✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun da ya sa ’yan PDP 6,000 sauya sheka

Masu sauya shekan sun kuma bukaci a gudanar da zaben kasanan hukumomi na gaskiya a Jihar Bauchi

Akalla yan jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Bauchi guda 6,000 koma jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Bogoro.

Shugaban APC na Bogoro, Haruna Rikaya, yayin karbar su a ranar Asabar ya ce, masu sauya shekar cikakkun mabiyan tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ne da suka sha alwashin bin sa a duk inda ya sa kafa a siyasance.

Ya ce, jiga-jigan siyasa uku suka jagoranci mutanen 6,000 zuwa APC: “Ayarin farko, Iliya Bulus dan takarar shugaban karamar hukuma a karkashin tutar PDP ya zo da su, sai Mista Kecho Alhamdu, tsohon dan takarar Majalissar Dokoki ya zo da na biyu, sai na uku Murtala Juma ya zo da su” inji shi.

Rikaya ya ba su tabbacin yi wa duk wanda ya biyo Dogara zuwa APC adalci ba tare da bambanci ba, “Hadin kan jam’iyya shi muka sa a gaba ba ra’ayoyinmu ba”.

Shugaban masu sauya shekar Bulus Iliya ya ce sun dawo APC ne domin biyayya ga Dogara.

Ya yi kira ga Gwamna Bala Mohammed da ya yi adalci wajen gudanar da zaben kananan hukumomin jihar “kamar yadda aka yi masa adalci ya lashe zaben da ya kawo shi a matsayin gwamna, ya kuma ba wa duk wanda ya ci zabe.

“Ina rokon sa ya yi wa dukkannin jam’iyyun da za su shiga zaben na watan Oktoba adalci yadda muka yi masa a zabensa na zama gwamnan Bauchi”, inji shi.

Ya kuma roki gwamnan ya ba hukumar zabe ta jihar damar gudanar da sahihin zabe bisa adalci, ba tare da katsalandan ba.