da barin farashin hannun jari ya karye a hannunsa. Karayar hannun jari a hannun dan kasuwa na iya karya jarin kasuwancinsa gaba daya. A misalan da na bayar a madalun baya na yi nuni ga farashin hannayen jarikan wadansu kamfanoni da suka karye fiye da kashi 50 cikin 100 na farashin da aka rida sayar da su a watan da ya gabaci wannan lokacin. Farashin jarikan wadansu kamfanonin ma ya fadi warwas da ta kai hukumar Kasuwar Hannayen Jari ta share su daga rijistarta, domin ba su da sauran darajar kudi. Haka kuma mun ga yadda farashin wadansu bankuna ya karairaye, har ma aka sayar da su. To a irin wannan yanayi dukkanin masu hannayen jari a irin wadannan kamfanoni sun yi asararsu kacokan. Kuma da a irin kamfanonin da suka karye ana yundurin rufe su a kan sayar da kadarorinsu a biya masu bin su basussuka, amma wadanda suke ride da hannayen jarinsa na zuwa darshe a rukunin masu haddi a cikin irin wadannan kamfanoni. A mafi yawancin lokuta ma, kudin da aka samu daga sayar da kadarorin irin wadannan kamfanoni na darewa kafin a iso kan masu hannayen jari.
Wannan hadari da yake tare da huldar hannayen jari ta hawa da faduwar farashi, dan kasuwa na iya maganinta yayin da ya kasance mai neman shawarar  dwararru, musamman ma wakilansa na kasuwar hannayen jari, wajen saye da sayar da hannayen jarinsa, da kuma tuntubarsu akai-akai a kan yanayin da kasuwar hannayen jari ke ciki. Kuma kamar yadda na yi bayani a madalar baya, wadannan shawarwari ba tsada gare su ba daga dwararrun da za a iya tuntuba. Idan ma aka neme su daga wakilan masu harkar hannayen jari, za a iya samunsu kyauta. Sannan kuma ‘yan kasuwa masu ilimin kasuwancin zamani na iya samun irin wadannan shawarwari kyauta daga dasidu da mujallu da sauran kafafen watsa labarai irinsu talabijin da yanar gizo da dai sauransu.
     A wata dasida da na yi a shekarar da ta gabata a kan rukunin masu sayen hannayen jari, na yi nuni a kan lokutan da dan kasuwa zai saya ko ya sayar da hannun jarin kamfani, dangane da yanayin farashin hannun jarin kamfanin, musamman ma idan ya yi la’akari da rukunin da shi kansa dan kasuwa yake na masu sayen hannayen jari: wato ko yana cikin ‘yan sodo, masu sayen hannayen jari domin farashinsu ya tashi, su sayar su ci riba; ko kuma yana cikin masu sayen hannayen jari domin samun ribar da kamfani zai raba a darshen shekara, ko kuma yana sayen hannayen jari domin ajiyar kudi.             
Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu makon gobe.