Search
Subscribe
Adam Zango ya kashe miliyan 46 don daukar nauyin karatun dalibai 101

Adam Zango ya kashe miliyan 46 don daukar nauyin karatun dalibai 101

Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Adam A. Zango ya dauki nauyin karatun marayu da marasa karfi su 101, inda ya kashe Naira miliyan 46.75 a makarantar Farfesa Ango Abdullahi International School da ke Zariya.

Adam Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa yana jin dadin taimakon marasa karfi, “Akwai dadi mutum ya samu damar taimakon wadansu, musamman marasa karfi. Taimakon mutane musamman yara da matasa yana sanya min jin dadi. Yaya mutum zai taimaka wajen sanya wa wani farin ciki?.

Ba za mu boye ayyukanmu na alheri ba. Za mu yi duk abin da za mu iya wajen taimakon mata da kananan yara marasa karfi da manyan ma,” inji shi.

Da yake tabbatar da labarin, Shugaban Makarantar Farfesa Ango Abdullahi International School Zariya, Malam Hamza Jibril ya tabbatar da daukar nauyin daliban da Zango ya yi, inda ya ce “Lallai da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai 101 a makarantarmu. Kuma ya biya kudin.”

Shaidar biyan kuxin makarantar da Adam Zango ya yi
Shaidar biyan kuxin makarantar da Adam Zango ya yi

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin