✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’a ce kadai za ta kawo karshen rikicin manoma da makiyaya –Limamin Sojoji

Tsohon Limamin Sojoji a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo, ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su rungumi addu’a…

Tsohon Limamin Sojoji a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo, ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su rungumi addu’a a matsayin babban matakin yakar rikicin Boko Haram da kuma tashin hankalin nan na rikicin manoma da makiyaya da ke ci gaba da ta’azzara a kasar nan.

Tsohon limamin sojojin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a gidansa da ke garin Bunza a Jihar Kebbi, inda ya bayyana cewa ta hanyar komawa ga addu’a ce kadai za a samu shawo kan rikicin manoma da Fulani makiyaya. “Ina mai shaida wa jama’a cewa karfin addu’a ya fi karfin bindiga da alburushi, don haka ina kiran kowa ya rungumi addu’a domin samun yakar wadannan matsalolin, ta hanyar addu’a ce kadai Allah Zai iya juya zukatansu su dawo zuwa ga aikata ayyuka masu kyau su zamanto mutane nagari,” inji shi.

Shehin Malamin ya ce “Kamar yadda muka yi ta addu’a Musulmi da Kiristoci a shekarar 2015 Allah Ya kawo mana karshen Boko Haram, kuma Allah Ya karbi addu’armu, to ko yanzu muka dage da addu’a babu abin da ya fi karfin Allah.”

Ya ce addu’ar nan ita ce za ta kai a samu nasarar inganta zaman lafiya da hadin kai a tsakanin jama’a ya ce sai da zaman lafiya ne za a samu magance matsalolin tattalin arziki da walwala da kuma jin dadin jama’ar kasa.

Sai ya bukaci ’yan Najeriya su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanai na sirri da kuma jama’ar da ba su yarda da su ba, ya ce irin wadannan duk hanyoyi ne na samun nasarar damke miyagun mutane.

Shehun Malamin, ya yaba namijin kokarin da Gwamnatin Tarayya take yi a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram musamman a shiyar Arewa maso Gabas. Yana mai cewa gwamnati tana  bakin kokarinta wajen wannan yakin, inda ya ce kubutar da ’yan matan makarantar Dupchi da ta yi ba karamar nasara ba ce ga kasa.