✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adali da mugu (2)

Mutumin da yake kaunar ilimi yakan so a fada masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ki yarda a fada masa laifinsa. Ubangiji Yana murna da…

Mutumin da yake kaunar ilimi yakan so a fada masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ki yarda a fada masa laifinsa. Ubangiji Yana murna da mutanen kirki, amma Yakan hukunta masu shirya mugunta. Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram. Matar kirki abar fariya ce, abar murna ga mijinta, amma idan ta sa shi kunya, ta zama masa kamar ciwo a kashinsa. Amintattun mutane za su yi maka abin da ke daidai, amma mugaye za su rude ka. Maganganun mugaye na kisan kai ne, amma kalmomin adalai sukan ceci wadanda ake neman ransu. Mugaye sukan gamu da faduwarsu, ba magada, amma iyalan adalai sukan dawwama. Idan kai haziki ne, za a yabe ka, amma idan kai dakiki ne, mutane za su raina ka. Gara kana talakanka, kana neman abinci, da ka mai da kanka kai wani abu ne, alhali kuwa abin da za ka ci ya fi karfinka. Mutumin kirki yakan lura da dabbobinsa, amma mugaye sukan yi wa nasu keta. Manomin da ke aiki kwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a batar da lokaci a kan aikin banza. Iyakar abin da mugaye suke so, shi ne su samu muguntar da za su yi, amma adalai suna tsaye daram. Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala. Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai samu abin da ya cancance shi. Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara. Sa’ar da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la’akari ba zai nuna ya kula ba. Sa’ar da ka fadi gaskiya, ka yi adalci, amma karairayi su ne jagorar aikata rashin adalci. Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka. Gaskiya dawwamammiya ce, amma karya kurarriya ce. Wadanda ke shawarta mugunta za a auka musu farat daya, amma wadanda ke aikata alheri za su yi farin ciki. Ba wani mugun abu da zai samu adali, amma mugaye ba za su samu komai ba, sai wahala. Ubangiji Yana kin makaryata, amma yana murna da masu fada da cikawa. Mai la’akari zai bar wa cikinsa abin da ya sani, amma wawaye sukan yi ta tallar wautarsu. Mutum mai mayar da hankali ga aikinsa zai samu iko, amma ragwanci zai sa mutum ya zama bawa. Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna. A koyaushe adalin mutum yakan gwada halinsa, amma mugaye sukan bata a hanya. Rago ba zai kai ga biyan bukatarsa ba, amma mai kwazo zai samu dukiya. Adalci hanyar rai ne, amma wauta hanyar mutuwa ce.

Da mai hikima yakan mai da hankali sa’ar da mahaifinsa yake kwabarsa, amma mutum mai girman kai ba ya yarda da kuskurensa. Mutanen kirki za a saka musu da alheri a kan abin da suke fada, amma mayaudara sukan kosa su ta da zaune tsaye. Ka lura da irin abin da kake fada don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa. Rago yakan kosa ya samu wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mayar da hankali ga aikinsa zai samu kowane abu da yake bukata. Masu aminci suna kin karairayi, amma maganganun mugun abin kunya ne da kaskanci. Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce faduwar masu zunubi. Wadansu mutane sukan nuna su attajirai ne, alhali kuwa ba su da komai. Wadansu kuma sukan nuna su matalauta ne, alhali kuwa suna da dukiya. Kudin attajiri suna iya ceto ransa, bai kyautu ba a razana matalauci. Adalai suna kama da haske mai haskakawa kwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da ke mutuwa. Fariya ba ta kawo komai sai wahala. Hikima ce a nemi shawara. Dukiyar da aka same ta a sawwake, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta karuwa. Idan ba bege, sai zuciya ta karaya, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya. Idan ka ki shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya. Koyarwar masu hikima mabubbugar rai ce, za ta taimake ka ka kubuta sa’ar da ranka yake cikin hadari. Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke. Mutum mai hankali a koyaushe yakan yi tunani kafin ya aikata abu, amma wawa yakan tallata jahilcinsa. Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma wadanda suke amintattu sukan kawo salama. Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsawatarwa za a girmama shi. Abu mai kyau ne mutum ya samu biyan bukatarsa! Wawaye sukan ki barin mugunta. Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abota da wawaye, za ka kuwa lalace. Wahala tana bin masu zunubi a ko’ina, amma za a saka wa adalai da kyawawan abubuwa. Mutumin kirki zai samu dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai. Saurukan da ba a aikatawa, za su ba da isasshen abinci ga matalauci, amma mutane marasa gaskiya sukan hana albarka. Idan ba ka horon danka, ba ka kaunarsa ke nan, amma idan kana kaunarsa za ka rika kwabarsa. Adalai suna da isasshen abinci, amma mugaye fama suke da yunwa koyaushe.

(Karin Magana 12,13)