Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Adam Zango ya sayi sabuwar motar Naira miliyan 23

Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam A Zango, ya sayi sabuwar motar kece raini kirar Wrangler Jeep da aka kera a shekarar 2019.

Aminiya ta gano cewar, Zango ya sayi motar ne akan zunzurutun kudi Naira miliyan 23.

ADVERTISEMENT

Da yake yada hotunan motar, a shafinsa sada zumunta na Instagram, a jiya Talata, jarumin da aka fi sani da ‘Prince Zango’ ya bugi kirjin cewa; lokaci ya yi da zai haska tauraronsa fiye da na tsaransa a fagen fim.

ADVERTISEMENT

Ya rubuta a shafin na Instagram din cewar: “Baya ga wannan murmushin, akwai kuma matukar godiyar Allah kan dukkan abin da Ya hore mini -yake kuma kan hakan…da sunan Allah na samu wannan Jeep din. Lokacina ne da in nuna kasaita kan tsarina, (Jarumin fim) dan haka ina godiya gare ku duk game da goyon bayan da kuke nuna mini.”

Binciken jaridar Aminiya, ya gano cewar, motar kirar Jeep mai suna Wrangler 2019 ana sayar da ita ne akan fam dubu 49,990.