Da Dumi Dumi

Achida ya zama Shugaban Majalisar Jihar Sakkwato

An zabi Alhaji Aminu Achida na Jam’iyyar APC a matsayin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato. Jam’iyyar PDP ce ke da gwamnati tare da majalisar da APC ke da rinjaye. Achida ya doke abokin karawarsa Abdullahi Garba Sidi mai wakiltar Mazabar Gwadabawa ta Kudu da ake zargin yana samun goyon bayan jagoran Jam’iyyar APC a Jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Rahotanni sun Achida ya samu nasarar ce, bisa goyon bayan da Gwamnan Jihar Aminu Wazirin Tambuwal, bayan da Ibrahim Sarki na  Jam’iyyar PDP ya bayyana sunansa a matsayin wanda za a zaba. Ita Jam’iyyar APC  tana da ’yan majalisa 16 ne yayin da PDP ke da 14. Samun nasarar shugaban majalisar ya biyo bayan samun kuri’a 16 daga cikin 30 da aka kada ne, bayan gudanar da zaben a asirce, sai abokin karawarsa Sidi ya samu kuri’a 13 aka kuma bayyana kuri’a daya ta lalace.

Mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar ya tafi ga Jam’iyyar PDP inda Abubakar Magaji mai wakiltar Bodinga ta Arewa kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar a majalisar da ta gabata ya sake rike mukaminsa, inda ya lashe zaben da kuri’a 17 ya kada Alhaji Isa Haruna na Jam’iyyar APC. Akwai jita-jitar da ake ta yadawa kafin zaben shugabannin majalisar cewa akwai wadansu ’yan majalisar na Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP ta saye su.

Daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar APC a jihar ya shaida wa Aminiya cewa dab da za a kaddamar da majalisar sun zargi ’yan majalisar da ke wakiltar Wamakko da Wurno cewa sun hada kai da Jam’iyyar PDP.

Hukumar Gudanarwar Majalisar ta hana manema labarai daukar yadda aka kaddamar da majalisar da kuma zaben shugabanninta, haka hanin ya shafi su kansu shugabannin jam’iyyun siyasar biyu da suka je majalisar da magoya bayansu, lamarin da ya so ya kawo rudani, amma sai ’yan sanda suka tarwasu ta hanyar harba barkonon tsohuwa.

ADVERTISEMENT

Sabon Shugaban Majalisar Alhaji Aminu Muhammad Achida a ziyarar godiya kan taimakon da Gwamna Tambuwal ya yi masa na zama shugaban majalisa ya jagoranci mambobin majalisa ciki har da ’ya’yan Jam’iyyar PDP ya ba da tabbacin goyon bayansu dari bisa dari.

Shugaban majalisar ya gode wa Gwamnan kan goyon bayan da yake ba majalisar, ya ce an gudanar da zaben shugabannin majalisar ta 9 cikin lumana kuma za su sanya jiha farko kan duk abin da za su yi ba tare da son rai ba.

Da yake karbar ’yan majalisar, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal  ya taya su murna nasarar zaben shugabannin da suka yi  tare da yi musu fatar samun nasarar gudanar da aikinsu da kammalawa lafiya.

Haka ya ba dukkan ’yan majalisar su 30 tabbacin cewa zai yi aiki da dukkansu ba tare da nuna wani bambanci ba.

Ya kuma tunatar da su cewa a matsayinsu na wakillan jama’a da aka zaba akwai bukatar su yi aiki tukuru domin kawo ci gaba da  bunkasa  jihar.

Gwamna Tambuwal ya ce  yadda aka gudanar da zaben shugabanin majalisar ya nuna cewa an samu ci gaba a fagen siyasa a Jihar Sakkwato.

Jam’iyyar APC  ta taya sabon Shugaban Majalisar murna ta ce wannan babbar nasara ce ga jam’iYyar da magoya bayanta. Jam’iyyar ta kara jinjina ga jagororinta da suka yi tsaye har jam’iyyar ta samu wannan mukami na shugaban majalisa.

APC a wata takarda da Shugaban Jam’iyyar Alhaji Isah Sadik Achida ya raba wa manema labarai ta ce majalisa na da muhimmanci a tafiyar da gwamnati don haka ’yan majalisar su yi tsaye waje aiwatar da aiki ga talakawan jihar. Ya yi fatar majalisa ta zama mai amfani da kawo ci gaba mai dorewa ga al’ummar jihar.

Share