✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adam A. Zango ya koma Legas da yin harkokinsa

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, ya shaida wa Aminiya cewa, zuwa yanzu ya koma birnin Legas da harkokinsa. Jarumin ya ce,…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, ya shaida wa Aminiya cewa, zuwa yanzu ya koma birnin Legas da harkokinsa.

Jarumin ya ce, ya koma Legas ne domin ya bunkasa harkokinsa akan yadda ya tsaya a Arewa, “komawa ta Legas kamar wanda ya yi makarantar sakandare ne idan yana son ci gaba a karatunsa sai ya nufi jami’a, wannan shi ne abin da nayi”

A Zango, ya kara da cewa, irin karan tsanar da abokan sana’ar sa suka aza masa yana cikin dalilinsa na yin kaura zuwa Legas.

Domin jin cikakkiyar tattaunawar da Adam A Zango ku nemi jaridar Aminiya ta mako mai zuwa.