Da Dumi Dumi

Adam A. Zango ya koma Kannywood

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya yi rajista da Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano, wato Kano State Censorship Board.

Jarumin ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram, inda ya wallafa kwafin fom din rajistar da ya yi, sannan ya rubuta a kasa cewa, “an wuce gurin.”

Idan ba a manta ba, a bara jarumin ya bayyana cewa ya fice daga masana’antar ta Kannywood, inda ya ce zai ci gaba da mashiryin fim mai zaman kanshi.

Daga baya kuma, ya bayyana aniyarsa ta komawa Legas da harkokinsa.

A kwanakin baya, an samu tsaiko da cece-kuce tsakanin hukumar da Adam a lokacin da ya sanar da cewa zai shigo Kano domin ya kalli fim din Rahama Sadau, Mati a Zazzau, inda rahotanni suka nuna za a kama shi idan ya shiga.

ADVERTISEMENT

A dokar hukumar, dole kowane jarumi, ko darakta ko furodusa ko wani ma’aikacin masana’antar Kannywood ya yi ragista da ita kafin ya ci gaba da gudanar da harkokin fim, musamman a Kano.

A lokacin da aka gudanar da rajistar, Adam A. Zango yana cikin wadanda ba su yi rajistar ba, amma kwatsam sai ya wallafa a shafin nasa cewa ya yi rajistar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya