✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun da ya kawo tsadar burodi a Kano

An wayi gari da karin kudin burodi, abin da ya sa mutane zargin gidajen burodi

Kungiyar masu gidajen burodi ta kasa reshen Jihar Kano ta ce tilas ce ta sa ta yi kari a farashin burodi saboda tashin gwauron zabin da farashin kayan hadinsa ya yi.

Rahotanni sun nuna cewa karin farashin a Jihar Kano ya fara aiki ne a karshen mako kuma ya shafi dukkannin gidajen burodi a jihar.

A hirarsa da Aminiya, Sakataren kungiyar reshen jihar, Kabiru Hassan Abdullahi, ya ce babu yadda suka iya, su ma dole ce ta sa su yin karin.

“Gaskiya ne mun yi kari kuma ya fara aiki daga ranar Asabar. A zahirin gaskiya ana yin kasuwanci ne domin riba, kuma a cikin ‘yan watannin nan kawai an kara kimanin N4,000 a kan farashin kowane buhun fulawa”, inji shi.

Sakataren ya kara da cewa, “Duk burodin N50, N60 zuwa N70 yanzu mun kara masa N10 a kan farashinsa na da.

“Na N100 zuwa N150 kuma yanzu mun kara masa N20, yayin da dukkan burodin N200 zuwa sama yanzu mun kara masa N50.

“Idan kuka yi la’akari za ku ga kusan dukkan kayan hada burodi kama daga fulawa zuwa sinadarin habaka ta, sukari zuwa sauran kayan hadi komai farashinsa ya yi tashin gwauron zabi.

Kara farashi ko rage inganci

“Yawanci mutanenmu sun gwammace idan irin hakan ta faru mu rage ingancin burodin a maimakon mu kara farashi, hakan kuma ba shi da kyau ko kadan”, inji Malam Kabiru.

Daga nan kuma kungiyar ta yi kira ga al’umma da su karbi karin da zuciya daya, tana mai cewa su ma ba da son ransu suka yi karin ba.

To sai dai wani mai sana’ar sayar da shayi da biredi a unguwar Kofar Waika da ke Kano, Abdullahi Garba, ya ce ya zuwa safiyar ranar Litinin ba su ga karin da aka ce an yi ba.

“Ka san a mafi yawan lokuta idan masu gidajen biredi za su yi kari yawanci abin da suke yi shi ne su rage ingancinsa a maimakon kara kudin.

“Na fi zaton abin da suka yi ke nan wannan karon ma, saboda an ce tun ran Asabar aka kara amma mu ba mu ga karin ba,” inji Abdullahi.

Yadda zai shafi jama’a

A nasu bangaren kuwa, magidanta da kan sayi biredin domin karin kumallo sun koka kan cewa karin zai shafe su matuka.

Auwal Sadauki, wani magidanci mai ‘ya’ya bakwai, ya ce ya kan sayi biredin N400 a kowacce rana, amma sakamakon wannan karin hakan na nufin kenan dole ya kara yawan kudin da ya ke kashewa wajen karin kumallon.

Ya kuma ce amma idan ta tabbata ba a kara farashin ba amma an rage ingancinsa, ya zama wajibi ya kara yawan kudin sayen biredin a kowacce rana.

Wannan karin dai zai shafi mutane da dama kasancewar burodin wani muhimmin abinci ne na gama-gari wanda kusan dukkannim talakawa da mawadata, a birni da kauye na amfani da shi.

Masana tattalin arziki da dama na ganin yawan hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci a matsayin wata babbar matsala da ke shafar ci gaban kasa.