✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adam Zango zai bar goyon bayan Buhari ya koma Atiku

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya shirya tsaf don ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Kamar…

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya shirya tsaf don ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Kamar yadda majiyarmu ta samo rahoton.

Rahoton na bayyana cewa, Adam Zango ya tattauna da na hannun daman dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da wasu shugabannin PDP a jiya Laraba a Abuja.

Rahoton ya kara da cewa, a tattaunawar shugabannin PDP suka yi da jarumin sun yi kokarin gamsar da shi akan ya canza jam’iyya daga APC zuwa PDP.