✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’a (8)

Fadin Gaskiya “Saboda haka, sai ku watsar da karya, kowa ya rika fadar gaskiya ga makwabcinsa, gama mu gabobin juna ne.” Afisawa 4:25. Godiya ga…

Fadin Gaskiya

“Saboda haka, sai ku watsar da karya, kowa ya rika fadar gaskiya ga makwabcinsa, gama mu gabobin juna ne.” Afisawa 4:25.

Godiya ga Ubangiji Allah Mai iko duka da Ya bar mu cikin masu rai a yau. Barkanmu kuma da sake haduwa a wannan mako inda za mu yi nazari a kan fadin gaskiya a wannan karo.

Kamar yadda muka yi nazari a kan fadin karya a makon da ya shige, mun ga yadda fadin karya kan sa mutum cikin kuncin rayuwa har ma ga mutuwa, amma a makon nan za mu ga yadda fadin gaskiya kan yantar da mutum har ga samun rai na har abada. 

Fadin gaskiya ba abu ne da ke da sauki ba, a lokuta da dama mukan tarar da kanmu cikin wani yanayin da fadin gaskiya kan zama da wuya, sai ka ga a nan take Shaidan kan samu zarafin rudin mutum da rashin fadin gaskiyar sai dai ya karyata gaskiyar domin ya tsira ko ya ci nasara cikin wannan yanayi. Amma a zamanka na Kirista hakan nan ne Yesu Almasihu ya koya mana, ko haka Littafi Mai tsarki ke fadi? Yaya muke ji idan wani ya fada mana gaskiya ko idan muka fada wa wani gaskiya? 

Salama, gaskiya na dauke da salama mara kimantuwa, a duk lokacin da ka fadi gaskiya ba ka da wani duhu kuma cikin zuciyarka.  Ubangiji Allah ma da kanSa zai yi farin ciki da abin da ka yi, sai dai ko Shaidan zai yi bakin ciki kwarai da gaske domin ka ci nasara bisansa, Halleluya!

 A wani bangare kake a yau, bangaren Ubangiji (Gaskiya) ko Shaidan (karya)? Rayuwarka tana cike da gaskiya, wato furcinka da ayyukanka da mu’amalarka da jama’a, cikin rayuwarka da iyalinka ko kuma cikin bautar Ubangiji Allahnka? Kana tsaye bisa gaskiya? Misali, za ka tarar da kanka a kotu, a zaman mai laifi ko wanda ake zarga, ko kuma mai shaida, alkali yakan iya tambayarka, a nan take abubuwa da dama sukan iya cika tunaninka, amma ka tuna fa, Ubangiji Yana sane da komai. Ka mika komai gare Shi domin neman taimakonSa da jagorancinSa wajen fadin gaskiya, Shi kuma zai cece ka a cikin kowane irin yanayi idan ka dogara gare Shi. Ba ma kotu ba kadai ba, ko wajen aikinka ne, ko a cikin gidanka, ko kana tare da jama’a, ka roki Ubangiji don Ya jagorance ka domin a san ka da fadin gaskiya a koyaushe.

A cikin wannan rayuwar da muke ciki, ya kamata mu nemi jagorancin Ubangiji don Ya koya mana kamar yadda marubucin Zabura ya yi. Zabura 25:5 “Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarKa, Gama Kai Mai Cetona ne. Dukan yini ina dogara a gare Ka.” 

Idan kana son ka zama cike da gaskiya, dole ne ka yi rayuwa cikin Ubangiji, wato bin tafarkinSa da farillanSa. Mutum ba zai taba cin nasara da ikon kansa ba, gama rayuwar gaskiya sai kana tare da Ubangiji, Shi kuwa zai bishe ka cikin hanyar gaskiya. Mutum ba zai taba cin nasara ba a cikin rayuwar nan da ikon kansa, sai dai idan mun nemi nufin Ubangiji Allah. Idan ka tarar da kanka ko wani cikin rashin fadin gaskiya, ka binciki kanka ko wannan mutum, za ka ga cewa yana aiki da nufin kansa ne, wato yana kokari ya ceci kansa ko ya burge mutane da wani abin da kunuwansu ke kaikayin ji. 

Misali, aikin siyasa, hatta majami’unmu a yau, Pastoci da dama suna guje wa gasiyar maganar Ubangiji na ceto da zunubi ko Jahannama, don irin wannan gaskiyar ba ta da dadin ji ga kunnen mai zunubi, sai ka ga sun sauya maganar Ubangiji ta gaskiya da nasu nufin don su burge jama’a ko su samu taron jama’a ga majami’unsu. 

Lokacin da Yesu Almasihu na nan duniya ya fadi gaskiya har ga malaman Attaura da Farisawa, bai ji tsoron kowa ba, ko kuma nemi yardarsu da goyon bayansu, ya fadi gaskiya, ya kuma tsaya a kan gaskiyar da ta yi musu dacin ji. Bai fadi wani abu don ya samu taron jama’a ba, domin fadin gaskiyar maganar Allah ne jama’a suka taru su ji shi, sai mu yi koyi da wannan, ko kai mai bishara ne, ko mai jin bishara, bari gaskiyar Ubangiji ta zama dalilin rayuwarka, ta wurin haka ne dukan duniya za su ga hasken Ubangiji a rayuwarka don su gaskanta su kuma juyo wurin Ubangiji Allah. Domin haka sai mu zama a natse da fadake cikin rayuwarmu, don mu guje wa shirye-shiryen Iblis don ya sa mu fada cikin tarkonsa.     

 “Ku natsu, ku kuma zauna a fadake. Magabcinku Iblis yana zazzagawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lankwame.” 1 Bitrus 5:8.

 “Daga karshe kuma, ’yan uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin kauna, ko mene ne daddadar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan wadannan abubuwa za ku yi tunani.” Filibiyawa 4:8

Ubangiji Allah Ya taimake mu, don mu zama masu fadin gaskiya cikin rayuwarmu, amin.