Search
Subscribe
Adam A. Zango ya yi hadari a Nijar

Adam A. Zango ya yi hadari a Nijar

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango, ya yi hatsarin mota.

Zango yana tafiya ne a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamhuriyar Nijar tare da wasu abokansa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sai dai jarumin ya ce “Allah Ya kare su, domin hadarin ya tsaya ne kawai a kan motar da suke tafiya a ciki”. kamar yadda BBC ya ruwaito.

Zango yana yawan yin tafiye-tafiye musamman a lokutan bukukuwan sallah, inda ake gayyatarsa domin yin casu.

BBC ta yi kokarin tuntubar A Zango domin neman karin bayani kan lamarin amma bai amsa wayar ba kawo yanzu.

Amma bayanai a shafinsa na Instagram sun nuna cewa ya je Niyami, babban birnin Nijar, domin yin wasan sallah.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin